![]() |
Hajji Yana daya daga cikin Shika-shikan Musulunci guda biyar, dole ne ga kowane musulmi/ma ya je hajji idan yana da hali |
Hukumar da ke kula da Mahajjata Yan Najeriya
ta ce ta fito da manhajar da za ta takaita batan alhazanta a lokacin Aikin
Hajji. Kumar ta na cewa manhajar ta G. P. S za ta dinga jagoranci wajen nuna ma
Mahajjatanta taswirar inda suke da kuma inda suke nema.
Manhajar da zasu yi amfani da ita tana
dauke da yanar gizo (intanet) kuma an sanya ta a dukkan shemomin jihohin kasar,
ta yadda za a iya latsa duk wacce mutum ke nema daga ko ina, kamar filin Arfa
da Muzdalifa da wajen jifa.
A nan take Manhajar za ta nuna wa
mutum taswirar inda zai bi ta manhajar Goggle Map.
Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito Manhajar
za ta yi aiki ne kawai a wayoyin tafida gidanka. Haka kuma Hukumar ta NAHCON ta
ce ta samar da wasu lambobin waya da alhazain Najeriya za su iya kira dare ko rana
domin neman taimako. Shugaban hukumar ta NAHCON Abdullahi Mulhtar ya yi kira ga
duk Alhajin da ya kira lambar ba a saurare shi ba, da ya kai korafi a shirye
suke su dauki mataki.
A kowace shekara daruruwan alhazai
ne ke bata, inda suke shan bakar wahala tsakanin shemomi yayin neman
tantinansu.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment