GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah kuma aminci ya tabbata a bisa za babben jakada shugaban Annabawa Muhammad dan Abdullahi wanda aka saukarwa fiyayyen littafi ma’ana al-kur’ani domin ya zama shiriya da kuma waraka ga muminai, Yar da da aminci su kara tabbata abisa iyalan gidansa da sahabbansa da kuma mabiya tafarkinsa har ya zuwa ranar sakamako.
Ina kara mika godiyata ga Allahu subhanahu wata’ala, wanda shine Ya bani ikon rubuta wannan littafi.
Ina mika godiya ta musamman ga Maihaifana Abubakar Sadiq Maccido da Zainab Sadiq Maccido da Aisha Sadiq Maccido da kuma Rukayya Sadiq Maccido ga irin dawainiyarsu da kuma nuna kulawarsu akaina, fatana Allah Ya biyasu, Ya kuma sanya alhairi a cikin rayuwarsu baki daya amin.
Godiya ta ba zata kare ba har sai na mikata ga yan uwa da aminai na kamarsu: Farida M. Bello, Shamsudeen Sadiq Maccido, Sharahbil Muhammad Sani, Yakub Al’amin Yakub, Walid Kabir Gada, Malam Usman Umar Aliyu, Badadiya, Habiba, Balki, Maryam Mufida, Ummu, Baby, Billy, Sumayya, Fatima, Jamila da kuma Lubabatu da fatar Allah Ya sanya alhairi a cikin rayuwarmu baki daya amin.
ASIYA SADIQ MACCIDO
(ASIKHAN)
09037433171
Copyright © Asiya Sadiq September, 2017
Hakkin Mallaka (M) Asiya Sadiq September, 2017
Published in Nigeria by
Sharhamak Computer Ventures
Beside Birnin Kebbi Local Government Secretariat
Kebbi State, Nigeria
Website: www.share4world.com.ng
Tel: 08113777717
HUBBUL YAKIN
Misalin karfe biyar da rabi ne na yamma, a daidai lokacin da ake tashi daga islamiya, dalibbai daga ko ina sa bullowa sukeyi kowa yana kokarin ya koma a gida .Wata natsatstsuwar yarinya mai hankali da kamala ce sanye da uniform dinta na islamiya hijab dogo har kasa tafe take tana tako a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a cikin uniform din sky blue ne sunyi matukar yi mata kyau duk da ba wani kwalliya tayi ba, domin ga dukkan alamu ita irin wayannan ne da ake kira da “Natural beuties” Ma’ana (wayanda basa bukatar kwalliya) domin wai ta kara musu kyau. Bakowa bace wanna face Bilkisu mai gadon zinari ‘ya daya tilo a wurin Malam Iro. Yau gabaki daya a cikin wani yanayi take jin kanta kuma itama kanta ta kasa gano meke damunta, kawarta Asiya ba karamar gwagwarmaya ta sha akan dai ta ga ta sake ta dawo dai- dai kamar yadda aka saba amma abin yaci tura, ga baki daya komai ba yayi mata dadi a duniya, kuma ta rasa gano dalilin faruwar hakan, bata tsaya fira da Asiya ba da aka tashi sakamakon tsayar da ita da Malam Babba ya yi, kawai sa kai tayi gaba abinta. A daidai wurin wani mazauni ta tsaya ta gaida dattawan da ke wurin cikin girmamawa, ansawa sukayi ga baki dayansu, yauwa Balkisu dama ke nake jira ungo wannan ledar kaiwa Umman ki, wani dattijo wanda ko ba’a gaya maka ba kasan mahaifintane akan tsananin kamar da suka yi, ya fada tare da mika mata ladar, hannu biyu tasa ta karba batare da tace komai ba, tasa kai tayi gaba.Wani daga cikin dattijawan wanda tun sa’adda Balkisu take wurin yake kallonta yana murmushi, shine ya bita da kallo har sai da ta kure masa.Ajiyar zuciya yayi sannan ya fara Magana gaskiya Mallam Iro kayi dacen diya maihankali da natsuwa ga ganin girman manya, murmushi mahaifin nata yayi mai nuna alamar har a cikin ranshi yaji dadin abinda ya fada ba tareda ya fadi komai ba. Gabaki dayan dattawan wurin kowa ya amsa da cewa ai kuwa gaskiyar ka Bilkisu yarinya ce mai hankali, Malam iro ya katse zancen tare da fadin ai kaima Alhaji Haliru ba karamin dace kayi ba da samun yaro mai natsuwa ga hankali da kokari, a gaskiya duk afadin anguwarnan ba sa’an Sulaima dana sani da yayi hankalin shi da sanin ya kamata.Ai kuwa ka tunamin ina zuci-zucin na gaya maku amma sai na manta, inji Alhaji Haliru ga baki daya hankali ya koma kanshi, me ya faru? Wasu mutum biyu suka hada baki.Sulaiman ya samu aiki Kaduna, kunsan ya tura takardar neman aiki, jiya sunanshi ya fito ya samu aiki a Kaduna, an bashi nan da wata hudu masu zuwa da yakoma ba kin aiki Insha Allah.Masha Allah! ai kuwa wallahi munyi murna Allah ya sanya Alkhairi ga baki dayan mutane suka ce Ameen, Alhaji Haliru ya fada tare da dan ya mutsa fuska kamar wanda ya tuna da wani abin haushi.Kunsan meye damuwata? A hakikanin gaskiya bana so Sulaiman yayi wannan tafiya shi kadai, har Kaduna garin da bayada kowa sai Allah ni na ma rasa me yasa aka kaishi aiki can, hakane to amma kuma ai namiji ne wanna ai ba abin damuwa bane ni a gurina. Wani daga cikin mutanen ya fada. Ba wannan nake nufi ba, ina nufin zaifi dacewa da ace yanada mata kaga sai kawai su tafi tare abinsu ai kaga zata ringa dabe masa kewa ko? A gaskiya kayi tunani Alhaji, ta mai zai hana ayi masa aure ne yanzu sai kawai ya wuce da Amaryar tasa? Aikai Malam Sani ba auren bane bana so nayi masa a’a Inaso ne na samar masa mace mai hankali da natsuwa. Abu mai sauki ai ina ga ga Bilkisu nan kamar halayansu yazo daya, me zai hana sai a hada su ko kuwa? Malam iro ne ya fadi haka kai tsaye tare da jefawa Alhaji Haliru wani kallo mai nuna alamar ko kuwa ya ka gani? Kamar ya san abinda yake zuciyar Alhaji Haliru kenan, shi tun da can yana son ace Bilkisu ta kasance suruka a gareshi, a ganin shi ba wanda ya dace ta aura face danshi Sulaiman. Da hanzari ya amsa da wallahi kuwa da gaskiyarka malam Iro wannan abin da ka fada shine daidai, Alhamdulillahi kai! da kuwa abu yayi daidai wallahi. Kai masha Allah a hakikanin gaskiya kunyi tunani yanzu sai arufe zance guda, Malam Iro ne ya fara da cewa ya mallakawa Sulaiman “da” a wurin Alhaji Haliru “yar” sa Bilkisu, shi kuwa Alhaji ya karba hannu bibbiyu tare da bashi sulaiman din damar yazo a gidansa domin su dai-dai ta a tsakaninsu kafin ranar daurin auren ta zo.Murna a wurin Ahaji Haliru ba’a cewa komai, kamar ma shine angon. Bai jira lokacin tashi yayi ba ya hauri takalmansa ya nufi gida cikin farinciki kamar wani wanda aka yiwa albishirin shiga aljanna. Shima Malam Iro da saurin sa ya nufi gidansa bayan an tashi daga mazauna, Allah-Allah ya ke yi ya isa gida, ya gayawa matarshi labari mai dadi har a ranshi yasan Sulaiman yaro ne mai hankaali da sanin ya kamata yana kuma sane da cewa zaya rike masa diyarsa da amana. Tun a kofar gida ya fara rangada sallama har ya isa a cikin gidan, da hanzari uwargidan shi ta fito, sannu da zuwa maigida an dawo lafiya, lafiya kalau ina Bilkisu? Yanzunnan taje raka kaawarta Asiya, lafiya dai Baban balarabe naga sai wani faman far’a kakeyi ko tsintuwa jakar kudi kayine ta fada cikin zolaya, murmushi yayi hade da yin gajeren tsaki,wannan abin yafi tsintuwar jakar kudi, to madallah bari na dauko tabarma naji wannan abin wani irin abin alkhairi ne haka,har ta dan yunkura ya dakatar da ita, ki bar tabarma kawai lokacin sallah ya gaba to yanzu masallaci zan wuce, gyara tsayuwarta taayi ta fuskance shi da kyau ina jinka baban Balarabe. Wato wani abin alkhairi ya same mu, kinsan Sulaiman dan gidan Alhaji Haliru na can hayin kusa da masallacin jumua’a? eh! Da hanzari ta fada tana kallon shi, mahaifinshi ya nemar masa auren Bilkisu kafin zuwa nan da wata hudu za’ayi biki a kai amarya dakinta. Daga nan ya kwance mata biri har wutsiya yanda sukayi a mazauna. Itama fara’ar takeyi ta kuma yi na’am da maraba da zancen, sai dai a wata zuciyar tana jin tausayin Bilkisu ne, ta yaya za’ayi mata haka kuma wai duka abin cikin wata hudu, bama wannan yafi damunta ba wai ba anan cikin garin zasu zauna ba a’a har Kaduna, inda su dukan su ba mai dangin iya balle na baba. Arwala yayi ya wuce masallaci tareda gaya mata bazai samu dawowa da wuri ba zasuje wani wuri kuma zasu dan dade yasa kai ya fita, da hanzari ya dawo da baya yauwa Hauwa’u ki fa gayawa Bilkisu komai idan ta dawo kinji! Tau ta fada tare da daga kai alamar naji. Yasa kai ya fita, daukar butar daya gama alwala tayi ta fara yin alwalar itama, har a cikin ranta tana farin cikin da abinda maigidanta ya gayamata kuma tasan bazai cutar da diyar shi ba. Sai dai kawai bata san ya Bilkisu zata dauki al’amarinba duk da tasan baza taki yin abin da mahaifinta yace tayi ba. Kamar ta tuna da wani abu kuma sai kawai ta shararda wannan zancen ta fara murna a ranta tana hango yar tata a matsayin amarya. Kabbarta sallar ta keda wuya sai ga Bilkisun ta shigo, ta nemi guri ta zauna a falo, remot ta dauka ta fara canja tasha daga NTA Hausa zuwa zee cinema, wani film akeyi duka hankalinta yana a wurin. Bayan mahaifiyar tata, ta idar da salla ta juya ta fuskance ta, tadan jima tana kallon nata batare da ita Bilkisu ta gani ba, kasantuwar duka hankalinta yana kan abinda take kallo, sai da ta kira sunan ta sannan ta waigo, Umma kin kare sallar ashe, ina wuni, lafiya kalau mi ya tsai dake daga rakiya? Wallahi Umma Asiya ce ke bani labari bamu san lokaci yana tafiya ba kuma sai akayi daidai da mu dukan din ba mai yi shi yasa bamu damu ba mukaci gaba, daga kai kawai tayi sai da tayi dan shiru na mintoci sannan ta fara da cewa: Maigado (sunan da take kiranta dashi kenan) duk da yake ba it ace yar fariba kasantuwar duk yaranda ta Haifa rasuwa sukeyi Bilkisu kadai Allah ya raya musu. Itama Bilkisu ta fuskanci mahaifiyar tata tace na’am Umma, dazu mahaifinki yazo yayi min wani albishir wanda naji dadin shi sosai. Ya kuma umurceni dana gaya miki wannan abin alkhairin. Gabanta taji ya fadi batareda tasan dalilin ba murmushin yake tayi meye umma, wani abin alkhairi ya same mu? Eh maigado babanki ne ya zabar miki da mijin aure, yaro mai hankali da natsuwa kyakawa dashi, har ma angama Magana za’ayi bikin ku cikin wata hudu masu zuwa. Kamar saukar aradu taji abin, shin wai ko mafarki ne takejin wannan, ko kuwa zolayace Umma keyi mata? Kuma tasan Umma bata haka da ita, hakikanin gaskiya dai take gaya mata,da kyar ta hadeye yawu, tace aure fa kikace Umma, eeh aure mana maigado.ya naga kamar bakiji dadin abinda na fada ba, maigado ki sani cewa mu iyayenkine ba kuwa zamu zabar miki abin da zai cutar da ke ba, anan ta dukufa tana maiyi mata nasiha tareda lurarda ita, har aka kira sallar isha’I, ta miko da nufin kabbarta sallah dan juyowa tayi a dai-dai lokacinda Bilkisun itama ta mike ta nufi dakin ta.Maigado ta kirata tana murmushi, waigowa tayi na’am Umma,ba za ki tambayi ko waye surukinnawa ba? Dukar da kanta kawai tayi, murmushi mahaifiyarta ta sakeyi, sulaiman na can hayin gidan da yake kusa da masallacin Jumuah, dan maman sule ta idar da maganarta da yar gajeruwar dariya, ita kuwa Bilkisu da hanzari ta fice daga falon ta fada dakin ta, a hankali ta zauna kan gadonta a dai-dai lokacin da ta kwanta tabi gadon, fankar take kallo amma ga baki daya halinta baya wurin, ji take kamar wata almara, wai ita za’ayiwa aure cikin wata hudu. hoton sulaiman h ta gani a’a idunuwanta a gaskiya tasan Sulaiman baya da matsala kuma yana da halaye masu kyau amma kuma batajin son shi kona kwayar zarra a ranta, dolene tayi biyayya ga mahaifanta domin ita kanta tasan samun miji irin Suleiman ba karamar sa’a bace amma ya zatayi ita dai ba sonshi bane batayi kawai dai tayi alkawalin ba zata sake son wani da namiji ba har karshen rayuwarta. Rufe idanunta tayi to idan ma bata amince da Sulaiman dinba wa take dashi da take so.kwatsam masoyinta rabin jikinta ya fado mata a rai wato Usman wanda take kira da (MAN) wani hadadden saurayi ne wankan tarwatsa sosai yana da jiki amma daidai dashi, yana da manyan idanu farare tas kamar madara, hancin sa irin wannan ne da yake faro tsawon shi tun a saman goshi wato dai irin na shuhrakan, yana dauke da wushirya da take haskaka fararen hakuransa kyau idan yayi dariya, kai a hakikanin gaskiya duk inda haduwata ta kai Usman ya wuce can domin idan ka ganshi ba tare dayayi Magana ba zaka zaci irin yan indiyan nan ne dake zuwa kasashe-kasashe yawon bude ido, sun hadu ne da Bilkisu lokacin tana (Secondary School SS1), hakika Usman gwanine wurin iya soyayya, sun kasance suna son junansa so na hakika Usman shine saurayin Bilkisu na farko a duniya tun tana SS1,suke tare har takai SS2, Suna matukar son junansu kamar su hadiye kansu amma ba wanda ya sani a gidansu kai karewa ma ko Aminiyarta bata sani ba duk kuwa irin shakuwar da suka yi a duniya. Wata ranar litinin bayan an tashi daga makaranta fitowarta bakin (Gate) din ta hangoshi tsaye cikin wani mawuyacin hali da hanzarinshi yazo ya taryeta suka hadu, a inda suka saba haduwa ya nufa.Lafiya (MAN) naga kamar kana cikin damuwa meke faruwa? Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya fara BILLY (shine sunanta yake kiranta dashi) nazone muyi------- kasa idarwa yayi idanuwansa suka cika da kwallah, muyi me (MAN) don Allah ka gayamin hankalinta duk atashe. BILLY nazo ne muyi bankwana zanyi tafiya kuma zan dan dade ban dawo ba, yanzu ma ni kadai ake jira a wuce.Nan take idanuwanta suka cika da kwalla, idan ka tafi yaushe zaka dawo ne? Ta fada dai-dai lokacin da hawayanda ke makale idanuwanta suka kwaranyo. Wani dogon nunfashi yayi tare da kanne nashi hawye bazan dade ba BILLY zandawo komai daren dadewa, zan dawo gareki domin ke kadai ce matata a duk fadin duniya nan kamar yanda nine kadai mijinki, karar wayarshi yaji wadda ke cikin aljihunshi, bai kula ba, ya cigaba da jawabinsa, “Nayi miki alkawarin duk fadin duniyar nan ba wadda zanso idan bake ba, zan dawo muyi aure dake mu zauna har karshen rayuwar mu”. Duk iya daurewar da ya yi a wannan karon sai da hawaye suka zuba a idanuwansa. Ita kuwa Bilkisu dama ta ke yi, juyawa ya yi da karfi “BILLY sai wata rana!” bai sake waigo inda ta ke a tsaye ba. Tafiya kawai yake, hawaye na zubar masa kamar wanda ya rasa iyayensa ko aka gayawa bazai sake ganin taba har abada. Bilkisu durkushewa ta yi a kasa tana kuka tana kiran sunansa. Tun daga wannan rana bata karajin ko labarinsa ba, abin da yafi ma ta zafi da radadi a zuciya shine bata da hotonsa ko guda daya wanda zata rika dubawa tana tunawa dashi sabanin shi da ya ke da hotunta bila adadin, domin kuwa ko haduwa suka yi suna hira zai rika daukanta hotuna ba adadi, kuma duk lokancin da tayi hotuna sai ta bashi. Wani tsaki ta saka mai dauke da takaici, “Mwts” a dai-dai lokacin da ta dawo daga kogon tunanin da ta ke yi, duk fuskarta ta jike da hawaye. “A hakikanin gaskiya Usman bai kyauta ba, haka ma zuciyata bata kasance mai adalci ba da ta kasa mantawa da Usman". Balkisu ke fadar haka a cikin zuciyarta. Wannan shine dalilin Bilkisu da yasa tun daga Usman bata sake gwada soyayya da kowa ba duk da tururuwar masoyan da suka mata zarya, domin irin kyanta da kirarta ta wuce gaban namiji ya kalleta sau daya ba tare da ya maimaita kallon nata ba. Bilkisu farace amma ba tasba, ta na da manyan Idauwa masu (Shape) din nan da ko ba’a sanya musu kwalli ba sai ka zata ai su na da. Ta na da Girar Ido irin dara-daran nan masutsawo da basa bukatar (mascara) wurin bayyana tsabar kyansu, girar idanuwawanta kuma irin bakar nan ce kirin mai matukar sha’awa, hancinta kuwa dogo ne shigen irin na Rani Muhurji shi baiyi tsawo sosai ba amma kuma dogo ne, gashin kanta kuwa dogo ne wanda ya zuba har a gadon bayanta baki wulik dashi kamar kullum tana saka mishi man da zai kara mishi baki, tanada fararen hakora sai kace sai da aka sanya ruler wajen daidaita su, shape dinta kuwa ko Nicki Minaj sai dai ta bawa kanta lafiya domin kuwa koda ita Bilkisun aka bawa dammar ta kera kanta da kanta iya shape dinda zata yiwa kanta kenan, kai! A gaskiya tsayawa bayanin halittar da Allah yayiwa Bilkisu bannan lokaci ne domin kuwa sai mu cika rabin littafi muna bayani ba tareda mun kammala ba.
Shi kuwa Sulaiman bayanda mahaifinsa Alhaji Haliru ya isa gida, ya kira uwargidansa ‘ya shaida mata duk yanda sukayi da malam Iro, wato dangane da batun aurenda ya nemawa dansu Sulaiman, tun daga farko har karshe.Kamar yanda yake tsammani matarsa, mace mai kirki da biyayya wato Hajiya Aisha tayi na’am da wanna zancen dari bisa dari, da kanta tasa a ka kira Sulaiman kasancewar tun-tuni yana gida, da hanzarin sa ya isa a falo inda mahaifansa ke kiranshi, ya duka ya gaida mahaifinsa ya umurceshi daya nemi guri ya zauna bayan ya zauna ya fuskanci mahaifinsa, Sulaiman game da tafiyar da zakayi Kaduna ne, kasancewar an mayarda kai ga baki daya acan, a matsayinka na namiji, bai kamata ace kaje gari da zama kai kadai ba, wannan san ba mutncin bahaushe bane, bisa ga la’akari da wannan da kuma ma wasu dalilai da ban gayamaka, na yanke shawarar zanyi maka aure kaje da matarka acan.Ras!! gabanshi ya fadi kamar andoka masa guduwa a zuciya da kyar ya hadiyo yawon da suka makale masa. Bai samu ta fadi ba gyada kansa kawai yayi alamar ina saurarenka. Nayi Magana da mahaifin yarinyaarda zaka aura, na namar maka auren yar’sa ya kuma amince da haka, harma mun saka ranar bikin, nan da wata hudu masu zuwa, sai ka rika zuwa wurinta domin ku fahimci juna ko? caraf mahaifiyar tasa ta amshe zancen tare da fadin, can ne gidan Malam Iro yarsa Bilkisu itace surukar taa tana murmushi, ta kara da cewa kasan maigida akwaishi da iya zabe. Shima mahaifin nashi murmushin jin dadi yayi yace ka fahimce ni ai ko? Daga kanshi yayi da yake a duko yace eh Abba nagode Allah yasa haka shine mafi alkhairi, amen Sulaiman tashi ka tafi Allah yayi maka albarka, mikewa yayi tare da fadin amen ya fice da hanzari ya bar dakin, kan gadonshi ya nufa, bai tsaya wata-wata ba ya afka saman gadon nashi, shin me mahaifansa ke shirin yi masa? aure!!. Kamar Bilkisu shima kogon tunani ya fada. Shi dai baya zargin mahaifinsa akan abinda ya aikata masa, domin kuwa yasan Bilkisu yarinyar arziki ce mai hankali da natsuwa, amma kuma shi bai taba jin yana sonta ba.Juyawa yayi kan katifarsa yana sakawa a ransa, “idan ma bai amince da wannan al’amarin ba wace mace ce nake da da har zan kawo nace ina sonta”. Tunda yake bai taba fadawa a tarkon son ko wace “ya” mace ba domin kuwa shi burinsa daya ne a duniya ya zama cikakken dan sanda mai gaskiya da rikon amana, sam bai dauki soyayya da wani matsayi ba, shi a ganinsa zata zama kashin baya ne wajen ruguza masa burin sa. Runtse idanunsa yayi ya danyi tsaki, ba damuwa ai naji ance soyayya a hankali take shiga a cikin zuciya, kuma ma koda banajin ina sonta a cikin zuciyata, bana kuma jin bana sonta, Bilkisu yarinyace mai hankali gata kuwa da ilimi, don haka inada yakinin cewa insha Allah zanji dadin kasaan cewa da ita. A haka yaci gaba da sake-sake har bacci yayi awon gaba dashi.
SHIN WANENE SULEIMAN? Sulaiman dai saurayine kyakkawa na gaban kwatance, dogo ne, fari tas irin kuwa farin larabawa, yanada saje, wanda ya kara fitar masa da kyan fuskarshi, ba domin wannan sunanshi Sulaiman ba kuma a Najeriya yake da idan ka kalli film din (student of the year) na indiyan nan, zaka zata tawaye ne da siddhart malhutra dayan saurian Alia batt wanda ya aure ta a fim din akan matsanancin kamar da suka yi dashi.Washe garin wannan rana da dare Sulaiman ya shirya cikin riga da wando kaftan jar shadda ce tasha gawado harta gaji hulah baka ya saka da takalma bakake, ya fesa turare dan ubansu, gaban (dressing Mirro) yatsaya, ya dau mintoci yana kallon kanshi, kana yayi murmushi yasa kai ya wuce. Dama shigarsa kenan, ga baki daya baya sanya kananan kaya ba wai domin yana gudun ko ba zasu yi masa kyau ba a’a sai domin shi kwata-kwata basa cikin tsarin rayuwarsa. A dai-dai kofar gidansu Bilkusu ya tsaya bai wani dade ba, ya hango yaro ya aikashi yaje yayi masa kiran Bilkisu, Bai fi minti goma da wucewar yaron ba. Bilkisu ta fito, kanshi na a duke yana dannar wayarda ke rike a hannunsa, wani kamshin turare yaji mai matukar kanshi ya doki hancinsa, daga kanshi yayi, yayi arba da kykkyawar fuskar Bilkisu abin kamar hadin baki itama jan kaya ta saka duk da batayi wata kwalliya ba tayi matukar kyawo, ya yadade yana ganin Bilkisu unguwarsu daya tun tana karama har ya zuwa yanzu data girma amma bai tabajin tayi masa kwarjini ba sai a yau. Sallama tayi ya amsa mata ta gaidashi, har yanzu bata kalleshi ba, lafiya kalau yasu Umma, sai a wannan karon ta daga kanta ta kalleshi dam! taji gabanta ya fadi batareda tasan dalilin faruwar hakan ba, Gaskiya shigarshi ta burge ta tanason namiji mai shiga irinta kamala, tasha gwagwarmaya da Usman dinta akan ya rika saka manyan kaya, amma shi ba kamar Sulaiman ba yafi son kananan kaya duk da can ba’a rasaba yakansa manyan kaya ya gwammace yasanya kananan kaya na naira dubu goma riga da wando kawai sunfi mishi akan ya sanya shaddar dubu biyar. Amma kuma halinsu sam ba dayaba shi Usman yarone dan kwalisa mai cike da takama da nuna isa, sabanin shi Sulaiman da kwata-kwata wannan bai dame shi ba, sunyi firarsu irinta masu hali iri daya, kowa ba gwani bane wajen iya sarrafa harshe da zuba zance, sai dai abinda ya burge su dukan kasancewar kusan halayensu ma duka iri daya ne, kuma su dukansu sun kai matuka wajen iya mutanta juna, a haka suka yi bankwana suka watse tare da musanyar lambobin wayar juna.Sannu a hankali suka rika sabawa da junansu har ta kai daya baya so yayi kwana biyu ba tareda yaga dan uwansa ba.Sun shaku matuka a cikin yan kwana kinda sukayi har ta kai ga kowannen su yana shakkar zuciyarsa akan cewa anya! ba son dan uwansa yakeyi ba?
Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a dade ba’a kai ba, masu iya Magana kance lokaci abokin tafiya wanda baya jiran kowa.A yau ne aka daura auren Sulaiman Haliru Moh’d da Bilkisu Ibrahim Khalil. Anyi biki an kuma tofa Fatiha an kai amarya dakin angonta, su Asiya baki baya rufewa kawarta tayi aure.Wannan rana itace rana mai matukar muhimmanci a garesu domin kuwa sun cimma wani matsayi na Rayuwa. Salamu alaiki ango ne ya shigo dakin amaryarsa mai kamshi da sheki kamar wata zinariya, tashi sukayi, sukayi raka’a biyu kamar yadda shugaban Halitta ya umurta, suka nemi Allah ya sanya Albarka da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin su. Zaune suke da junansu lafiya bakajin tsakaninsu, hakika su karan kansu sun san sun shiga cikin wata duniya, wannan kuwa ba ko wace duniya bace face duniyar soyayya da tsananin begen juna. Satinsu daya a garinsu wato Bauchi suka gangami nasu ya nasu suka cilla ya zuwa Kaduna inda aka tura Sulaiman da aiki.Bilkisu taci kuka kamar ba gobe, gani take kamar ba zata dawo ba dakyar ango ya iya shawo kanta ta hakura dole, sun sauka ne a wani hotel anan cikin garin Kadunar, kasancewar sai dare suka sauka. Washe gari Sulaiman yaje ya nemo musu gidan haya.Da fara’ar sa ya gayawa Juliet dinshi sun samu gida mai kyau dai-dai su kuma yana da tabbacin zata so gidan matuka, abinda ma yafi burgeshi da gidan shine irin (self content) dinnan ne wanda komai akwai ciki,su gado,kujeri, katifa kai komai ma akwai aciki. Itama Bilkisu ba karamar murna da farinciki tayi ba tun kan ma taga gidan.Sai yanzu Bilkisu ta tabbatar da abinda mijinta yace gaskiya gidan yayi sosai. Da isarsu basu tsaya wata-wata ba suka fara aikin gyara gida baji ba gani duk da yake Sulaiman ya samo musu wa’yanda zasu taimaka musu da aikin.Bayan sun kamala gyara komai, Sulaiman ya biya wa’yanda ya dauko domin su tayasu gyaran gidan. Gida yayi kyau matuqa gwanin ban sha’awa da shi ko’ina ka duba kyal-kyal kawai yake kasancewar tiles (tayis) ne fari sol dukan gidan mai kyan gaske ne. Farkon gidan wani gate ne mai qayatarwa, idan kuwa ka shigo cikin kitchen. Gaba kuwa idan ka fito tsakiyar falon gabas da falon bedroom kenan wanda yake dauke da matattakalai guda biyu kafin ka shiga, bima’ana kofar nada dan tsawo kadan, a cikin bedroom din kuwa akwai toilet. Duka wayannan dakunan wuri daya suke, sai dai kuma wani dan wuri da akayi kamar wurin wanke-wanke, dan korido ne akayi mai dan tsawo. Idan ka shiga cikin wurin zaka hadu da wani daki a can karshe wanda ga dukan alama (Store) ne, a gefenshi ne akayi wurin wanke-wanke tareda fanfo da kuma inda ruwa zai fita waje, ya fada cikin (Suck-Away), kai a gaskiya gidan yayi matuka. Bayanda suka kare gyara, Sulaiman ya tafi ya siyo musu abinda zasu ci da kuma kayan abinci ma’ana (Provision). Fitarsa keda wuya ta dawo falo ta dan kwanta saman kujera ta kishingida akan doguwar kujera. A hankali aka fara jan kujerar da take kai, ta yanda ba za’a tada ta daga baccin da takeyi ba, daga bisani kuwa kujerar ta daga sama chak da ita batare da wani bil’adama ya dauketa ba, ita dai kujerar da kanta ta cira kanta da kasa ta nufaci kofar falon, adai-dai wurin ta ajiye kanta. Sannu a hankali harta kai a kasa, ba tareda Bilkisu ta koda motsa ba. Sulaiman ne ya dawo,bude kofar da zaiyi sai yaji kamar wani abu ya danne kofar,iza kofar ya sakeyi amma a wannan karon da duka iya karfinsa, aiko sai ga Bilkisu a kasa rim!.Da saurinsa ya shigo a falon ya taimaka mata ta tashi. Har goshinta ya fashe da jini, sakamakon tayis dake wurin kuma ba kadan ta fadi ba. Meya kawoki a nan Bilkisu, Sulaiman ne ya fada yana mai cike da matukar mamaki.Itama dai Bilkisun rasa ta cewa tayi, tsananin mamaki da al’ajabi ya dabaibayeta. Sai can ta samu tace nima bansan yanda akayi nazo……….. bata samu damar ida maganar da takeyi ba Sulaiman ya fashe da dariya key’ an mata ki fadi gaskiya, ke dai kinga ba kowa a gidan sai kikaji tsoro shine kika janyo kujera, kika kawo bakin kofar falo kina gadi, kafin ayi haka bacci ya kwasheki. Yaci gaba da dariyarsa batare da ya lura ta bashi ansa ba, murmushin yake kawai tayi tace to naji tunda haka kace.Amma har a zuciyarta tasan ba hakan bane, tasan ba anna ta kwanta ba, lallai wanna abin da ban mamaki yake, ita inama take iya daukan wannan kujera mai matukar nauyi, amma nan a take ta share da maganar a ranta, ta karbi kayanda Sulaiman ya siyo, shima kuwa ya taimaka mata wurin aje ko wane abinci inda ya dace. Lebara ya samu suka shigo da sauran kayan abincin sannan suka mayarda kujerar mahallinta na da. Bayan sun kammala cin abincin daya siyo musu, suka dan kunna kallo farin wata (T.V) suka sa amma kwatakwata hankalinsu baya kan kallon.Hira suke abin gwanin ban sha’awa. Bilkisu kinga gida yayi ko? Eh wallahi abin sam barka, naji mamakin yadda muka sami gidan nan acikin farashi mai sauki haka, sai kace dai kyauta aka bamu. Murmushi yayi yace nima dai abinda na gani kenan, mutumin yayi muna rangwame sosai, kuma fa duba duk da kayan nan dake ciki bankara da yadda na gaya mikiba. Nima fah (Dearest) kaga abinda ya qara burgeni kenan, mutumin ya yi muna rangwame sosai wai ashe dama ana haka, abawa mutum hayar gida harda kayan dake ciki? Dariya ya farayi kafin nan ya bata ansa, ke malama ba wai harda kayan duk haya bane, kayan. Duk Month zan riqa bada wani abu har in biya ga baki daya, kinga kenan sun zama namu.. Oho! Yanzu na fahimta itama ta danyi dariya. Duba agogon dake jikin bango yayi kai ashe dare yayi itama dagowa tayi ta gani ai kuwa.To bari naje na kwanta kinsan gobe zan koma kan aikina. Nasan kuwa ke sha daya da rabi ake fara series dinda kike so ko? Don haka na barki lafiya. Mikewa tayi itama. Ka manta ai yau Lahadi, basa kuwa yi ranar weekend sai gobe. Kwarai kuwa hakane kinga harna manta Wurin kayan kallon ta nufa ta kashe sannan tabishi suka wuce bedroom suka kwanta. Da asuba Sulaiman ya fara tashi kasancewar dama ita Bilkisu a gajiye take kan gyaran gidan da sukayi. Sai da ya fara shiga toilet ya dora alwala sannan ya tayarda ita domin itama tayi sallah daga bisani ya wuce masallaci tashi tayi tayi alwala tayi Sallah ta fada kicin tayi musu (break fast) koda tafito Sulaiman ya dawo sai ta kwaso abincin ta kawo dani taje ta gaida shi da kwana sannan ta gaya masa ga ( break fast) nan (ready). Tasowa yayi suka dunguma sai (dany) sukayi kari lafiya qalau ta dauki kwanuka taje ta wanke ta fara wankan kwanukan kenan a dai-dai farkon korido taji kamar mutum ya tsaya yana kallonta irin kaji nauyin mutum hakannan. Juyawar da zatayi sai taga ba kowa ta danyi shiru kadan kamar mai nazari sai kuma ta juya taci gaba da wanke-wankenta sake jin tayi mutum a bayanta a wannan karon ba’a tsaya a farkon koridon ba, da karfi ta juya kuma sai taga ba kowa, tattara kwanukan tayi duka zata juya ta waiga sai kawai taji nauyin mutum gaf da ita da azama ta wuce da karfin tsiya dogon numfashi taja da ta ga sulaiman ne tsaye yake kallon ta a wannan karon lafiya dai naga kamar a firgice kike? Lafiya qalau ta fada tana mai dan yin murmushi. Zoki dan taimakamin ki gogemin takalmana please kinsan sauri nake karna makara ta kammala goge masa takalma a dai-dai lokacin da ya gama sanya (uniform) dinshi karbawa ya yi ya sanya tare da fadar (thanks you) ya kika ganni yayi tsaye yana kallonta, kayi kyau sosai Sir! tare da sare masa, dariya sukayi su duka. Ta rakashi ya wuce ita kuwa ta dawo. Ta kunna kallo ta zauna a falo abinta. Ba’a jima ba ta tashi taje tayi musu abinci, tayi wanka ta dawo falo taci gaba da kallo (Rimote) ta jawo ta canja tasha zuwa Zee cinema inda tayi sa’a ana bugun number fara wani film kenan. Kallo takeyi gaba dayan hankalinta yana kan (T.V) sai gani tayi wani bakin fata ya taso ya rufe camera gabaki daya to me yakawo bakin mutum a Indian Film kuma Ita dai tunda tafara kallo bata ga an nuna shiba sai yanzu kuwa gashi yazo ya rufe t.v ga baki daya shi ka dai ake gani.Ke! da karfi bakin mutumin ya fada. Ke kuma a Indian film din? Ke! Dake fah nike yi, bude idanu tayi gwala-gwala tana kallon ikon Allah. Ke!! ya daka tsawa har sai da ta zabura ke maigado dake akeyi ko ke kurma ce, da karfi ta tashi tana mai ja da baya-baya. Don Allah malama kije ki budewa mai gidanki gashinan shigo----- bata jira ya idar ba ta yanka da gudu tsoro taji na fitar arziki da karfi ta bude kofa da nufin gudu aiko nan taji kafarta ta juye sai fadawa tayi kan wani abu a hankali ta bude idanuwanta mijinta Sulaiman ta gani lafiya lafiya? Bilkisu meya faru kika sheko haka me ya biyoki ne kuka ta farayi Zee cinema ……. Ta kasa fadin kome kara fashewa tayi da matsanancin kuka da kyar ta yadda suka shiga cikin Falo. Abin mamaki kuwa kayan kallo ma a kashe suke yaje ya zaunarda ita akan kujera ya bude firji ya dauko mata ruwa masu sanyi ya bata kuka kawai takeyi da kyar ya samu tasha sannan ya zauna a kusa da ita yana mai lallashinta da kyar da sidin goshi ya samu tayi shiru ta daina kuka ya tambayeta miya faru ta kwashe labari ta gaya masa. Kamar almara yaji abin amma da yaga taji tsoro matuka sai ya kanne bai nuna ba, addua’a yayi ya tofa mata akai sannan yace a duk sanda taji tsoro ba kuka zatayiba ta ringa fadar la ilaha illa antas subuhanaka inni kuntu mai nazzalimin, da kuma Ayatul kursiyyu ba komi bane face shedan yakeso yayi wasa da hankalinki, ki rike addu’a insha Allahu bake ba sake jin wani tsoro a gidannan. Ta dan samu kwanciyar hankali sannan yace taje ta samu bacci sannan ya fito Falo ya dibi abinci da kanshi yaci. Tun daga wannan rana ta riqe addu’oi baji ba gani duk da yake wani Sa’i takanji kamar an tsaya mata akai ko kuma taji kamar idan tana tafiya ana binta a baya ko taji an wulgo da karfi haka dai abubuwa suka ci gaba da faruwa.
Suna zaman su lafiya da Sulaiman abin sai ace san barka. Misalin karfe sha daya na dare yaji ana tadashi daga barci buda ido yayi, me zai gani farin cikin rayuwarsa ce Bilkisu a tsaye taci ado da wadansu kananan kaya masu jan hankali, tasha kwalliya ta fitar hankali sai kamshi takeyi mai matsanancin dadi tsaye take tanayi masa wani mayen kallo ai kuwa bai san sa’ada ya tashi zumbur ya mike ba, ta dan ja baya kadan ta bude hannuwanta biyu alamar yazo, saikuwa yayi kai tsaye inda take amma sai ta goce tana mai yi masa dariya. Au ni zaki wasawa haka da gudu ya bita suka fada sai a falo da gadunshi a tsaye yayi chak----- sakamakon ganin Bilkisun shi zaune a falo tana kallon Series dinda take kallo ko yaushe mai makon tufafin da ya biyota dasu kuwa rigar baccin da yasan Balkisu da ita itace sanye a a jikinta da saurinta ta mike da sauri lafiya dearest me ya faru naga ka shigo haka da gudu lafiya. Bai samu ta cewa komai ba mamakin ya hanashi Magana ga baki daya sai a ranshi yake Magana ba yanzu na biyo Bilkisu da gudu ba, idan dai ga Bilkisu nan a zaune to waccan wacece na biyo kafin ya samu amsar wadannan tambayoyi na Bilkisu, ta sake tambayarsa lafiya baka ce komai ba, menene? Murmushin yake yayi yace babu komai amma da yaga Bilkisu na tantamar abinda ya fada sai yace mafarki yayi wai tana nakuda akace ya sheka ya kira likita shine ya shigo wai, dauka ta gaskiya ne. fashewa tayi da dariya tare da ajiyar zuciya dauke indonta tayi akan nashi yanzu dan wannan gudunne zakayi in akace ka kira likita? Dariya kawai yayi batare da ya bata amsa ba, zuwa yayi ya kashe kayan kallon, chak ya dauketa, dama dariyar takeyi harda ma shakewa, Malama (is time for bed now), sai daki ya ajiyeta ya maida kofa ya rufe. Gobe (workers day) kamar kullum ma’aikata suna hutu, Sulaiman tunda safe yasa Bilkisun shi tayi musu girki mai dan yawa yaje ya dauko motar ofishinsu ya dauke ta sai babban (park) din kaduna sun yi nishadi sosai. A can basu wani dade da zuwa ba, yace bari ya daukota su zaga gari domin taga Kaduna tunda yau (free) yake a cewarsa yau wata babbar damace daya samu, anan take kuwa Bilkisu ta amince da wannan shwarar, sun zazzagaya wurare da dama balkisu ta bude ido, a gaskiya Kaduna babban birni ne mai kyan gaske. Bari muje bakin ruwa ko Balkisu? Da hanzari ta amsa masa da eh muje, dama kamar yasan abinda yake rantane ba abinda Balkisu keso daya wuce wurin ruwa. Tafiya suke kowane ranshi cike da farin ciki, ‘yar fira suke gwanin ban sha’awa. “Wai ni ko in tambaye ka mana” Balkisu ta fada tare da kallon Sulaiman, eh ina saurarenki yace batare da ya kalleta ba kasancewa driving dinda yakeyi, halama dai baka son zama cikin mutane ne? Me yasa kike fadi haka? Sulaiman tare da yi mata wani kallo mai dauka da alamar tambaya kawai dai naga daka tashi nema mana gida ne sai ka nemi layin daba mutane a cikin sa mutane saura duk irin gidajen nan ne na manyan yan siyasa da suka yi domin kawai idan sun shaqi iska suzo suyi dan hutun sati biyu su koma ni ma tunda nazo duka gidajen da ke side dinmu masu gidan ko sau daya basu taba zuwa ba, sai kuma sau daya gidan da muke (facing) suka zo suma basufi (two weeks) ba suka wuce, su kuma gidajen nan hudu da suke akwai mutane aciki uku duk (cristian) ne fah. dayan kawai ne musulmai su Khadija da Fatima kuma suma bawai kusa da gidanmu suke ba. Hakane amma ba yanda kike nufi bane, me zai/sa na ki son zama acikin mutane bayan cikin mutane na tashi, Allah dai ya nufa nan zamu zauna shi yasa, kuma banda abinki ba gani ba koda bamuda maqota ai kullum ina tare dake kamar inuwa ya fada tare da murmushi itama murmushin tayi, hakane (Dear) af dazu ko na manta na gayama Umma ta kira tace na gaisheka, ina amsawa ko mutanen gidan ina fatar kowa lafiya, lafiya qalau, madallah,, Bilkisu mun iso, a dai-dai lokacin da suka iso wurin ruwa yayi parking ya fito ya budewa Bilkisu itama ta fito tare da fadin (thank u) bude boot din mota yayi yafito musu da babban (carpet), ita kuwa Bilkisu ta bude sit din baya ta dauko abinci wuri suka nema mai ni’ima suka shinfida suka zauna, bilkisu ta dibar masu abinci suka ci, kasan garin Kaduna baban birni ne dab a wanda ya kula da wani, bayan sun kamala cin abinci suka dan taba hira irinta miji da mata suna tsakiyar firar ce Sulaiman ya hangi mai sayadda Tuffa wato (Apple), Bilkisu bari naje na siyo mana apple yanzu na dawo, ya tashi ya nufi wurin wai sayadda Apple, kai mai Apple nawa Apple, din, ya sayi apple din ya miqa masa kudi ya jira shi ya bashi canji, juyowar da zaiyi ya dubi gurinda Bilkisu take, me zai gani ya gani wata mata sani dai-dai sa’ar Bilkisu ta rige Balkisu a tsakiyar ruwa tana nutsar da kanta da gudu ya rugu ya watsar da (Apples) dinda ya siyo Bilkisu!Bilkisu! gudun yake yana kiran sunanta, ita kuwa wannan matar a dai-dai lokacin ta nutsar da ita gamin da tsoma kanta cikin ruwa Bilkisu nata kokari amma a wanna karon sai ganin yayi kafafuwanta dake motsi sun daina, har yanzu matsanancin dugu yakeyi yana kiran sunan Bilkisu, bai Ankara ba sai ji yayi tuntube sai kasa ya fadi ya wuntsila duk da haka mikewa yayi da sauri ya sake ruga wa. Ga baki daya mutanene da ke wurin kallan sa suke yi, ji yayi, kamar daga sama murayan Balkisu a bayan shi, bai fasa gudunda yake yi ba, ya dan juyo kadan, me zai gani Balkisu ce kuwa take binsa da gudu tana kiran sunan sa tsaye yayi duba cikin ruwa yayi a inda yaga wata tana kokarin kashe masa Balkisu shi, ba kowa wurin lokacinda ya juyo inda Balkisu ke gudu tana kiranshi, har balkisu ma ta karaso idonta cike da kwallah ganin irin mummunan faduwar da yayi, da zuwa rungume shi tayi ta fashe da kuka lafiya Dearest mike faruwa gani ana, ina inda ka barni banje ko inaba meke faruwa? da kyar ya hada yawu da suka lake masa, numfashi yake sama-sama Alhamdulillahi Balkisu tunda kina lafiya ba abinda ya sameki, dauko kaya mu wuce yanzu-yanzun nan kasa Magana yayi, ga baki daya mai Apple ne ya iso bakin mota, Alhaji ga canjin ka fa da Apple din da ka saya, said a Sulaiman ya dan tsaya kamar mai nazari sanna ya ansa, ya wuce ya bude mota ya tada suka wuce gida, ba wanda yake Magana a cikinsu. Ita Bilkisu tunanin ta keyin ya akayi mutum ya barta zaune sanna ya dawo a guje yana kiran sunanta har da wannan irin faduwa haka? wadda tayi sanadiyar daya fasa. Hancin sada jinni mike damin Dearest dinta me ya gani ne haka lallai koma meye ba lafiya ba, amma ba yanzu ya dace tayi masa Magana ba kamata yayi ta bari sai sun iso gida hankalinshi ya kwanta sannan, domin yanzu yana cikin rudu da fargaba. Shi kuwa a bangaren Sulaimn ga baki daya kansa ya kwance stabbas yaga wata tana yunkurin kasha balkisu yasan lallai yaga haka to amma kuma ya akayi bayan da ya sake dubawa yaga ba hakanan bane, idan dai balkisu na can a inda ya barta da yaje sayen Apple to waccan da ya gani wace? Wacce wadda kuma ta yi yunkurin kashe waccan Balkisu? anser day a kasa ganewa kenan har ya iso gida bayan ya shiga ya bude gate ya shiga da mota ya kulle gate ya dawo, ya taradda Bilkisu na jiranshi a kofa suka shiga taje, kai tsaye ta dauko first aid box ta bashi taimakon gaggawa, taje ta mayar da magungunan ta kuma biyo mashi da ruwan sanyi, ya ansa yasha, bayan kamar minti biyar ba wanda yace uffan sai Bilkisu ta katse shirun da tambayar shi ko lafiya game da abinda ya faru dazu? Ya so ya gaya mata sai kuma ya tuno da cewa Balkisu mace ce idan ya fada mata zai kara dagula lissafi ne kawai. Domin haka yace ta barshi ba komai bane amma sam taki amincewa da haka, da dai yaga tanace akan sai ya fada mata sai ya maida abin ba’a yace yana ganin sonta ne yake neman zautar dashi, duk da ta san ba haka bane ama sai murmushi ta sharer da maganar kamar yadda. Taga baya son zancen, tun daga wannan lokacin bata sake tamabayarshi ba kuma, yayi kamar sati baya wani sakewa sosai ko office yaje zai yita kiranta yaji ko lafiya, amma sannu a hankali anaka manata da wannan abu komai ya dawo normal a kaci gaba da yadda aka saba, yau asabar su Balkisu sukayi baki abokanshi Nuhu dashi da matarshi a gidansu, suke wuni sai bayan magariba suka wuce tare da alkwarin suma wani sa’I zasu je suyi masu yini kamar suma yadda suke yi masu. Bayan wuce war su Nuhu Sulaiman yasa Balkisu tad an dafa masa abinda zasu ci domin ba sauran abinci a gidan kasancewar bakin da sukayi sunada zara, kitchen ta shiga ta daura abinci macaroni ce yar two minute ta aza musu, ta dauko timatir fresh tana yankawa harma ta kusa kareyankawar, daya kawai yayi saura maid an girma haka, yanka wanda zatayi sai kawai taga jinni ya fito cikin tumatirin, sake dubawa tayi kamar dai wadda ta tashi daga mafarki. Tabbas haka dinne jinni ke zuba daga jikin tumatirinda ta yanka, baya-baya ta farayi tana duba ttimatirin me zata gani saurantimatirin data yanaka ga baki daya wasu irin tsutsoci ne ke fitowa daga garesu ta ko ina kara yi tayi da baya tana shirin guduwa sai kawai tayi kicibis da Sulaiman, lafiya? A firgice sai juyawa tayi tana nuna timatir din. Me ya faru yankewa kikayi wajen yanke timatirin ko shiru tayi ta kasa cewa kome a, sakakamakon ganin timatirin da tayi lafiya kalau ba abinda ya same shi, ba wani jinni bare kuma wasu tsutsoci dake sukuwar sallah a sama a.a da rasa ta fada tayi to meyee haka? mike faruwa ne day a dauki tumatitrin abinda take fada bay a dauki tumatirin da kanshi yasa cikin tukunya ya juya kinga jeki zauna yau zakici girki mai dadin da baki saba cin irinshi ba, kasa tafiya tayi saida yazo ya fitar da ita da kanshi Sulaiman ne yayi masu sanwa sam bata iya cin abincin da kyarya matsa mata ta danci kadan, abincin ba, ku fa mata haka kuke idan kamala shirin ba, ku fa mata haka kuke idan dai mutum yace ya jira ku to shi kuwa sai ya shiga uku da jira Sulaiman ya yakema Bilkisu bita, na kare ranak ya dake muje ta fada tana dariya tare suka fita suka kulle gida ya dauketa wurin saloon suka, nufa can kan titin shigowa layin su. Sai a bakin shagon ya ajeta tare da bata kudin saloon din har ma da Karin, idan aka kare sai ki kirani sinzo na mai dake gida murmushi tayi tareda fadin nan wurin ne har sai ka dawo daga office dinku ka mayarda ni sanna ka koma? Malam ko cikin dare ne ai zan iya mayadda kaina ballantana zanzu da rana kiri-kiri. Shima murmushi yayi yace to kinga laifina ne ina tsoron kada ki bata ne kinsan Kaduna da fadi idan kika bata a in azan nemoki, har ganoni ne wani abin wahala ni ai ko a brining sin ka bat azan nemoka, ke kin kuwa san ko inane birnin sin kinsan yawan mutanen da ke cikinta, Dearest bari ta yawan mutane ko a Birnin ALJANU DA FATALWA ka bata wallahi ni Blkisu sai na nemoka koda kuwa zan rasa rayuwata ne. wani irin dadi Sulaiman yaji musamman da yayji irin tsantsar kaunar da Balkisun shi take mishi, allah ko matata? Ya tambaya yana main zolayanta ko shakka babu ta fada tare da taba kundar ta suduka suka fashe da dariya, to bari na wuce office kar naje na dade na bata nasa matata cikin wahalar nemana, sake fashewa sukayi da dariya ya tada mashin dinshi bye love ya fada tare da kashe mata ido daya murmushi tayi see you soon ta sfada ta kuma hanyar shiga cikin shagon saloon din, sai da ta shiga cikin shagon sanna ta juyo shima Sulaiman a dai-dai lokacin ya juyo suka hada ido dariya yayi ya daga mata hannu alaman bye bye sanna ya juya yaci gaba da tukin mashin dinda yake yi, murmushi kawai tayi ta karasa shiga cikin shagon excuse wata mata ta amsa da yes shigo. Sannu fa ga wuri ki zauna ta zauna, ta zauna tareda fadin nagde me kikeso ne madam inji mai shagon saloon sdin nazo sa mai ne okey bada bata lokaci ba ta fara cikinta shigar Bilkisu drayer kada wuya sai ga wata syarinya yar kimanin shekara sa takwas ta shigo a cikin shagon da gani basai ka tambaya ba kasan ‘yar mai shgon ce domin tsananin kamarsu day abaci said a ta gaida Balkisu sannan ta koma kan maaifiyarta dauke take da kwan abinci da kuma wani jug da drinks aciki, mummy ga abincin na qare ni zan koma shagon, wani dan karamin siket ne iya gwaiwa tasa duk ilahirin jikinta a fili kai gaskiya ya musulunci nada dadi shine addinin dake mutunta ‘ya mace ya kare darajar ta da martabarta. Ita dai madam abincin wanda ke nuni da da cewa dama a jiraye, take malama muna kwarya fa please kici abinci a’a nagode wallahi, kici kawai ni a koshenake kallon abincin tayi, ta kasa gano ainihin menene kamar soyayyar doya amma kuma abin ya banbanta to meye haka gwanin ban sha’awa, taso tayi shuru sai kuma ta tuna matambayi baya bata kuma ma ai karuwanta ne, madam menene haka kamar soyeyyar doya domin saloon shi zanyiba, irin na soyayyar doyar doya bace. Haka ne wannan ba doya ta mikawa Balkisu kici kiji yanda yake yafi doya soyyaya dadi sossai da kyar balkisu taci aiko gaskiyarta gaskiya abinnan nada dadi sosai ya akeyin shi ne Madam. Bata jira ta kammala cin abincinta ba ta fara gayamata farko zaki dan dafa doyanki amma kada ya dafu sosai, kamar irin far-builing dinta tattasai da albasa, sai kuma ki fasa kwanki kisa spices dinki ki gurje, doya da kika sauke kuwa sai ki gujeta kaman yanda kike gurje yakuwa, ba wai yayi gari ba kinsan bata wani dafu ba, bayan kin gama gogewa sai ki zuba tarugunki da tattasai da kika daka tun farko ki gauraya ko’ina yaji, ji dan kara species dinki bada yawa ba sai ki kawo kwanki ki zuba ciki, shine ki gauyraya, sai ki samu leda kisa kamar dai yadda akeyi alala ki kulle ba sosai ba sai ki saka a ruwa zafi kamar zakiyi alala idan yayi da kin duba zaki gane, sai ki fitar kiyi masa shape din da kike so. Great gaskiya nagode, fah madam na karu sosai thank you onces a gain Bilkisu ce ta fada, madam kuwa sai faman budar baki takeyi itafa nan ganin yake ta burge. Sosai, no ai wannan is notting, shiru tayi kamar wadda ta tuna wani abu sai kawai ta tsayyoma drinks dinda yake cikin jug Balkisu ta kawowa malama ga wannan kisha ‘yar gajeruwar dariya balkisu tasa a’a gaskiya ki barshi kawai nagode ko wancan dana ci domin nasan ya dafuwanshi yake idan na dafa ne ki barshi nagode Allah. Malama Balkisu meyasa nace kisha ba ko wannan drinks din hadashi akayi kuma yanada dadi, sosai nasan mai gidanki zai so shi sossai shiru Balkisu tayi cikin ranta tana dariyar madam domin tasan wannan ba komai bane face dadin yabon da tayi Balkisu tayi mata, zugata da taji anyi duk shi ya janyo takeso ta kara nunawa Balkisu ita ce kwaruwa ce wujen iya girke-girke. Karba kofi kawai tayi ba tareda tasha ba drinks din menene na cocumber ne da kwakwa a lokacin ta dan ka baki ta kurba kai? Gaskiya shima ya hadu. Cocumber da kwakwa shi kuwa ya ya akeyin shi, ai madam bata jira ta kammala maganar da takeyiba ta soma; farko ki fere cocumber ki sai ki yayyanka ki saka a bander ki blende ta sai ta blendu. Sosai sai ki kawo kwakwa itama ki blader ta cikin cocumber idan kuma kin gama kina iya blande su tare, sai ki saka madara a ciki kisa cikin frige shikenan kin hada drinks dinki, kuma wani abin burgewa das hi drink dinnan bawai kawai dadin shi kesa ayi shi ba a’a yanada matukar amfani a jiki sossai. Gaskiya madam nagode sosai naji dadin zuwa saloon wurinki domin na karu da abubauwa sosai, kinga yanzu ko kina karemun gyara kai na zanje nayi abubuwannan da kika koyamin sauri karemin naje so drink suka fashe da dariya, madam ko ta gyara mata Kanata fes-fes gwanin ban sha’awar har bakin shago ta rakayota sukayi bankwana Balkisu ta wuce. Bata zame a ko’ina ba sai gidan su khadija da Fatima yan layinsu can ta nufa tayi kwatanta mata inda ake sayerda kwa-kwa domin duk abinda zatayi aiki dashi tanada kwa-kwace kawai batada, tayi kokarin kiran Sulaiman a waya Switchup tana sane ta gayamai zataje wani wuri ba zata dade da text, Sulaiman dinne yake gayamata zai kai dare kada ta jirashi akwai meeting dinda zasuji ne kuma ba dole zai kasha wayanshi sauke nunfashi kawai tayi kutsa kai gidan su Khadija da Sallamarta Fatima kadai ta cimma Khadija batanan ta fita anguwa, tayi sa’a yar cikinsu Habiba nanan kuwa, ita ta aika ta siyomata,, ita kuma ta koma gida, kai tsaye ta nufi daki ta saukar da akwatuna gaba daya ta bude ta kasan sai data fitarda rabin kayan sanna ta kai ga wasu tulin kanan kaya ma’aita English wears, said a tad an tsya zabe sanna ta ciro wasu jajayen sun hadu matuka murmushi ta saki, lallai aminiyarta gwaruwace duk ita ta saya mata kananan kayan nan dama a inda ta dialiara kenan Asikhan? Asikhan ta fada tana dariya ta tuna irin mitarda tayi mata game da kayannan data saya mata, da gaskiyar aminiyartata duk cikin kayan ba Wanda bai kai matuka ba wurin kyau, kai wai ita Asikhan tana da kayanda tabawa muhimmanci ne da suka wuce kananan kaya? Dariya kawai tayi ta ajiye wadanda ta ciro Akan gado ta shiga mayadda sauran kaya ta maida akwatuna yadda suke, sannan ta fara gyaran gida ta shiga aiki tukuru baji ba gani tad an canga wasu kuwa duka ta maidasu falo ta bubbuga, komi yayi gwani ban sha’a. daganan kuma ta fada kitchien ta fara ferewn doya kenan taji bugun kofa da sauri ta nufaci kofa koda ta bude Habiba ta gani da abinda ta aiketa ansawa tayi, ta kuma yi mata godiya Habiba ta miko mata sauran canji naira talatin ne suka rage ki barshi kawai ki dauka na bakai in kinje kice ina gadasu kinji nagode Habiba tace tareda washe baki zasuji nagode Amarya ta sake fada, murmushi kawai balkisu tayi ta rufe kofa ta koma bakin aiki bata manta ba yadda madam ta gayamata haka tayi, kamar ko ba ranar ta farayi ba domin tayi dai-dai yadda akeso koma tayi kyau sosai ta fidda shape dinda takeso ta rufe a kula ta kai dany ta hada drinks dinta a hakikanin gaskiya yau ta aikatu, ta kamala hada drinks dinne a kayi kiran magariba, ta saka shi afrige ta shiga bandaki ta doro alwala ayi sallah, bayan ta idar da sallah ta koma kitchen ta wanke kwanukan da tayi aiki dasu ta goge kitchen din, sannan ta nufi frige ta dauko kankara ta faffasa ta saka ta sake mayadda drinks din a cikin frige, kiran salla isha’I taji taje tayi sallah, ta cire kayanta ta nufi bathroom har takai kofar shiga toilet din kuma sai wani abu ya fado mata a rai, falo ta nufa ta bude kofar falon tad an iza kofar ta yadda idan mutum ya iso daya dan tura kofar zata bude sannan ta nufi daki ta rufe kofar dakin amma a wannan karon dakin kalloshi tayi ta yanda idan dai ba ita da take ciki ba ba wanda zai iya budewa, dariya ta saka sanna ta fada toilet tayi wanka abinta bayan ta kamala wankan a gaba dressing mirrow ta tsaya, tunanin irin kwalliyar da takeyi sanna ta zauna ta fara zuba kwalliya bata kammala kwaliyarada takeyi ba can a falo taji sllama dearest dinta, salamu alaikum Honey in Home ya kara fada dariya kawai tayi, tace gaba da kwalliyarda takeyi, kai waye daki ya nufa wai ina masu gidanne, za kofar dakin yayi ya kuwa jita gam a kulle, a,a Balkisu lafiya dariya ta sake sakawa malam kaje falo ka zauna zan fito nan da minti biyu shiru yayi duk mamaki ya cika shi as you wish my lady na fada ya komo falo ya zauna, sai kamshi kawai ya keji yana tashi, dama ko yunwa yakeji, ita kuwa Bilkisu saka kayanta takeyi ta bude yar karamar kit ta dauko agogo ja ta saka ta sake komawa a gaban dressing mirow ta kalli kanta masha Allah ita karan Kanata tasan ba karamin kyau tayi ba, hakika aminiyar tat a cancanci yabo wayanna kayan haka, wana murmushi ta sake, ta jayo turaruka kala-kala a fara yiwa kanta wanka dasu bancin na jikinda ta shafa kafin ta saka kayan kanshi ba’a cewa komai, kofa ta nufa ta bude a hankali sannanta leka wata yagogan mata ya kasa hakuri harya isa diny ya fara bude kula fitowa tayi ta tsaya ajikin kofar nade kafafuwanta tayi ta aza daya bisa daya sannan ta jigina a kan kofar hannunta kuwa dagashi tayi sama ta mannashi da bango, irin tsayinnan dai tayi nay aka gannine, irin wanda karishna kapoor tayi a cikin film din raja Hindustani wani kamshi ta doki hancin Sulaiman a yayinda yake kokarin bude kular da ganin fuskarshi yayi ya dubi inda kamshi ke fitowa, la haula wala kuwati illa billah!!! Mikewa yayi ai ya saki baki wacece wannan yake gani haka Bilkisu ce kallonta kawai ya keyi bakinshi a bude da murufin kula a hannu tazo tayi dariya amma kuma sai ta kanne wata irin tafiya takeyi kamar batason taka kasa karayraya jikinta takeyi ta yanda ko ina nata motsi yakeyi, frige ta nufa ta wani dan duka ta zaro jug dinda ta saka drinks a ciki, a saman frige din ta jayo kofunan jug din guda biyu ta nufo dany din. Har yanzu tsaye yake yana kallonta kamar wata baindiya yake ganinaka shi ga baki daya yama rasa me yake ciki, yama manta da yunwarda yakeji shin wai
Bilkisu ce haka, ajiye jug wani zaburar das hi. Cikin kissa da kisisina irinta wayayyin mata, sannan ta anshi murufin kular ta ajiye ta ciro flet ta zuba masu abinci ta ciro fork daya ta ajiye a gabanshi, gab aki daya rasa ta cewa yayi, to muna zaice daukar fook din yayi a sannan ne ya tuna da yunwarda yakeji ya fara cin abincin yana kai loma ta farko a baki lakuwati! Wani irin dadi yaji ya kamashi. Har kunne, ya kara dibo ta biyu ya ci sai a sannane ya lura Bilkisu bata ci, lafiya baka cin abincin ne ya tambaya yana kallonta bata fuska tayi kamar zatayi kuka dazu ne da ina fere doya na yanke hannuna Magana takeyi cikin salo irin na shagwaba, ajiye spoon din yayi mu gani sannu --- injin bakiji ciwoba sosai, bari na dauko first aid box da kyar ta kanne dariyar da tayi kokarin fito mata yanda taga yanayi abin gwanin ban dariya dan taliki dukya rude, a’a ka basrshi kawai ya daina yimin zafi sosai, to bari na baki abinci ko da sauri ya fada yana dubanta, dama haka takeso nufinta kenan, daga kai tayi cikin shagwaba tace to, ci yakeyi yana har said a su duka suka koshi, sanna ta tashi ta zagayo ta zuba drinks din a kofi ta tattako dai-dai inda yake said a ta wani kwanta mishi sanna ta fara bashi a baki, rasa duniyar da yake yayi da mai zaiji dadin drinks din ko kuwa Balkisu da take kokarin zautarda shi, nan take ya shanye, ta tambayeshi cikin wani irin kasha murya a karo tana wani murmushi mayen kallo daga kai kawai yayi batareda ya samu Kalmar eh ta fito ba, ta kara tsiya yamishi ta bashi a baki nanma ya shaye a karamaka ta sake tambaya sake daga kai yayi kamar wani dan karamin yaro wanda bai iya Magana ba, duk iya kannewanda tayi wannan karon said a tayi dariya ta yanda ba zai gane dashi take ba duk da tasan ya koshi baya dai iya cewa ya koshi ne said a ta fara tsiyayowa kafinta kai masa a baki, sai ji tayi ayi wani irin gyashi da kyar ta iya hadiye dariya tace anya Dearest baka kishi ba, na’am eh nakoshi gaskiya kam, saura ke mana kasha, daga kai tayi tareda fadin uhum ta tashi ta nufi kujerar ta a fara shan drinks din, kallonta yakeyi kamar bai taba, ganinta ba ita kuwa tana sha tana kallonshi yanda taga yanayi kamar zai hadiye ta saura kiris tag ware, tagama sai tace masa miasa na koshi, dan gajeren murmushi yayi tau, bata jira yace wani abuba ta fara daukan kaya tana kai kitchen, dama ai kin barsu sai gobe naga dare yayi kome kike gani, dare fah kace yanzu ko karfe tara tayi ne duba agogonshi yayi au da gaskiyarki fa tara da minti takwas ni ca nike dare yayi sosai goben na kai sauran wayanda bankai ba, shima murmushin yayi ba tareda yace komai ba, zo muje yau za’ayi wani film dinda nakeso sosai farin wata ta wuce kawai batareda ta jirashiba, da sauri ya taso ya biyota wane fil ne? Marokon zamani kasan ko sau nawa zan kalleshi bana gajiya taje ta kuma kayan kallo koda suka kawo harma an fara ta nemi go ta zauna shima ya zo kusa ta ita ya zauna, ta lura dashi, kamar yana so yayi wata Magana kawai yi tayi kamar bata ganeba, sai can yayi dan guntun tsaki, kinga nama manta banyi wanka ba, ni da nace ina zuwa ko abinci baznci ba zanyi Wanaka, dauko idanuwan ta tayi akan kallon da takeyi hakane fa kaga nima sam na manta, mikewa yayi yanufi dakii harda dan tuntubeshi, ya fada tailet yayi wanka sanna yasa wata doguwar riga baka ya dawo falo ya zauna wai yanzu naji wani irin iska yana shigowa juyowa tayi ay hark agama wankan, ita dai tasan baifi minti hudu da yabar falon ba wannan wane irin wankane haka ta danyi murmushi, eh harna kare mana ko kinga nayi sauri ne? a’a tambaya kawai nayi, wurin wani dariya akayi musa mai sana’a ne kun sanshi wajen iya acting dariya ta saka harda shakewa kallonta kawai yakeyi shi kwata-kwata baiga abin dariya acikinba sai a lokacin ya kula a yanda aka canza wasu abubuwa da yanda ta mayadda sauran lamination dinsu a falo, akice yau an canza tsarin gida oh! Wai sai yanzu kai ka gani dama ta fada tana dan noke kai gaskiya yayi kyau, murmushi kawai tayi, Bilkisu yau kinsha aiki, kika gyara gida haka sanna kuma kika dafa abinci da idan mutum yaci baya iya Magana akan dadi gaskiya im the luky husband in the whole universal kuma wai kinga yanda kikayi kyau kamar irin ‘yar tsawar nan Barbier kinyi kyau fiye da yanda kike tsmmani fah. Wani tashi tayi yanda tayi yana kodata haka, tashi yayi ya nufi inda take kashin kanta ya taba sannan kuma haka sai kace na indiyawannan dariya ta saka don Allah malam dadin bakin ya isa haka, Allah ba dadin baki nakeyi ba ni dai yau nama rasa me zanlawa tantaki dashi wurin haduwa murmushin dadi tayi tace “hauni” Balkisu kinsha aiki da yawa ya kamata ace kinje kin kwanta dariya ta yi tace waya gayama ba yaje ya kasha kayan kallo yace muje ka? Mikewa tayi tsaye amma sai duk ta wani langwabawa kamar zata fadi yadai yafada, kafafuwana ne sukeyimi nauyi cikin shagwaba, ai cak ya dauketa ya shiga daki. Balkisu ke faman gudu wani katon mutum yana binta kuwwa take ta faman bugawa amma ba kowa a wajen a jikin wani bango ta fada, shi kuwa katonan ya tsaya a gabanta ya rutseta kuwwa kawai take famanyi, hannu daya yasa ya shaketa a hannu dayan shi kuwawata irin wukace doguwa daga wukar yayi sama dana kokarin soka mata wukar yayi sama girgiza kai takeyi tana fadin a’a duk idanuwanta sun firfito alamun firgita, amma koa jikin katon nan, da karfi ya nasa mata wukar ta kwala uwar kara mai tsnanin karfi. Maigado!!! Da karfi ummah ta farka tana kururuwar kiran sunan diyarta firgigi shima malam iro ya fara a sakamakon hargowar da yaji matarshi tayi. Lafiya? Meke damuwanki? Me akayi? A firgice tace mai gado? Maigado! Wani ne da wuka -------- ta kasa idarda zancen duk ta firgita da ummunan mafarkinda tayi dakata ba sai kin fadi abinda kikayi mafarki ba sherin shedan ne kawai shi yakeso yayi wasa da tunaninki, tukunna ma dai kinyi addu’a ne kafin ki kwanta sai da tayi shiru na dan lokaci har a lokacin a firgice take sannan ta tuna da batayi addu’a ba a sakamakon dan kishin gidawa kawai tayi bacci ya shareta a’a banyi ba ta amsa masa kingani ko shedan ne kawai shi yasa addu’a takeda muhimmanci a rayuwar musulmi tayama za’ayi mususlmi ya kwanta baiyi addu’a ba wadda idan kayita ba aljani ba har mutum bai isa ya cutar maka ba, wallahi dan kishingidawa nayi bansan sa’adda ma bacci ya kwasheni ba malam, amma ina ganin kamar Bilkisu tana cikin wani mummunan haline ko kuma wani mummunan abu yana shirin faruwa da ita ni naji ----- don Allah kibar wayannan shirmen baxaki nemi wuri ki kwanta kawai daga kinyi mafarki, to ance miki mafarki gaskiyane, shifa mafarki kasha biyu ne, na alhairi daga Allah ne na sharri kuwa daga shedan Bilkisu na can lafiya kalau da mijinta ba ke kika gayamin da rana cewa ta kiraki kunri wata hart ace tana gaidani, ba? Daga kai kawai tayi alamar ah kiyi addu’a kawai ki kwanta Bilkisu na lafiya kalau ba kuma ba abinda zai same ta sai alkhari da iznin Allah. To malam, harta fara addu’a sai kuma ta juyo ta dubashi tace malam kanada kudi a waya na kirata naji hankalina zaifi kwanciya? Kira! Zanzu kinsan ko karfe nawa ki kira ta yanzu cikin wanna tsohon daren abin ma ai gwanin ba dariya, yarinya da mijin ta haka kawai ki kirasu yanzu ki tada masu da hankali ko, ba halin ta kara cewa wani abu domin ta lura maigidan nata ya fara hasala dole tayi addu’a ta kwanta ba domin tana jin wani bacci ba sai domin hakan ya zama dole gareta ne, sam bacci kasa daukar ta yayi ita kawai tasan abinda ta gani Allah dai ya nuna mata goobe da safe lafiya dole ta kira taji ya ake ciki. A bangaren malam iro kuwa tabbas yasan maid akin sa taji tsoro sosai dangane da mafarkinda tayi amma ba yadda zai yi dole wannan hanyar dayabi ita kadai zai yi domin ya tasa abin a zuciyanta karshe yazo ya dameta, Hmm koma da menene Allah ya fefaddashi ya juyoshi zuwa alkhairi amen haka dai yayi ta sake-sake ba tareda ya dade ba bacci yayi awon gaba dashi. Tunda sassafe ummata aika aka siyo mata kati ta bayar aka saka mata a waya number Bilkisu ta danna ta kira. Ita kuwa Bilkisu tana diney suna break fast da dearest dinta sai ringing din wayarta taji, tashi tayi ta nufi saman kujera inda wayar ke faman kara o wake kirana da sasssafen nan, dubawanda zatayi taga Ummarta ce da sauri ta dauka salam alaikum umma ina kwana, lafiya ba wata matsala umma, muna cikin koshin lafiya, Umma lafiya dai ko dariy atayi sanna tace to ummah, amen,amen, amen umma mungode, zaiji ahan sai anjima ina gaida abba sosai ummah, tau amen umma nagode, to sai anjima aha, ta katse wayar ta ajiyo ko lafiya umma keta faman jeromata tambayoyi haka, wanna addu’a tasha bamaban da irin addu’oin da umma keyi masu a kullum, sauri tayi ta kore wanna tunani ta koma dany, wayene? Sulaiman ya tambaya, umm ace tace tana gaida kai Allah sarki ina ansawa lafiya take dai ko lafiya kalau take bilkisu ta amsa, ya mutan gidan ina fatan kowa lafiya ko? Kowa lafiya kalau madallah, please in kunji waya ina gaidasu koda yake idan ma naje office inada niyar na kirasu, mikewa yayi ya shiga daki ya dauko mukullin mashin dinshi ya fito bari na wuce to karna makara har kofar gida bilkisu ta rakashi, koda yake tai iyyar ta bude gate din cewa kawai yayi ta rike mashi, bayan ya fitada mashin din kuma ya dawo ya rufe da kanshi wai shin baya son ta wahala ita dai dariya kawai takeyi tad an rakashi waje, ai kinfita yayi can I have a pot? Ya tambaya yana yar kasha murya dariya tayi tace no langabewa yayi kamar mai shirin kuka please don Allah, fashewa tayi da dariya yadda taga yayi said a tasa hannu daya ta rufemai idanu sannan ta yimasa kiss a kumatu, wani dogon ajiya zuciya yayi thanks a lot matata kin biya yanzu zanje office da karfi suka fasa dariya su duka ya fito da nufin hawa mashin dinshi ita kuwa tana bayanshi wani tsoho sukeyi kicibis dashi zaune a kusa da gidan su kanshi na duke ga dukan alamu yana neman taimako. Nauyin mutanen da yaji yasa ya daga kanshi su Bilkisu ya gani suna kallonshi cike da tausayi yauwan yaro don Allah ko da akwai abinda zaku taimakamin dashi wallahi ina neman taimako, hannu Sulaiman yasa a aljihu ya zaro dari biyar ya bashi ga wannan da hanzari ya karba nawa zan shire dauka nab aka baba, dauka! Nagode, nagode Allah ya saka da alkhairi Allaah ya biyaka amen kawai Sulaiman yace yah au mashin, har ya tada mashin din Bilkisu tace mashi bari na kawo mishi sauran break fast dinmu, yauwa jeki kawo masa ya tada mashin ya wuce, ita kuwa Bilkisu ta shiga gida ta zuba masa ragowar abincin da sukaci ta fito waje ta kawo masa, nagode, nadoge Allah ya biyaki, Allah yak are ku daga sherin duk wani mai sharri, gaskiya kunada hankali da nutsuwa kun dace sosai, kinyi dacen miji, shin kuwa yayi dacen mata, allah ya barku tare ya baku zuri’a dayyiba, murmushi tayi tace amen, har a ranta taji dadin kalaman shon nan ta shige gida ta rufe kofa. Wai Bilkisu yau har wanka nawa zakiyi ne Sulaiman ya tambayi Bilkisu wadda take ta faman goge jiki da tawel, dariya tayi, ko wanka nawa nayi dai-dai nike ai, domin yanada kyau ga kowace matar aure ta kansance mai yawan wanka tana tsafface jikinta, domin (bad ordour) is natural wanan ga duk wani wanda shekarunsa suka kai, ba ko
Bilkisu ce haka, ajiye jug wani zaburar das hi. Cikin kissa da kisisina irinta wayayyin mata, sannan ta anshi murufin kular ta ajiye ta ciro flet ta zuba masu abinci ta ciro fork daya ta ajiye a gabanshi, gab aki daya rasa ta cewa yayi, to muna zaice daukar fook din yayi a sannan ne ya tuna da yunwarda yakeji ya fara cin abincin yana kai loma ta farko a baki lakuwati! Wani irin dadi yaji ya kamashi. Har kunne, ya kara dibo ta biyu ya ci sai a sannane ya lura Bilkisu bata ci, lafiya baka cin abincin ne ya tambaya yana kallonta bata fuska tayi kamar zatayi kuka dazu ne da ina fere doya na yanke hannuna Magana takeyi cikin salo irin na shagwaba, ajiye spoon din yayi mu gani sannu --- injin bakiji ciwoba sosai, bari na dauko first aid box da kyar ta kanne dariyar da tayi kokarin fito mata yanda taga yanayi abin gwanin ban dariya dan taliki dukya rude, a’a ka basrshi kawai ya daina yimin zafi sosai, to bari na baki abinci ko da sauri ya fada yana dubanta, dama haka takeso nufinta kenan, daga kai tayi cikin shagwaba tace to, ci yakeyi yana har said a su duka suka koshi, sanna ta tashi ta zagayo ta zuba drinks din a kofi ta tattako dai-dai inda yake said a ta wani kwanta mishi sanna ta fara bashi a baki, rasa duniyar da yake yayi da mai zaiji dadin drinks din ko kuwa Balkisu da take kokarin zautarda shi, nan take ya shanye, ta tambayeshi cikin wani irin kasha murya a karo tana wani murmushi mayen kallo daga kai kawai yayi batareda ya samu Kalmar eh ta fito ba, ta kara tsiya yamishi ta bashi a baki nanma ya shaye a karamaka ta sake tambaya sake daga kai yayi kamar wani dan karamin yaro wanda bai iya Magana ba, duk iya kannewanda tayi wannan karon said a tayi dariya ta yanda ba zai gane dashi take ba duk da tasan ya koshi baya dai iya cewa ya koshi ne said a ta fara tsiyayowa kafinta kai masa a baki, sai ji tayi ayi wani irin gyashi da kyar ta iya hadiye dariya tace anya Dearest baka kishi ba, na’am eh nakoshi gaskiya kam, saura ke mana kasha, daga kai tayi tareda fadin uhum ta tashi ta nufi kujerar ta a fara shan drinks din, kallonta yakeyi kamar bai taba, ganinta ba ita kuwa tana sha tana kallonshi yanda taga yanayi kamar zai hadiye ta saura kiris tag ware, tagama sai tace masa miasa na koshi, dan gajeren murmushi yayi tau, bata jira yace wani abuba ta fara daukan kaya tana kai kitchen, dama ai kin barsu sai gobe naga dare yayi kome kike gani, dare fah kace yanzu ko karfe tara tayi ne duba agogonshi yayi au da gaskiyarki fa tara da minti takwas ni ca nike dare yayi sosai goben na kai sauran wayanda bankai ba, shima murmushin yayi ba tareda yace komai ba, zo muje yau za’ayi wani film dinda nakeso sosai farin wata ta wuce kawai batareda ta jirashiba, da sauri ya taso ya biyota wane fil ne? Marokon zamani kasan ko sau nawa zan kalleshi bana gajiya taje ta kuma kayan kallo koda suka kawo harma an fara ta nemi go ta zauna shima ya zo kusa ta ita ya zauna, ta lura dashi, kamar yana so yayi wata Magana kawai yi tayi kamar bata ganeba, sai can yayi dan guntun tsaki, kinga nama manta banyi wanka ba, ni da nace ina zuwa ko abinci baznci ba zanyi Wanaka, dauko idanuwan ta tayi akan kallon da takeyi hakane fa kaga nima sam na manta, mikewa yayi yanufi dakii harda dan tuntubeshi, ya fada tailet yayi wanka sanna yasa wata doguwar riga baka ya dawo falo ya zauna wai yanzu naji wani irin iska yana shigowa juyowa tayi ay hark agama wankan, ita dai tasan baifi minti hudu da yabar falon ba wannan wane irin wankane haka ta danyi murmushi, eh harna kare mana ko kinga nayi sauri ne? a’a tambaya kawai nayi, wurin wani dariya akayi musa mai sana’a ne kun sanshi wajen iya acting dariya ta saka harda shakewa kallonta kawai yakeyi shi kwata-kwata baiga abin dariya acikinba sai a lokacin ya kula a yanda aka canza wasu abubuwa da yanda ta mayadda sauran lamination dinsu a falo, akice yau an canza tsarin gida oh! Wai sai yanzu kai ka gani dama ta fada tana dan noke kai gaskiya yayi kyau, murmushi kawai tayi, Bilkisu yau kinsha aiki, kika gyara gida haka sanna kuma kika dafa abinci da idan mutum yaci baya iya Magana akan dadi gaskiya im the luky husband in the whole universal kuma wai kinga yanda kikayi kyau kamar irin ‘yar tsawar nan Barbier kinyi kyau fiye da yanda kike tsmmani fah. Wani tashi tayi yanda tayi yana kodata haka, tashi yayi ya nufi inda take kashin kanta ya taba sannan kuma haka sai kace na indiyawannan dariya ta saka don Allah malam dadin bakin ya isa haka, Allah ba dadin baki nakeyi ba ni dai yau nama rasa me zanlawa tantaki dashi wurin haduwa murmushin dadi tayi tace “hauni” Balkisu kinsha aiki da yawa ya kamata ace kinje kin kwanta dariya ta yi tace waya gayama ba yaje ya kasha kayan kallo yace muje ka? Mikewa tayi tsaye amma sai duk ta wani langwabawa kamar zata fadi yadai yafada, kafafuwana ne sukeyimi nauyi cikin shagwaba, ai cak ya dauketa ya shiga daki. Balkisu ke faman gudu wani katon mutum yana binta kuwwa take ta faman bugawa amma ba kowa a wajen a jikin wani bango ta fada, shi kuwa katonan ya tsaya a gabanta ya rutseta kuwwa kawai take famanyi, hannu daya yasa ya shaketa a hannu dayan shi kuwawata irin wukace doguwa daga wukar yayi sama dana kokarin soka mata wukar yayi sama girgiza kai takeyi tana fadin a’a duk idanuwanta sun firfito alamun firgita, amma koa jikin katon nan, da karfi ya nasa mata wukar ta kwala uwar kara mai tsnanin karfi. Maigado!!! Da karfi ummah ta farka tana kururuwar kiran sunan diyarta firgigi shima malam iro ya fara a sakamakon hargowar da yaji matarshi tayi. Lafiya? Meke damuwanki? Me akayi? A firgice tace mai gado? Maigado! Wani ne da wuka -------- ta kasa idarda zancen duk ta firgita da ummunan mafarkinda tayi dakata ba sai kin fadi abinda kikayi mafarki ba sherin shedan ne kawai shi yakeso yayi wasa da tunaninki, tukunna ma dai kinyi addu’a ne kafin ki kwanta sai da tayi shiru na dan lokaci har a lokacin a firgice take sannan ta tuna da batayi addu’a ba a sakamakon dan kishin gidawa kawai tayi bacci ya shareta a’a banyi ba ta amsa masa kingani ko shedan ne kawai shi yasa addu’a takeda muhimmanci a rayuwar musulmi tayama za’ayi mususlmi ya kwanta baiyi addu’a ba wadda idan kayita ba aljani ba har mutum bai isa ya cutar maka ba, wallahi dan kishingidawa nayi bansan sa’adda ma bacci ya kwasheni ba malam, amma ina ganin kamar Bilkisu tana cikin wani mummunan haline ko kuma wani mummunan abu yana shirin faruwa da ita ni naji ----- don Allah kibar wayannan shirmen baxaki nemi wuri ki kwanta kawai daga kinyi mafarki, to ance miki mafarki gaskiyane, shifa mafarki kasha biyu ne, na alhairi daga Allah ne na sharri kuwa daga shedan Bilkisu na can lafiya kalau da mijinta ba ke kika gayamin da rana cewa ta kiraki kunri wata hart ace tana gaidani, ba? Daga kai kawai tayi alamar ah kiyi addu’a kawai ki kwanta Bilkisu na lafiya kalau ba kuma ba abinda zai same ta sai alkhari da iznin Allah. To malam, harta fara addu’a sai kuma ta juyo ta dubashi tace malam kanada kudi a waya na kirata naji hankalina zaifi kwanciya? Kira! Zanzu kinsan ko karfe nawa ki kira ta yanzu cikin wanna tsohon daren abin ma ai gwanin ba dariya, yarinya da mijin ta haka kawai ki kirasu yanzu ki tada masu da hankali ko, ba halin ta kara cewa wani abu domin ta lura maigidan nata ya fara hasala dole tayi addu’a ta kwanta ba domin tana jin wani bacci ba sai domin hakan ya zama dole gareta ne, sam bacci kasa daukar ta yayi ita kawai tasan abinda ta gani Allah dai ya nuna mata goobe da safe lafiya dole ta kira taji ya ake ciki. A bangaren malam iro kuwa tabbas yasan maid akin sa taji tsoro sosai dangane da mafarkinda tayi amma ba yadda zai yi dole wannan hanyar dayabi ita kadai zai yi domin ya tasa abin a zuciyanta karshe yazo ya dameta, Hmm koma da menene Allah ya fefaddashi ya juyoshi zuwa alkhairi amen haka dai yayi ta sake-sake ba tareda ya dade ba bacci yayi awon gaba dashi. Tunda sassafe ummata aika aka siyo mata kati ta bayar aka saka mata a waya number Bilkisu ta danna ta kira. Ita kuwa Bilkisu tana diney suna break fast da dearest dinta sai ringing din wayarta taji, tashi tayi ta nufi saman kujera inda wayar ke faman kara o wake kirana da sasssafen nan, dubawanda zatayi taga Ummarta ce da sauri ta dauka salam alaikum umma ina kwana, lafiya ba wata matsala umma, muna cikin koshin lafiya, Umma lafiya dai ko dariy atayi sanna tace to ummah, amen,amen, amen umma mungode, zaiji ahan sai anjima ina gaida abba sosai ummah, tau amen umma nagode, to sai anjima aha, ta katse wayar ta ajiyo ko lafiya umma keta faman jeromata tambayoyi haka, wanna addu’a tasha bamaban da irin addu’oin da umma keyi masu a kullum, sauri tayi ta kore wanna tunani ta koma dany, wayene? Sulaiman ya tambaya, umm ace tace tana gaida kai Allah sarki ina ansawa lafiya take dai ko lafiya kalau take bilkisu ta amsa, ya mutan gidan ina fatan kowa lafiya ko? Kowa lafiya kalau madallah, please in kunji waya ina gaidasu koda yake idan ma naje office inada niyar na kirasu, mikewa yayi ya shiga daki ya dauko mukullin mashin dinshi ya fito bari na wuce to karna makara har kofar gida bilkisu ta rakashi, koda yake tai iyyar ta bude gate din cewa kawai yayi ta rike mashi, bayan ya fitada mashin din kuma ya dawo ya rufe da kanshi wai shin baya son ta wahala ita dai dariya kawai takeyi tad an rakashi waje, ai kinfita yayi can I have a pot? Ya tambaya yana yar kasha murya dariya tayi tace no langabewa yayi kamar mai shirin kuka please don Allah, fashewa tayi da dariya yadda taga yayi said a tasa hannu daya ta rufemai idanu sannan ta yimasa kiss a kumatu, wani dogon ajiya zuciya yayi thanks a lot matata kin biya yanzu zanje office da karfi suka fasa dariya su duka ya fito da nufin hawa mashin dinshi ita kuwa tana bayanshi wani tsoho sukeyi kicibis dashi zaune a kusa da gidan su kanshi na duke ga dukan alamu yana neman taimako. Nauyin mutanen da yaji yasa ya daga kanshi su Bilkisu ya gani suna kallonshi cike da tausayi yauwan yaro don Allah ko da akwai abinda zaku taimakamin dashi wallahi ina neman taimako, hannu Sulaiman yasa a aljihu ya zaro dari biyar ya bashi ga wannan da hanzari ya karba nawa zan shire dauka nab aka baba, dauka! Nagode, nagode Allah ya saka da alkhairi Allaah ya biyaka amen kawai Sulaiman yace yah au mashin, har ya tada mashin din Bilkisu tace mashi bari na kawo mishi sauran break fast dinmu, yauwa jeki kawo masa ya tada mashin ya wuce, ita kuwa Bilkisu ta shiga gida ta zuba masa ragowar abincin da sukaci ta fito waje ta kawo masa, nagode, nadoge Allah ya biyaki, Allah yak are ku daga sherin duk wani mai sharri, gaskiya kunada hankali da nutsuwa kun dace sosai, kinyi dacen miji, shin kuwa yayi dacen mata, allah ya barku tare ya baku zuri’a dayyiba, murmushi tayi tace amen, har a ranta taji dadin kalaman shon nan ta shige gida ta rufe kofa. Wai Bilkisu yau har wanka nawa zakiyi ne Sulaiman ya tambayi Bilkisu wadda take ta faman goge jiki da tawel, dariya tayi, ko wanka nawa nayi dai-dai nike ai, domin yanada kyau ga kowace matar aure ta kansance mai yawan wanka tana tsafface jikinta, domin (bad ordour) is natural wanan ga duk wani wanda shekarunsa suka kai, ba ko
style="mso-spacerun: yes;"> a son duk wata macen aure mijinta ya shaki wannan smell din, (adressing mirrow) ta zauna bayan kamala jawabinta, hakane your bighness sulaiman yace tareda mikewa akan gado ya bude, bandaki ya shiga, guntun murmushi tayi ta zaro (comp) ta fara shace kanta, zara comp din ta sakeyi a gashinta me zata gani!! Ga baki dayan inda ta shace duka gashinta ya cire saura ya fadi kasa sura kuwa yana a jikin comp din, kamar dai wadda ta saka (cliffer) ta aske wurin haka wurin yayi, wurgi tayi da (comp) din ta mike tsaye ta fara ja da baya tana kallon taswirar ta a cikin dressing mirrow din, ga baki daya gashin saman kanta zubewa yakeyi yana yankewa daga lokacin duka gashin ya zube cikin kankanin lokaci, ba suma ko daya kamar wadda tayi aski da rega. Wata irin karat a buga mai tsanani karfi, a guje Sulaiman ya fito daga cikin bandaki, ga baki daya ta fita hayyacinta, gam yariketa Bilkisu lafiya! Bilkisu! Sumana! Sumana! Kawai take kira, me ya faru da sumanki nuna masa mudubin tayi dad an yatsa, me sumanki tayi kai hannu yayi ya taba sumanta, dai-dai lokacinda ta kai dubanta ya zuwa madubi, me zata gani kuma!! Sumanta dai yananan kalau ba abinda ya sameshi, cak ta tsaya kamar abinda aka zarewa lakka, baya-baya ta ringa ti shi kuwa Sulaiman yana riketa tama rasa ta inda zata fara, wasu zafafan hawaye suka rika zubowa takan kumatunta, kuka takeyi baji bagani gabaki daya al’amarin gidanan ya isheta wannan wace irin rayuwace mai dauke da firgici da tashin hankali, a hakikanin gaskiya dab a domin tana yiwa Sullaiman HUBBIL YAKIN bad a ba abinda zai hana ta gudu ta koma garinsu ko zata tsira daga wannan ukuba, Sulaiman ya shiga aikin sa rarrashin ta ya ringa yi tareda yimata nasifa akan komai yayi tsanani saukin na nan zuwa, a haka suka kwana kowa da abinda yake sakawa a nashi ran ka shegari Bilkisu tayi kokarin ta sharar da abinda ya faru da dare bayan sunyi break fast tar aka mijinta kamar kullum, fitarsu keda wuya suka yi kicibis da tsohonnan da suka saba taimakawa a kwanakin baya. Gaidashi sukayi da yar fara’ar su, da hanzari ya amsa shima yana mai nuna fara’arshi a fili kamar wanda ya dade da sanin su, wannan karon ma Sulaiman dari biyar ya bashi yah au mashin dinshi yayi gaba, ita kuwa Bilkisu taje ta zuba mashi ragowar abinci, yayi sallama yawuce sannu a hankali suka fara sabawa das hi, har y azan idan ya dade bai zo ba, daga bisani ya zo sukan tambayi dalili. Sun shaku matuka da juna har sunayimasa kallo a matsayin dan uwan shima kuwa yana yi masu kallon diya. Bilkisu ce zaune a falo taci wanka harta gaji tana kallo, sallama taji ana rangada wa, da hanzari taje ta bude kofa su Fatima ne suka kawo mata ziyara taje ta bude kofa sannunku da zuwa ku iso. Makotan ta ne su Khadija da Fatima suka kawo mata ziyara. Sannun ku fad a zuwa ku zauna, taje ta kawwo musu abinsha ta ajiye musu, ta nemi gu itama ta zauna, bayan sun dan karba abinda ta kawo musu Fatiman ta fara da cewa Amarya bakya laifi ko kin kasha yar masu gida murmushi kawai tayi rufamin asiri ta fada wanna kwalliya haka ai sai ki hana angon ki fita waje, wannan karon dariya tayi ni dai don Allah kurufamin asiri. I fira suka ringayi da juna abin gwanin ban dariya, gaskiya su Fatima akwaisu da raha abinda ya dauke hankalinsu daga firar da sukeyi wani film dinda akayi na india mai suna Ghajini film din yayi kyau sosai. Sun dan dade suna fira kafin Khadija ta daga kai ta kai dubanta ya zuwa wani karon inlargement na Bilkisu da mijinta Sulaiman a lokacin aurensu, Wow!! Masha allah! Ta fada batareda tasan a baiyane ta fada ba tsananin kam da sukayi yadda suka yi kama da juna baka sai kace ‘yan biyu, agaskiya sunada kama sosai da mijinta kuma ba kananan indiyawa bane wajen kyau, su duka sun yaba da kyan ilargement din tare da fatan ganin yadda ya yansu zasu kasance ta fannin kyau. Ita dai Bilkisu bata samu ta cewa ba kyalesu tayi sukayi ta zuba abinsu sai da suka tashi zasu wuce Bilkisu ta rakasu kamar wadda ta tunada wani abu da hanzari ta tambayesu, ina ake kitso nan unguwar don Allah? Me kike nufi? badai tunda kikazo maigidan keyi miki kitso ba Fatima ta fada suka bushed a dariya ga baki dayansu. A’a wata yar office dinsu yake kaini gidanta takemin to bata iya irin wanda nake so ba wibin kawai ta iya kullum abin daya mukeyi abin duk ya fara isata. Anan bayan mu kuwa akwai wata inna Kande ko wane irin kitso kike so ta iya, amma da wuya ki gane gidan daga kwatance idan dai kika tashi kibiyo ta gidanmu ma hadaki da Habiba yar aikin mu sai ta kai ki. To ni ko gobe ma ba sai tazo ta kaini koda yake ba sai kinzo ba ma aikota goben ta kaiki. Kin san halinmu da surutu kar kizo mu tsaidaki. Dariya tayi tace ina jira har garka tar aka su sukayi bankwana suka wuce ita kuwa ta dawo daga cikin tana dariya. A haqiqanin gaskiya taji dadin zuwan su matuqa domin tayi fira sosai dasu gaskiya gwanayene wajen bayar da dariya sai faman dariya suke sta, kuma sun tattauna abubuwa masu muhimmanci wanda ya shafi aure, kasha gari da safe sbayan Sulaiman ya wuce office ta shirya tana zaman jiran habiba isowar habiba yar aiki su Khadija bata wani dade sosai ba tazo suka wuce sai gidan mai kitso: Habiba tayi Sallama dasu ta wuce tayi sa’a kuwa bata cimma kowa ba ita kadai ce suka gaisa da inna Kande tsohuwa dattijuwa da ita mai kirki, zauna yan nan ki jira na dan dama kokon nan kinji ta shimfida mata tabarma Bilkisu ta zauna ita kuwa taje tadama koko ta sauke ta zuba a wani bokiti mai murufi ta kai daki ta ajiye ta fito. Sannu da zuwa fah, ince dai kona tsaidaki ko kiyi haquri fa, haba inna ba komai ai Bilkisu ta fada tana maid an murmushi. Kujera ta dauko ta zauna wane iri za’ayi? Kitson ulu nakeso tau sai ki juyo a fara aiko. Kitso take suna dan fira, basu dade da fara kitso ba sukaji Sallama, wa alaikissalam ah hajiya Larai sannu da zuwa, wata babbar mace c eta shigo suka gaisa sa juna. Kai bari kallah kitson nan yayi kyau sosai, murmushi kawai Bilkisu tayi ya sunan ki sunana Bilkisu, yarinya mai hankali da nutsuwa nan dai aka fara fira da matar, ita dai sba mai fara’a bace sosai irin mutanen nan ne da basa son Magana ba ruwanta, ita dai har a ranta Bilkisu ta shiga a zuciyanta. Bayan an kamala yi ma Bilkisu kitso ta bude Jakarta ta dauko wata leda wanda ta rikowa mai kitso,sabulai ne na wanka dana wanki ssai man shafi da turare ta ajiwa mai kitso tayi godiya. Kai! Alhamdulillah nagode sosai buki inna Kande ce da murnanrta sosai wane layi kike ne domin ban saba ganinki ba. Anan bayan naku nike gaidan mu yana kallon bayan ginar church dincan mune karshen layin da karfi. Inna Kande tace gidan gate kalar madara da baki a firgice, ita kuwa hajiya Larai da take zaune mikewa tayi zumbur da karfi firgice lafiya inna meya faru kika firgice haka na fadi wani abune ku gayamin a’a ba komai Bik ai---ai--- inna Kande bata samu dammar iyadda maganarda takeyi ba, ji kawai Bilkisu tayi an cakume tad a karfi an shaketa, ina dana? Hajiya laraice ta shaketa take mata wannan tambayar a gigice. Bilkisu ke kokarin kwatar kanta nace ina dada? Ki fito min da dana abinda taci gaba da fadi kenan da kyar inna kande ta kwace Bilkisu a hannunta t samu ta riketa shieka Bilkisu yi sauri inji inna Kande, daukawa tayi ta dauki jakar tat a wuce da karfi said a takai bakin kofar fita tadan juya har yanzu hargon wa Hajiya Larai keyi tana fisge-fisge ku fitomin da yarona Bilkisu ki shega nace tsawa inna Kande ta bugamata, ai kuwa da gudu ta fita. Ga baki daya kan Bilkisu ya kulle tafiya kawai take amma hankalinta baya ga inda take tafiya. Shin ko dai hajiya Larai mahaukaciya ce? Amma kuma bata da alamun hauka, ko kuwa irin mahaukatan nan ne da haukar keyi tana taso musu? Can taji kamar a kunnenta maganar inna Kande “gidan gate kalar madara da baki?” hakika hajiya Larai ba mahaukaciya ce ba domin inna Kande ma a tsorace ta fadi wannan maganar, to wane yaronta kuma? Me yasa su suka suka firgita dajin gidan da take? A dai-dai lokacin da ta’iso kofar gidanta kenan, kicibis tayi da Sulaiman Bilkisu kin dawo har an gama kitson? Firgigi tayi kamar wadda ta tashi daga barci kallon shi kawai take batare da tace masa uffan ba lafiya tambaya yana meya faru Sulaiman ya tambayeta yana mai cike da fargaba hida da tsoron kallon shi kawai take gaba dayi kamar wata bebiya ta kasa furta kome. Hannunta ya janwo ya shiga da ita cikin gida bayan ta zauna ya sake tambayar ta Bilkisu lafiya meke damunki ne bata fasa kallon da take masa baga baki daya ta kasa Magana kamar wace aka rikewa harshe duk jikinta ya mutu tarasa meya sameta da kyar taji bakinta ya fadi bacci nakeji tare da wata hamma mai tsayi, to zo muje ki kwanta girgiza kanta kawai tayi alamar a’a sai kuma ta miqe kafa a nan saman kujerar da take bisa ta kwanta idanuwanta taji suna budewa suna kullewa sannu a hankali, nan take bacci ya kamata. Ita ce bata farka ba saida akayi isha’I, a hanakali ta bude idanuwanta tayi arba da Sulaiman take Bilkisu kin farka? Daga kai tayi ta bishi dany tace abinci lafiya naga kai bakaci ne murmushi yayi ai naci nawa wanna naki ne, maida masa tayi da murmushi to ai ni yayimin yawa dariya yayi nima dai nasan da haka kici kawai wanda zaki koshi harki damu da sauran to a ina ka siyo shi yayi dadi fat a fada tana dan kallonshi wani restaurant ne ko dalili sunan shi nan dai tace abinci ta koshi tasha ruwa masu sanyi hankalinta ya dawo jikinta. Nace ba Bilkisu dazu mun fara Magana sai kikayi bacci meya faru dake ne dazu? Ince dai lafiya ko? Ai kuwa nan take komai ya dawo mata kamar yadda ya faru dazu a gidan inna Kande mai kitso a tsorace ta fara bashi labara kasan meya faru dazu bayan naje wurin kitso har an faramin sai ga wata mata tazo ----- baran wani almajiri ya katseta almajiri yau a gidnmu Bilkisu ta fada tana mamaki, a kinga kuwa bamuyi asarar abincin mu ba saiki dauki saura ki zuba masa ki dawo kici gaba da gayamin abinda ya faru dazu to ta fada tare da daukan sauran abinci ta nufi almajiri zo ansa da hanzari ya shigo ya gaidata dan qarami dashi taro kwanon ka a taro kwanon shit a juye masa, nag ode Billy! Da karfi tadago me kace tasan duk/a fadin duniyarnan ba wanda ke kiranta Billy idan ba “Man” dinta nada ba kuma yama akayi yasan da sunanta me kace da karfi ta sake tambayarsa dagowa yayi yace cewa nayi nagode Hajiya ajiyar zuciya tayi cikin ranta tana mai godewa allah daba yadda taji ya fada ba, a cikin ran nata ne ta juya zata wuce domin taje ta idarma Sulaiman da labarinda ta fara bashi mai dauke da al’ajabi da kuma firgici ji kawai taji almajirin yace “ba wani tsoron da kikaji dazu Billyn da kikaji da farko na fada shi dai na fada tsayawa cak tayi ta daina tafiya a hankali ta fara juyawa maganarda tayi a rai wadda ko fatar bakintabatasan anyi baya akayi shi ya jiya Billy fah yace idonta a zare hankalinta a tashe a firgice ta nunashi da yatsa me kace sake maimautawa. Rike yake da kofar gate din gidan qafarsa daya ciki daya yana fuskantar ta ya bude baki yafara Magana “kowane mutum yanada lokacin shina tsoro inayi miki bushara da yanzu lokacin tsoron ne da firgici da tashin hankali a gareki da kuma mijinki Sulaiman daga yanzu kwanciyar hankali ta kaurace Mukuhar ----- bata jira ya I darda maganar da yakeyi bat a fara ja da baya baya ta wurga da kularda ke hannunta ta runtuma da gudu ya zuwa cikin gida. Da gudu ta fada falo Sulaiman ya mike ya dai wai Bilkisu meke daminki ne iye? Abinda almajiri ya fada mata duk ta kwashe fada mishi, tana Magana cikin firgita da ruduwa kuma a tsaye take bashi labaran ha ta kamala sai dai kuma daya a cikin labarinta ta boye almajiri ya kiramata wato Billyn da taji almajiri ya kirata dashi, dalilinta kuwa anan shine tana jin tsoron ta yadda Sulaiman zai kalli al’amarin ne kallonta yake yi idon sa a zare kai da gani kasan yana cikin tashin hankali, lokaci daya idanuwanshi suka ciko da kwallah da kyar ya samu ya iya zaunawa akan kujera, a da-dai lokacin kuwa Bilkisu durkushewa tayi kasa tana tsala uban kuka, ganin halinda ta shiga yasa Sulaiman ya tuna shifa namijine don haka yayi yake ya ta yadda ita ya zaunar da ita akan kujera kada ki damu Bilkisu koma me ne yake shirin faruwa, damu Allah nanan shine gatanmu, bata jira ya idar da abinda yake fadi bata tari nunfashin sa wallahi bana iya zama anan gidan, ko kwana daya bana karayi a cikinsa, tun ranar da nazo nake cikin fargaba da tashin hankali mara misaltuwa, ni bana iya zauna cikinsa ta kawo dai-dai nan ne ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi don Allah na rokeka ka maidani gidamu ka kaini garinmu bana son wanna garin duk tausayi ya kama Sulaiman hakika da gaskiya Bilkisu akwai wani mummunan abu dake biyarsu, tabbas akwai wani boyayyen al’amari a tattare da gidan nan da suke ciki. Bilkisu ki saurareni ki natsu da kyau koma menene nayi alkawarin zamu bar gidannan gobe zanje na nemi transafer dole ne mubar garin nan, yanzu ne taji sauki a ranta sossai, zo muje mu kwanta in Allah ya yarda komi yazo karshe Bilkisu. Ta shi tayi ta biyo shi tare sukaje suka kulle kofar gidan sannan suka wuce daki yayi addu’a akoina ya tofa itama Bilkisu haka suka kulle daki suka kwanta duk da kasancewar ba wanda bacci ya dauka cikin su. Kamar wadda aka gwanta ta tashi da sauri ta girgiza Sulaiman tashi-tashi sai dai abinda bata sani ba bacci yakeyi bad a sauri ya tashi lafiya wani abinne kuma? Menen? Gobe idan zakaje office neman transfer tare zamuje ko domin bazan iya koda second daya a gidannan ni kadai ba wallahi. Ajiyar zuciya yayi game da murmushi da yaji akan wannan bin ne kafin nawuce zanyi waya da abokin aikina Nuhu kinsan yanada ‘yaya mata masu dan girma kuma kinsan gobe ba skull kinga sai suzo su tayaki zamam har na dawo kinji to ta fada tare da da’a kai alamun ta gamsu da haka. Kasha gari asuba daya daya tashi baije masallaci ba domin samin halinda suke ciki, shi dai gurinshi su bar garinnan lafiya, bayaso wani abu ya cutarda su musamman ma Bilkisu. A hakikanin gaskiya sanan kanshi ne akwai abinda yake faruwa a gidannan, shima kanshi ba saudaya ba basau biyu ba yasha jin abubuwa a gidan sanna kuma yasha garin sai dais u kama yi masa kamar dabo, baifi sati biyi bad a ya fito daga wanka yazo a dressing mirrow kawai wani kato ya gani a bayanshi hankali a game da katon shine a gefen fuskarshi tun daga samamn girrshi harya zuwa kumatunsa wani irin mummunan rauni ne yank ace babba wadda har kama hango kashin fuskarsa, jinni ne yake zuba kamar fanfo daga mummunan raunin har ya rife masa gaba ki dayan fuska, da karfi ya juya amma ba’a mamakinsa ba wannan katon ba dalilinsa suke maida duban sa yayi ya zuwa madubi sai kuma ya sake ganin wanna katon da karfi ya juya zai fita yabar dakin sai ga Bilkkisu ta shigo kannewa kawai yayi domin kada ya fada Bilkisu ta firgita kai abubuwa ba iyaka da suke faruwa dashi a gidannan, lallai akwai boyayyen alamari, a dangane da gidannan numfashi ya sauke sa;annan ya tayar da Bilkisu domin ta tashi tayi alwala suyi sallah. Bayan sun idarda sallah ga musu break fast suka ci, ya tashi taje yayi wanka, Bilkisu bata yarda ba’a bakin bandaki tashi dai abin dariya ma ya koma yana bashhi, har ma dai lokacin da tace itama sai ya jirata a bakin bandakin tayi nata wankan domin ita sambata yarda ta fada bandaki ita kadai ba dolen shi ya zauna yayi gadinta hart a kare wanka yanata faan yimata dariya, ita kuwa ko a jikinta, ita dai kada yayi nisa da ita. Bayan ya kamala shiryawa yace mata shifa zaije ya nemo transfer dinda ya gayamata daga nan kuwa zai wuce gidan wanda ya basu haya domin ya sanarda shi sufa zasu bar masa gidanshi. Nnfa kawai, wata sabuwa inji iyan caca!! Alan baran taki yarda sam ita ba ba inda zaije ya barta. Ke tunfa a jiyannan nayiwa Nuhu text akan cewa ya kawo diyan shi a yau a gidanana suyi mana wuni, kinga shima yayimin reply kinga danna wayarshi shima ya nuna mata reply din Nuhu ta gani da kanna in allah ya yarda duk da haka said a kyar sannan ta yarda zata zauna da sharadin zata zaunaa kofar gate har Nuhu ya kawo yaranshi tukunna kafin nan su dunguma su koma cikin gida. Ya ya iya haka ya amince ta biyoshi suka fito tare, sunyi sa’a kuwa domin a bakin kofar gidan su. Ajiyar zuciya su duka sukayi. Sulaiman ya fara Magana Alhamdulillah baba kazoo akan dai dai lokacinda ake bukatar zuwanka cikin rashin gamsuwa da abida suka fada ya tambaya a dai-dai lokacinda ake bukatar zuwana? Me kuke nufi su duka suka fashe da dariya Baba wani tsoro takeji n tafi na barta ita kadai a cikin gida, tunda yanzu gaka ba sai ka tayata zamaba. Murmushi yayi mai hadeda ajiyar zuciya eh zan iya tayata zama daga nan wajen har kaje kadawo daga inda zakaje, ga baki daya suka sake dariya, ai ko aciki baba zaka iya shiga mu a wurinmu ai kai tamkar dan uwammu ne na jinni sulaiman ya fada a-dai-dai lokacinda yake shirin tada mashin dinshi, a’a nikam dana ai lokaci shigowana baiyi ba tukum, idan lokaci shigana cikin gidanku yayi bama sai kun kirani bada kaina zan shiga. Allah ko Baba Sulaiman ya fada a dai-dai lokacinda mashin dinshi ya tashi ya bashi amsa kai tsaya to Allah ya kaimu lokacin ya tuka mashin dinshi yayi gaba murmushi, suka sake su duka tareeda fadin amen, a nan Bilkisu a zauna suka dan fara hira da juna, Baba ne ya tambayeta ‘yata me yake baki tsoro cikin gidanku da har kike shakkar zama a ciki? Sai da ta danyi jim sanna ta iya bude baki ta fara gayamasa abinda ya dace ya sani bayan takai aya, yayi dogon numfashi daga ganina gujewa bla’I bashine tsira daga bala’I ba, fuskantar bala’In shine masalaha, irin wayannan abubuwa suna faruwa daku kuntaba samun dama kuka tambayi kanku shin meye dalilin faruwar duk wayanan abubuwa? Tabbas akwai dalili, dalili mai girma, da ganan kuwa har zuwa Birnin sin in kunje ba zaku tserewa faruwarsa ba. Diyata ina mai baki shawara duk da ba, za ki fuskanci koma meye yanzu gadan abinda zan iya taimaka miki dashi yasa shannunshi a cikin babbar rigarda ke sanye a jikinshi take cikin yanayi na rashin gamsuwa kana ta mika hannu ta karba. Bilkisu koda ni mai cutarwane bazan taba cutar daku ba ki duuki wanna maganin duk wata hanya da kikasan wurine da ake iya shiga cikin gidanki, ma’ana bakin kowace kofa harta bandaki ki zuba maganin, yadda kuwa zaki zuba kereriyar kofar zakibi, kina zuba maganin tun daga farko ta har karshe, karki damu kome muguntar abu bai isa ya ketare takan layin nan ba, kuma koda kin share maganin, aikin shi yanan bazai goge ba, abu daya kawai ke ruguza maganin shine idan ruwa ya zuba a inda aka zuba maganin, ruwa anan ana nufin duk wani abu da bane ina fatan kin fahinta, daga kai tayi eh Baba na fahinta nagode sosai Allah ya saka da alkhairi amen, tashi ki shiga cikin gidanki ba abinda zai sameki kinji yanzu ya zama mini dole na tashi na bar wurinnan ba domin naso ba. Ji tayi matukar karfafa mata guiwa ta tashi ta shiga cikin gida kai tsaye, da isarta kan kujera ta zauna kalaman Baban nan suka ringa fadomata a rai kwata tawata ta rasa ta inda zatasa kalaman nashi, shin gargadinta yakeyi ko kuwa shawara yake bata, koma meye yau zata saka maganinda ya bata kuma zata ga karshen koma meye kafin gobe su kaura ya zuwa garinsu, murmushi ta saka wani irin dadi taji ya ratsa zuciyarta. Aunty taji ankira da karfi, juyowa tayi su Ummi ta gani tana murmushi har a ranta taji dadin zuwansu, sai a yanzu kuka zo, waya kawo ku Babamu ko? Ina yake ne. amina ce tace ya wuce shine ko shigowa baiyiba, ku zo ku zauna, aunty sa mana nicklochen sukayi zamansu, suna masu nishadi, sai fara’a take yaran akwai su da shiga rai, sai dai abin mamaki zuwansu da salo Ummi kuwa shiru-shiru ba ruwanta, har iyayen suna fada ko Magana batason yi idan dai bata zama mata doleba amma a wannan karon itace mai baki karma bakin nata da salo ya zarce na Amina a wannan karon ita kuwa Amina itace ba ruwanta a wanna karon.
Shi kuwa Sulaiman tunda ya wuce bai tsaya ko inaba sai a bakin gate din office dinsu, kaf ya tsaya tsam kamar wanda yaga wani dodo, sani ya manta oganshi yayi tafiya, ya tafi wajen wani comfrence da za’ayi a sokoto kuma zasuyi kamar kwana shida zuwa biyar basu dawo ba, to meyasa ma wai bai tuna ba sai a yanzu, wani tsaki yayi mai hade da takaici, said a yayi kamar minti biyar a bakin gate din office din nasu sanna ya tada mashin dinshi ya nufi gidan Alhaji day a basu haya domin ayita takare idan yanada wani gida ya canza musu ko kuwa asan yanda za’ayi kafin nan da zuwan kwanaki shida da oganshi zai dawo ya nemi transfer ya bar gari tun a kan layin gidan Alhajin ya fara ganin dandazon mutane ba adadi har ya iso kofar gidansa, me zai gani ga dukan alamu wani abu akayi ras! Gabansa ya fadi a wurinda shimfida take ya dire takalma yayi sallama ya mike hannu tabbas gaisuwar rasuwa ake yayi gaisawa aka ansa masa ya nemi ya gana da babban dansa, kasan cewar yasan sulaiman domin tare dashi akayi process din gidansu Sulaiman. Bayan da Sulaiman ya kara yi masa gaisuwa ya tambayeshi yanda haka ta faru, ya shaida mai matukar rudarwa, a jiya da dare ne yana bacci sai kawai akaga ya mike tsaye ya sauka daga kan gado, ya farayin da baya-dabaya yana ta ko’ina har ya fadi kasa, likitoci sun auna sun fada cewa sakamakon ganin wani mummunan tashin hankali da idon dan adam da kuma kwakwakwar sa basa iya dauka da yayi shiya hifar masa da wani matsanancin bugun zuciya da har yayi sanadiyar rasa rayuwarsa a nan take dirshan ya fadi a kasa hawaye suka riqa zuba a idanuwansa, al’amarinda yayi matukar bawa mutanenda ke wurin mamaki kenan hade da tausayin musamman babban dan Alhaji, lallashin shi aka dingayi har ya dawo cikin hankalishi ya daina kukan da yake. Shi kadai yasan abinda yakewa kuka tabbas shakkah babu akwai wani mummunan abu dake shirin faruwa dasu, gashi sub a yan gari ba yaya zai yi. Ya zabura ya mike ya sake gaisuwa yayi sallama ya wuce, dole subar garinan gobe-gobe ba domin sko yanzu lokaci ya kure musu bad a sun bar garin a yau, kara gudu yayi kamar wanda zai tashi sama domin kar dai wani abu yazo ya sameta domin kuwa Bilkisu shi c eta fado mishi a rai, kar dai wani abu yazo ya sameta. Krar shit ta dawo masa da hankalin shi daga tunaninda yakeyi bai yi ni yar ya dauka ba kuma dai yaji bari ya dauka aljihu ya zara wayar shi sanan abakinshi Nuhu ya gani da sauri ya dayka ya karakan kunnensa, slamu alaikum ya fadawa alaikussalam, Sulaiman don Allah kayi hakuri kaga ban samu dammar kawo su uUmmi ba Wallahi jiya da sakiyar dare mamansu ta kuma da matsanancin ciwon ciki amai da gudawa tun sa’annan muna asibiti sai yanzu muka dawo, yanzu dai Alhamdulillahi ta samu sauki sosai, kayi hakuri fatun sannan ban masan ida wayana yake ba sai yanzu da muka dawo bare na kiraka na gagayama bazan samu dammar kawo su ummi ba kasan ya yanda al’amuran suke wallahi tun sannan bansamu nutsuwa ba sai fa yanzu da kaga na kiraka. Rasa ta cewa yayi can ya lalibo kalamai yace ai badamuwa Nuhu Allah dai ya bata lafiya ya tashi kafadarta sai munzo dubata nida Uwargidata tau amen, amee, Sulaiman, When sai kunzo, sai an jima ya katse wayar. Wani matsanancin gudu yakeyi kamar ranshi zai fiita ya nufaci gidanshi haiqan dearest!dearest! dearest! Yake fadi kamar wani mahaukaci, da karfi yasha kwanar gidansi, kicibis! Yayi da wani abin ban mamaki, Bilkisu ya hango tana fama dariya tana bye-bye da hannunta, kyar ya iso a gabanta, murmushi tayi ta nufaci inda yake sannu da zuwa ga baki daya ta jagula masa lissafi zauwa ke dawa kike bye-bye haka? Malam mu shiga daga ciki ai ko, biye kawai yake da ita, suka shiga cikin gida su waye suka zo wurinki ne haka, ni fah da farko duk kin tsoratani n zata ko ke kadaice a gidan duk hankalina ya tashi, wani kallo tayi mai alamar ina ma fushi da kai, eh ai dole kace haka ai, ta wani shagwabe murya sanna tace stunda kasan Nuhu ya kawo su Ummi! Shine ka tafi abinka ka shallake, to sune nakewa bye-bye da yazo daukan su, nayi-nayi ya jiraka amma yaki ta, su ummi!! Kuma Nuhun ne yazo daukan su!! Mikewa yayi inna lillahi wa inna illaihi raji’un, a firgice itama ta mike hakika sulaiman dinta ba karamar razana yayi ba to muje na razana a cikin abinda ta fada. Lafiya dearest meya faru meye don Allah gayamin, Bilkisu tashi ki had kayanki gobe-gobe zamubar garinnan, me ya faru ka gayamin! Ta daka masa tsawa tana mai zubarda kwallah batareda tasan ma tayi ba, da kyar ya kwantarda hankalinshi ya zaunarda ita kana ya bayyana mata duk abinda ya faru tun daga farko har rasuwar Alhaji da rashi lafiyar mata Nuhu duka ya bayyana mata shiru tayi ta kasa koda motsa dan yatsan ta akan tsananin firgitarda tayi Bilkisu! Bilkisu! Ga baki daya batajin abinda yake fada, said a ya wujijigata da karfi sanna ta dawo ayyacinta, Bilkisu karki damu gobe-gobe zamu bar garinan a’a ba sai na ta fada tana mai fashewa da matsanancin kuka, a’a Bilkisu ki bari gobe tunda sassafe, a’a ta durkusa kasa ta rike masa guwayyunsa na rokka don Allah Mubargarin nan a yau din nan, nunfashi ya aje, to shikenan jeki hado kayanki mu wuce, karki damu sa sauran kayan, idan nazo karbar transfer letter din azan wuce dasaura, shiga tayi ta tattara kayanta shima tattara nashi kayan yakeyi, sai a yanzu ta gane lallai wayannan basu Ummmi bane, bayan da ta zuba maganin sai taga duk sun wani kamar rikice, ta tuna sanda ta aika amina kitechen ta dauko mata plate sam takasa shiga a kitchen din, sa yanzu ta fahimci tun lokacinda ta zuba maganin basu sake takawa daga cikin falon ba. Tsam ta mike tunawa tayi da yanda Ummi ta dauko jug a cikin feeg wanda ta cika da drinks din kwakwa ta wankada akan kofar fita falon wanda zata fitar da mutum zuwa ta gane da gangan ta fadi ta zubar da drinks din don dai kawai su samu su fita. Kamala hada kayan tayi a dai-dai lokacinda shima y agama kamala nashi muje ko yace ta janyo hijabinta data ajiye kalar kayanda ta saka tace eh, muje tare suka nufi hanyar fita, tsayawa sulaiman yayi ya kalli gidan da kyau ya gayda kai ya wuce suka kulle gida sun juya zasu wuce sukaji an kyalkayale da wata mahaukaciyar dariya, duban juna kawai sukayi ba tareda sun ce ko kalaba sukaja akwatunansu sai a kan titi suka tsaya, wani mai a daidaita suka tsayar, garge zaka kaimu, yasa kayansu ya nufaci garge din, misalign karfe uku da rabi ne narana garin ana tsananin zafi, wurin fifa ya tsayar day an layin su, jira suke ya dauko musu hannu su wuce, ji tayi kamar ana girgiza kasa, ruguzum komi na wurin ya fara rusgawa cikin kasa, kuwwa da hrgowar jama’a kawai kakeji, motuna da baburra sairuguzawa sukeyi kamar an cilla a dai daita sahu su, sulaiman ya runtuma cikin, caf tasa hannuwanta ta cafkoshi, wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta shiga kuka take tana hargowa karka tafi ka barni tana rike da hannunshi sauran jikinshi kuwa yana lib, hannunshi ya fara subuce mata tana mai tsala uwar kuwa tsundum ya fada yana kiiran sunanta Bilkisu! Bilkisu! Sulaiman ya ingi zata, caraf ta dawo daga wanna mummunan mafarki zatace ko tunani, ita dai tasan a zahiri taga wannan abu ya faru, lafiya me kike tunani haka? Sulaiman ya katseta, waige-waige take da idanuwata cikin mawuyacin hali, ke meye? Meya faru? Jin ta kama hannuwanshi ta jinike da nata, a jiyar zuciya yayi, karki damu masoyiyata insha Allahu zamu isa gida lafiya, gobe irin wannan lokacin kina gaban Umma, ya fada yana zolayata, duk day a kokarin da tayi wajen gani tayi murmushi ta kishingida dai-dai wajen ‘yanBauchi aka ajiye su, sune passengers na farko da suka fara loda a motar, bayan an saka masu kaya a mota, suka shiga ciki mota suka zauna suna jiran zuwan sauran passengers, zaunawar su keda wuya dum! Sukaji ko ina yayi rufe da wani matsanancin duhu smai tsananin muryoyi sukaji kala-kala ta yadda ba zasu iya tantance ko murya mace, namiji? Ko kuwa karamin yaro ba. Gargadinsu a kayi da murya mai kaushi akan suyi gaggawar fita daga cikin motar na su koma ya zuwa gidansu da suka baro, muddin kuwa sukace zasuyi taurin kai, kuwa zasu hadu da matsanancin hadarin motar da zatayi sanadin halkar duk wani passenger da ke a cikin motar, sanna kuma aka wayanda basuji basu gani ba, domin kuwa driver matarshi ta haihu kwana biyu yayi saura ayi biki, idan sukayi sanadiyar mutuwar wazai dauki nauyin iyalishi kuwa wanda yake kan gaba a kusa da driver dan makarantane shi kadai ne namiji a gidan su, mahaifinsa ya rasu mahaifiyarsa ke wahala wajen ganin ta biya masa kudin makaranta. Ita kuwa wannan matar ‘yaranta duka biyu marayu ne ‘yan uwan mahaifinsu sun kwace musu dukiyarsu, wajen ‘yan uwanta zataje neman agaji. A haka akaci gaba da lissafo musu ko wane passenger da abinda yake kunshe dashi duk domin dai so fita daga cikin motar bayanta aka gama gargadinsu, wayau! Sukaga ko’ina ya yaye, kuma motar da suke ciki hart a cika da passengers, kamar yadda aka shaida musu haka kuwa suka gani, duk wayanda aka lissafa musu a motar su da ne ke ciki. Kallon juna sukayi ba yareda sun samu dammar furta wata kalam ba, wayar direba ce yita wau kara, dauka yayi tareda sallama, slamu alaikum lafiya kalau wallahi, a’a alhamdulillahi mun gode Allah, amen, amen, sosa kunnenshi yayi yana ‘yar dariya, eh saura kwana biyu ma ayi bikin ai ina Allah ya yarda. Dam gabansu yafadi suka sake duban juna da karfi, tare suka hada baki dakata!! Duk motar kowa ya jiyo ya ba, ana saka kayane a but da hanzari suka bade murfin motar suka fito, mun fasa tafiya Sulaiman yace gaywa condester, don Allah kuyi hakuri wallahi mun fasa tafiyar me kace malam, kamar ya ya kunfasa lafiya wanna aima maganar banzace, duka mutanen wurin suka taso wasu na bayadda hakuri wasu na zugawa, anan dai aka samu wani dattijo mai hankali da sanin ya kamata, yace tunda ai ga wasu passengers nan ba sai kawai su shiga a madadin wayannan ba, ai wannan abun bai kai na wani dogon bayani ba, sukayi masa godiya suka nemi a dai-daita sahu suka sake saka kayansu suka nufi gidansu da suka saka baro, suka bar mutanen garage din kowa tana mamakin wayannan mutane haka, su kadai suka san dalilin da yasa suka bar motar, ba kuzari mai adai-daita ya sauke su a kofar gidansu, said a suka yi kamar minti bakwai a tsaye suna kallonn-kallo sanna Sulaiman ya bude gida suka dunguma a ciki, ga baki daya duniya tayi masu zafi komai ya kulle musu, sun ma rasa ta inda zasu fara bamai cewa kowa ko kala, suka isa bakin kofar falo ya saka key a ciki yana kokarin mirdawa ya bude kofar falon, kiririn,kirin wayar Sulaiman tayi kara su duka suka zabura da karfi, hannu yakai aljihu ya ciro wayar, sunan mahaifinshi ya gani ya bayyana a gaban screen din wayar shi, dauka yayi, yayi kokarin boye duk wata damuwar shi, da ke tattare dahshi, slamu alaikum Abba ina wuni lafiya kalau, lafiya kalau take, komai Alhamdulillahi, Na’am Abba na nameye ya tambaya yana mai nuna mutukar mamakinshi a filli kamar a gaban Abban nasa yake, kallonta yayi da hanzari eh yayi murmushin yake yace amen, har yanzu kallonta yake yi, to amen baba ehan, ya katse wayar har yanzu kallonta yakeyi, ga baki daya hankalin shi a tashe yake itama kallon nashi take yi, meye ta tambaya tana kallonshi wai Abbane yake tayani murya, wai a dazun nan Ummata ta kira ki a waya, kika gaya mata mun dawo ne daga Asibiti likita ya tabbatar mana da cewwa kinda juna biyu na tsawon wata biyu, dirshan ta fadi zaune barkewa tayi da wani matsanancin kuka, shima, sulaiman zama yayi a dai-dai kusa da ita sai dai wannan karon ba lallashinta yakeyi ba, hada tagumi yayi ta fada kogon tunani, shi ba abinya fada ta gida ba, a can hankalin su ya tashi, kuma ma zai iya yuwa idan wani yace zaizo a kasheshi a kan hanya sunfi minti goma anan zaune, sa’annan Sulaiman ya mike ya iyadda bude kofar falon su duka suka shiga ciki, jawo akwati takeyi itama suka nufi daki ji tayi kamar an ja mata kafa jicce ta fadi kass ram! Yunkurawa tayi ta tashi amma ta kasa, wasu taurarin wahala ta ringa gani sunayi mata yawo, yarda tashi akwatin yayi ya nufo inda take da gudu, yanka kokarin tada ta, lumshe idanuwanta ta farayi, tun tana iya budsu har takai ga duka suka rufe rungumeta yayi ya kwala uwar ihu, da hanzari ya tallabeta da gudu ya fito baima tsaya ta wani rufe gida ba. Mijin Khadija yayi kicibis dashi ya dawo, da karfi ya tsayadda mota, Sulaiman da gudu ya shiga, Asibiti, asibiti! Da isarsu asibiti aka daurata saman keke da gudu aka wuce da ita emergency, gaf aka rufe kofar emergency aka dakatar dashi daga yunkurin shiga cikin dakin da yayi, jiginawa yayi a jikin bango emergency zaune yayi a nan wurin ya fara kuka ne ya ringa lallashi da kyar da sidin goshin daina hargowarda yake ya zama hawaye kawai ke zuba daga idanunsa, nurse c eta fito da fara’arta da kafri suka mike su duka sister ya lafiyar jikinta, zan iya shiga yanzu, don Allah ku bari na shiga nag anta, Sulaiman k eke jero wayannan zancen duk shankalinshi a tashe relax malam cogratutaltion ma, wani kallo yake mata me kikace? Cewa nayi congratulation matarka na dauke da JUNA BIYYU na tsawon wata biyo, kuma zaka iya shiga ka ganta, za ma kaiya tafiya da ita, because she is out of danger known. Bai jira ta kommala jawabinta ba yaruga da gudu zuwa cikin inda dearest dinshi take, zaune ya taradda ita tana kallon yan yatsunta tsaye ya tsaya cak, kamar tasan dashi ta daga kai suka hada ido, ya karaso inda take ya rungumeta yana zubarda kwalla, Alhamdulillahi kin tsoratani, don sAllah kada ki sake yimin irin haka. A nan aka sallame su daga asibiti maigidansu Khadija ya maidasu gida, sukayi masa godiya sun ma rasa zaune kawai sukayi kamar masu ansar gaisuwa, kiran mariba akayi, suka tashi sukayi alwala, ya jagoranceta sukayi sallah, mikewa yayi ya fada kichen a dafa mata indomies, a wani bangare na rayuwarshi harga Allah dadi yakeji mara misaltuwa, matarshi nada ciki, kenan zai zama baba, zubo indomie yayi a flate ya kawo masu a nan bedroom dinsu tareda rowan da zasu sha, aka kira isha’I suka mike suka sauke farali, suka jawo kwanon abinci sukaci sukasha ruwa, ta tashi da dauki kwanuka da ni yar ta kai kitchen karaf ya amshe, no wannan ba aikin ki bane yanzu, zauna ki huta, kada ki wahaltamin da baby, duk da irin halin da suke ciki said a tayi yar dariya, duk kunya ta lullubeta, ya dauki kwanuka yaje ya ajiye ya dawo, suka yi addu’a suka kwanta. Wayyo!! Wata kara aka buga mai mai matukar firgitarwa zunbur suka sauka daga kan gaso jan abu sukaji anayi a falo, kasan tys idan ana jan abu akanshi zai ringa bada wani sauti daban, kuka sukeji anayi matsananci,
a hankali suka tattaka ya zuwa bakin kofar daki yaddazasu iya hango abinda ke faruwa a falon, da baya sukaja da kafri saka makon ganin wanan tashin hankali da basu taba gani shi ba, wata mace ce ko ince budurwa wace bata wuce shekara goma sha takwas zuwa sha tara ba, ake ja, batareda suna ganin mai jan nata bag a baki daya jikinta jinine faca-faca, kama kuwa kadan ya rage ya rabuda gangar jikinta, rokonsu take tana kuka don Allah ku taimaka mini, karaja sukeyi da baya suka rungume juna suka kankame waje daya, wuf tayi ta nufo su da niyar ta cafke su, kamar an wulla ta ta fada can gefe daya, sake mikewa tayi kanta yana shillo ta kara nufo su amma kamar a karon farko ma sake wurgata akayi, kuwa take kala-kala iri-iri tana yunkurin kamasu amma ta kasa, su kuwa suka buga suka kara ja da baya suncakankame juna, duk wani yunkuri, na shiga cikin dakin tayi amma ta kasa Sulaiman ne yayi karfin hali ya ja kofar daki ya rufa da karfi ya dawo daga baya. Duk hargowarda takeyi a kunnuwansu yake, addu’a suka yi suka tottafa ko’ina suka haye kan gado ko runtsawa ba wanda yayi-sai yanzu Bilkisu ta gano dalilin da yasa ta kasa shigawa acikin dakin, maganinda baban nan ya btane, haka suka zauna ba wanda ya koda runtsa idanuwashi, sai a shiyoyin asuba su duka bacci ya sace sub a tareda sun sani ba Sulaiman ya fara falkawa, kasa rufe bakinsa yayi sakamakon kashin ganin matarshi da yayi akan gado, kofa ya gani bude, a hankali ya tashi ya fara tafiya yana duba kofar, can ya hango Bilkisushi a falo zauna murmushi, zo dearet, zo mu karanta Qur’ani kama meye yayi kadan ya cuta mana, shi nake karantawa kazoo mu sauke Qur’ani a yau dinna, ajiyar zuciya yayi ya sauke nunfashi da karfi okay bari na dauko nawa Qur’anin, a’a ai gashi na dauko duka zo kawai mu karanta, fitowa yayi ya nufa ci falon ya tsallaka ya fada cikin falon, sai dai kuwa abinda bai saniba Bilkisunshi tana kwance sa bias gado tana sharer bacci abinta. Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka itama kamar yadda Sulaiman yayi haka itama ta fara duban mijinta har a toilet ta dubashi bata ganshi ba cak ta tsaya da taga kofa a bude, a
hankali ta fara tafiya ta nufaci kofar da zata kaita falo wani faduwar gaba taji da bugun zuciya tsallako kofar tayi ta nufo mijina kam ta kame tsaye akan matsanancin tashin hankalin da taji, mijinta dearest dinta ta gani a zaune da wasu kananan kayan da hula da wasu rufaffun takalma kai! Sak shigar USMAN! Yadda yake zama, yadda yake kada kafa daya juye hularda yake yi kai! Kome sak na MAN! Daga kai yayi ya fara dubanta tun daga sama har kasa, itama suban nashi takeyi, nikewa yayi kau!! Ya wanka mata wani hatsa bibin mari said a ta fadi ta fasa bakin ta, kamar wanda ya dawo daga hayyacinsa y ace cikin wata murya wadda ko ba’a gaya maka ba kasan mace c eke wannan murya, yanzu idan Usman yaji yanda nayi miki fa ya fara dube-dube kamar wanda yaga usman din a falon, da karfi kuma ya juyo ya kalleta kallo irin na mugunta da tsananin kiyayya yaci gaba da Magana wannan dai ta mata, idan na kasha ki ai bai zai taba sani ba yana fadi yana cize hakoranshi, ya nufaci inda take ya sa hannun ya cafko wuyanta ya dagata dashi sama har ya cirata har karfi aka banko kofar shigowa falon! Tsohon nan ne da suka saba dashi, da karfi ya wankada mashin wasu ruwa da suke rike da hannunshi, wai gowa Sulaiman din yayi da karfi suka hada ido da tsohon, wurgarda Bilkisu yayi da karfi ya sheka ya nufi bangon falo tuma yayi ya tsunduma cikin bandon baya bace. Baban yaje ya tayadda ita kuka takeyi kamar ranta zai fita, ba dai Usman ne keyin duk wannan abinda ke faruwa ba, take fadi tana kuka mai tsanani. Ba Usman bane ke muku wanna abun amma sanadiyar sa ne duk wannan abun ke faruwa, how? Tayaya? Ina mijina kuma wane sanadine na Usman aka da yake faruwa dan haka ta fada tareda zubewa a kasa tana kuka. Gyara zama yayi ya fara fadi mata kamar haka --------
a hankali suka tattaka ya zuwa bakin kofar daki yaddazasu iya hango abinda ke faruwa a falon, da baya sukaja da kafri saka makon ganin wanan tashin hankali da basu taba gani shi ba, wata mace ce ko ince budurwa wace bata wuce shekara goma sha takwas zuwa sha tara ba, ake ja, batareda suna ganin mai jan nata bag a baki daya jikinta jinine faca-faca, kama kuwa kadan ya rage ya rabuda gangar jikinta, rokonsu take tana kuka don Allah ku taimaka mini, karaja sukeyi da baya suka rungume juna suka kankame waje daya, wuf tayi ta nufo su da niyar ta cafke su, kamar an wulla ta ta fada can gefe daya, sake mikewa tayi kanta yana shillo ta kara nufo su amma kamar a karon farko ma sake wurgata akayi, kuwa take kala-kala iri-iri tana yunkurin kamasu amma ta kasa, su kuwa suka buga suka kara ja da baya suncakankame juna, duk wani yunkuri, na shiga cikin dakin tayi amma ta kasa Sulaiman ne yayi karfin hali ya ja kofar daki ya rufa da karfi ya dawo daga baya. Duk hargowarda takeyi a kunnuwansu yake, addu’a suka yi suka tottafa ko’ina suka haye kan gado ko runtsawa ba wanda yayi-sai yanzu Bilkisu ta gano dalilin da yasa ta kasa shigawa acikin dakin, maganinda baban nan ya btane, haka suka zauna ba wanda ya koda runtsa idanuwashi, sai a shiyoyin asuba su duka bacci ya sace sub a tareda sun sani ba Sulaiman ya fara falkawa, kasa rufe bakinsa yayi sakamakon kashin ganin matarshi da yayi akan gado, kofa ya gani bude, a hankali ya tashi ya fara tafiya yana duba kofar, can ya hango Bilkisushi a falo zauna murmushi, zo dearet, zo mu karanta Qur’ani kama meye yayi kadan ya cuta mana, shi nake karantawa kazoo mu sauke Qur’ani a yau dinna, ajiyar zuciya yayi ya sauke nunfashi da karfi okay bari na dauko nawa Qur’anin, a’a ai gashi na dauko duka zo kawai mu karanta, fitowa yayi ya nufa ci falon ya tsallaka ya fada cikin falon, sai dai kuwa abinda bai saniba Bilkisunshi tana kwance sa bias gado tana sharer bacci abinta. Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka itama kamar yadda Sulaiman yayi haka itama ta fara duban mijinta har a toilet ta dubashi bata ganshi ba cak ta tsaya da taga kofa a bude, a
hankali ta fara tafiya ta nufaci kofar da zata kaita falo wani faduwar gaba taji da bugun zuciya tsallako kofar tayi ta nufo mijina kam ta kame tsaye akan matsanancin tashin hankalin da taji, mijinta dearest dinta ta gani a zaune da wasu kananan kayan da hula da wasu rufaffun takalma kai! Sak shigar USMAN! Yadda yake zama, yadda yake kada kafa daya juye hularda yake yi kai! Kome sak na MAN! Daga kai yayi ya fara dubanta tun daga sama har kasa, itama suban nashi takeyi, nikewa yayi kau!! Ya wanka mata wani hatsa bibin mari said a ta fadi ta fasa bakin ta, kamar wanda ya dawo daga hayyacinsa y ace cikin wata murya wadda ko ba’a gaya maka ba kasan mace c eke wannan murya, yanzu idan Usman yaji yanda nayi miki fa ya fara dube-dube kamar wanda yaga usman din a falon, da karfi kuma ya juyo ya kalleta kallo irin na mugunta da tsananin kiyayya yaci gaba da Magana wannan dai ta mata, idan na kasha ki ai bai zai taba sani ba yana fadi yana cize hakoranshi, ya nufaci inda take ya sa hannun ya cafko wuyanta ya dagata dashi sama har ya cirata har karfi aka banko kofar shigowa falon! Tsohon nan ne da suka saba dashi, da karfi ya wankada mashin wasu ruwa da suke rike da hannunshi, wai gowa Sulaiman din yayi da karfi suka hada ido da tsohon, wurgarda Bilkisu yayi da karfi ya sheka ya nufi bangon falo tuma yayi ya tsunduma cikin bandon baya bace. Baban yaje ya tayadda ita kuka takeyi kamar ranta zai fita, ba dai Usman ne keyin duk wannan abinda ke faruwa ba, take fadi tana kuka mai tsanani. Ba Usman bane ke muku wanna abun amma sanadiyar sa ne duk wannan abun ke faruwa, how? Tayaya? Ina mijina kuma wane sanadine na Usman aka da yake faruwa dan haka ta fada tareda zubewa a kasa tana kuka. Gyara zama yayi ya fara fadi mata kamar haka --------
Ku biyoni a littafi na biyu dan jin cigaban kayatacce labara.
Taku mai debe muku kewa Asiya Sadiq maccido
(Asikhan)
Excellent
ReplyDeleteHubbul Yakin: Complete Hausa Novels Book By Asiya Sadiq Maccido ~ Share4World.Com.Ng >>>>> Download Now
ReplyDelete>>>>> Download Full
Hubbul Yakin: Complete Hausa Novels Book By Asiya Sadiq Maccido ~ Share4World.Com.Ng >>>>> Download LINK
>>>>> Download Now
Hubbul Yakin: Complete Hausa Novels Book By Asiya Sadiq Maccido ~ Share4World.Com.Ng >>>>> Download Full
>>>>> Download LINK
Matar maza 3
ReplyDelete