Dabi’u 10 mabudan nasara ne da baka taba tunani akansu
ba…
Menene
mabudin nasara?... Yana da kyau mu fara da wannan jawabin
“Da
yawa suna ganin cewa sihiri shi ne matakin nasara,
Shine
tabbatacciyar hanya daya da za a iya nasara akanta.”
Ni
kuma ina sanar daku cewa babu wani mabudi mai kama da hakan.
Mabudan
nasara suna da yawa.
Kana
da mabudan a hannunka, kamar yadda kake da makargama a hannunka. Abin da kake
bukata shine kawai ka aikata.”
Akwai
mabudan nasara….
Hakika
mabudai 10 masu jagoranta ne ga rayuwa a bisa nasarar da kake fata ka kasance a
cikinta.
Zan sanar da kai su kuma ka zurfafa tunaninka domin ka
fahimci zance na, kayi aiki da shi domin ka kasance a cikin masu nasarar
rayuwa.
1. Tsara Manufofi Masu Kyau:
Da
yawan karatuttuka na alakanta tsakanin nasara da kuma tsarin manufa. Abu mafi
sauki anan shine ka tsara yadda kake burin tsarin rayuwarka ya kasance idan har
baka san inda zaka fara kamawa akai ba. Tsara manufufin da kake burin cimma
cikin lokaci kalilan da wadanda kake burin cimma masu dorewa, ka saka lokacin
da kake burin kasancewarsu sai dai kuma dole ne akanka da ka dinga aiki akansu
a kullum, su kasance a birbishin tsarin zuciyarka. Idan har ka cimma nasarar
wannan, ka tsara dukkan matakan da dole ne ka bisu idan har ina da manufar
cimma wadannan manufufi naka. Sai kuma, KAJE RUWA AIKI. Idan har tsarin da kayi
yayi maka daidai, to sai ka tsara bangon manufarka na kowane abu da kake son
cimma na ko wace rana.
2. Karfafaffen
Tsarin Aiki da Babu Gazawa
Cewar “Jajircewa a aiki na kada masu kwazo” gaskiya ne, sai dai kuma har
kullum, Kasala da Nasara kalmomi ne da basa tafiya tare. Idan har ba zaka iya
jajircewa akan manufarka ba, kada ka yi tunanin wata rana zaka yi Nasara.
3. Dauwama
Kawai kamar komai na Rayuwa, idan har
ba zaka dage ba wajen dauwama akan neman sa’a tabbas hasara na tare da
kai.
Idan har bazaka dauwama ba akan cin
abinci mai gina garkuwar jiki to, lallai kai kuma zaka rasa lafiya. Idan har ba
zaka dauwama a cikin zumunci ba tabbas zaka samu matsaloli. Haka kuma gaskiyar
kasuwanci da kuma dan kasuwa dole sakonsa ga abokan hulda ya zama dauwamamme
sannan yayi nasara.
4. Tarbiyya
Saboda kana da wani abu mai ma’ana da
kake aiki ba dare ba rana akansa, tarbiyar cewa A’a ga abu maras kyau duk da
cewar a tsarin kana duban cewa za a samu nan kusa, ribace wajenka ga manufarka
ta nan gaba mai dorewa a matsayin sakamako da kuma abinda zakayi alfahari
dashi.
5. Dole ne ka
zama mai sadaukarwa
Ka zama mai iya sadaukarwa a yanzu,
hakan zai sa ka yi farin ciki a gaba. Babu sauki ga hanyar, sai dai dukkan
matashiyar maganar itace sadaukarwa zata jagoranceka zuwa ga inda kake burin
kaiwa. Anan gaba.
6. Ka dage wa Neman Ilimi
Napleon Hill ya ce acikin
littafinsa mai suna Think and Grow Rich: “Hanyar nasara itace hanyar dauwama
akan neman ilimi”
Duniya na zagayawa haka
kuma tana sauyawa cikin sauri sosai, idan har baka nemi canji ba… idan har baka
da ra’ayin neman ilimi sosai, nan kusa duk abinda ka sani bazai isheka ba. Kayi
kunanin dukkanin abubuwa ko ayukka, dabamammaki, kamfanoni da kuma sana’o’I da
ke a koluluwa a halin yanzu, sanin kowa ne cewa a da can baya basa nan, sai
gashi a yanzu biliyoyin daloli aka samu ga wadannan kamfanoni kamarsu AirBnb,
Istagram, Uber, Bitcoin da kuma Spotify, babu shakka shekaru goma da suka
gabata a baya babusu. Idan har wadanda suka kirkizo wadannan shafukan basa da
ra’ayin neman ilimi ta yaya zasu yi su kirkiro wadannan sababbin fasahar da
babu ita a baya, su fito da damammaki wa kawunansu har su kafa wadannan
masana’antu da babu irinsu a da can baya. Yawan NEMAN ILIMIN KA, yawan RIBAR
KA, haka kuma BAZA KA TABA KOSHI daga NEMAN ILIMI BA.
7. Ka zama mai
saurare
Misalin cewa baza ka taba koshi daga
neman ilimi ba, haka ma ba zaka taba koshi daga sauraron wasu daga cikin
wadanda sukayi nasara, ko wadanda suka fadi kamun kai ba. Ka saurari manyan
malamai da manyan shugabanni. Ka saurari abokai, yan uwa da abokan kasuwanci
domin ka gina kyakkyawar mu’amalarka. Ka saurari irin yadda za a mayar maka da
martani na batanci domin kawai ka gina kanka, ka gina kasuwancika tare da
samawa kanka sakamako mai kyau a cikin rayuwarka. “Sarkin Na iya ba zai taba zama
gwani ba” saboda bai taba ganin anyi ba dai dai ba abubuwa ko suna
faruwa da yawa akan mutane daban-daban da ya dace su zama darasi akanka. Ka
zama mai kunnuwan saurare don gane maha’inta idan sun zo ha’inci sannan kuma ka
zama mai karfin bibiyar gyara a kowane lokaci.
8. Ba zan taba
bari ba ya zama dabi’arka
Ka karanta labarin duk wani mutum da
ya zama daya daga cikin wadanda suka yi nasara a cikin rayuwarsu, babu shakka
zaka taradda cewa labarin nasu duk daya ne. akwai wata rana ta rayuwarsu, babu
wata rana da suke ja daga baya su daina, duk yadda abu ya zama baya yiyuwa, sai
kaga kamar babu wata mafita…
Kashi 99.9999% na mutane sukan
sakankance da rayuwa ta tsaka tsakiya, su kanji cewar ta wadatar dasu, sai dai
zaka ga abubuwa na zuwa musu wani iri, komai na sauyawa zuwa wani iri daban.
Su kuma suna kallon rayuwar a
matsayin darasin da zai taimaka musu gajen gyara kuskurensu, wannan ne halayyar
da ya dace kowa ya kasancewa da shi idan har suna burin nasara a duk kanin
al’amurransu, saboda ita Rayuwa na zuwa maka ne da jarabawa kuma dole ne akanka
ka fadi idan tura da kai bango.
Tsara tsauni kuma ka cigaba da taka
matattakalar kada ka fasa duk lokacin da kake ganin kamar ba zaka iya ba. Yi
maza kace A’a! bazan taba bari ba, koda kuwa a duniya kowa zai yi tunanin zaka
fada.
9. Manufarka ta
zama cikin tsafta
Babu wani abu da ke cikin Rayuwa da
zai hana ka cimma nasara idan kana da manufa mai tsafta, kuma kana da tsari mai
girma. Idan har kasan dalilin ka, to tabbas zaka yi nasara komai wuya. Idan
kuma dalilinka yana da ma’ana mai karfi zaka tabbatar dashi komai wahala babu
abinda zai hana manufarka cika.
10. Kada ka ji tsoron fadawa hatsarin
rayuwa
Kada ka taba tsammanin ka
cimma wani babban al’amari idan har ba zaka iya shigar da kanka a cikin babbar
matsala ba. Wannan abu ne da kowa ya sani matuka, wadanda sukayi nasara a
rayuwarsu suna jefa rayuwarsu ne acikin hatsari sosai domin kawai su cimma
abinda suke buri a rayuwarsu. Mutanen dayan bangaren kuma kullum tunaninsu su
zama a wanke, sai dai kuma bazasu taba samun abinda yafi hakan ba a rayuwarsu,
bazasu taba samun cikar burinsu ba, ai kuwa shi kenan abu yayi kyau, babu wani
hukunci. Sai dai kuma idan burinka ne ka zama cikin rayuwar mafi daukaka dole
ne ka karbi tsari na shi hatsari domin ka sabu mafi girman sakamako.
Shin ko akwai wanda ya aminta da
jawabi na?
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment