MABUDIN NASARA...........
@ Daga:-Shamsuddeen Ibrahim Fatimiyyah
07032908169
sifatimiyyahkt@gmail.com
Dan Adam bai mallaki wata dama a rayuwarsa kamar damar lokaci ba, matukar akwai lokaci to za ka iya zuwa ko'ina, zaka iya yin Komai. A cikin jerin shafukan wannan rayuwa ta duniya, komai mai yuwuwa ne matukar an baka damar lokaci Sannan ka yi Amfani dawannan lokaci.
Ko a cikin mafarki kada ka kuskura kashe kanka da kanka ta hanyar barin mafarkinka ya tarwatse domin gamsar da Wasu mutane, Al'adar mafiyawancin mutane itace Suna son ka bar abin da ka ke yi ka bisu cikin duniyar ta'ayinsu. Da yawa Wasu mutane sun dauka wai sai kana da zurfin ilimi, ko makudan kudi, ko mulki kafin ka iya kaiwa ga mafarkinka, kawai abin da kake bukata shine ka gano wanene kai? Me ka ke muradi? Sannan lokaci guda ka yarda da kanka, ka kuma tsayu kyam a kan abin da kake son cim mawa a rayuwa.
Mafi yawan mutanen dake faduwa a wannan rayuwa matsalar da ya dabaibayesu guda daya ce ba biyu ba. Sun fara aiwatar da abu mai kyau, Amman kuma sun dare gabanin cimma nasara. Ita wannan rayuwar cike take makil da radadi da kuma azaba,amman mafi radadi da azabar da Dan Adam ke haduwa da Ita shine dan Adam ya samu kansa cikin kokarin gamsar da mutane.
Wani babban masani mai Suna, Bill Cosby yana Ce wa "Ban San member hakikanin hanyar nasara ba. Amma hanyar faduwa itace kayi kokarin da kowa ".
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment