AURE KO ZAMAN GIDA
BY
HAUWA MUHAMMAD JABO
Akan hanyar asibiti nida qawata
zeenah khalifa zamuje duba wata maqociyarmu da batada lafiya,Muna shiga asibiti
mukayi karo da wata mata da yara guda biyu a hannunta zenah khalifa tayi sokoko
tana kallonta.Ke zeenah khalifa kinji haushi ki kalli maza ki kalli mata.!
Banason wulaqanci hauwa jabo.! Mikike nufi da inkalli mata in kalli maza? kamar
wata bunsura..!!! Na kwashe dadariya nace yanzu dai yimin bayani mi kika
hango.?? Ta kwashe da dariya kibari kawai,Hauwa jabo matar nan ta hadu billahillazi.. Da
ace ba baqa bace sai ince wllhy ba indiyace keni muje muyi qawance da ita,Ke
zainab muna fama da talaucinmu zamuje gurin masu kudi.? Bazanje a wulaqantaniba
gaskiya,Ke Hauwa jabo wllhy kin cika tsoro,Idan bazakiba bari inje ingabatarda
kaina,Ta kwace wayata taje tana kuri. Bansan yanda sukayiba naga har sunyi
musanyar number suna yiwa juna murmushi wani namiji yazo naga yana mata magana
tay murmushi ya rungumeta hannunsa dayan hannunsa riqe da handbag dinta ya mata
kiss a kumatu ina tsaye ina kallo araina nace dama matan nigeria suna soyayyah
haka? In shot sun burgeni kuma inason inji tarihinsu da inda suka iya soyayyah
irinta Iranian saboda Iranian ne kawai zakiga sundaukarwa matansu jaka su
rungume jariri kuma su rungume matar kamar wani zai kwace musu.. !Zainb ta dawo
sai murna takeyi ina tsaye,Sai wangale baki takeyi zainab,Amma fa matar ta
haduko H jabo? uhun ba laifi!, Ke Wllhy kincika matsala,! Nidai muje, Zamu
shiga kenan sai gasu sun fito suna dagawa zainab hannu sai wangale baki take
har yar wushiryarta da dan dimple dinda take kuri dashi ya fito araina nace
zainb ansamu aikin yi, Munshiga mun duba mara lafiya munfito muka wuce city
plaza muka dan sayi ice cream muka samu keke npn sai gida..... Eshqi mano
too... tuye qalbam mimune....zandagi batu behtare..... Ringtone din zainb kenan
kuma gashi tashiga wanka naga anrubuta sister zainb araina nace waye kuma
sister zainb... hello, hello namesake, nasissim adaya banqaren naji dafada cike
da dariya... Araina nace wannan yar turkiyace ni jabo ba Turkish na iyaba
hakadai na amsa mata nasissim eyem ebit ta kwashe da dariya.. Araina nace
zatace ban iyaba na kwabsa, Sai tace ni ban iya wannan da kika fadaba nima nay
dariya, Tace yaushe zaku zo gidana da sauri nace gobe zamuzo ba matsala, Eh kuzo
ta fada cike da shauqi, Ta bani address dinta na rubuta zeenah khalifa na
fitowa nace namesake dinki takira tace gobe muzo... ihuuuuuuhw.!! Wani ihu tayi
tanajin dadi nima naji dadi ko banxa inason muje inyo gulma... Tun safe kinsan
yau zamuje unguwa ko? Unguwa kuma.? Lallai wllhy jabo kinji dadinki kin manta
zamuje gidan namesake dina.!!?? Au natuna qarfe nawa ma zamuje.?? 12 mukace
mata. Kk.. mun isa gidanta wani qaton gidane da shuke shuke ya rufe ko ina nace
anya nanne zainb karmuje a cire mana kai, Eh nanne mana muka danna bell maigadi
yabude mana yace su zainb ko mukace eh kushigo, Araina nace har angayawa
maigadi zamuzo Lallai anaji damu.. Munsameta tsakiyar gida tana ganinmu tazo ta
rungume mu...... muje zuwa muji yanda hauwa jabo zatayo mana gulma agurin
zainab...... Kukasance tare dani a
AURE KO ZAMAN GIDA part ♥♥♥AURE KO ZAMAN
GIDA♥♥♥•••••••• •••••••PART 2•••••••••••••••••• …Munci munsha mun hole anan na
fahinci zainab tanada balaeen saurin sabo kuma akwai tsiwa da wasan rainin
hankali, Nandanan muka saba da ita amma naga tafi maida hankali gurina ko dan
taga nafi hankaline ohoo..? Watannmu uku da sanin zainab duk ansanmu a gidanta
tana zuwa gidanmu sosai,Ranar munje gidanta, Nan nanemi ta bamu labarinta daga
farko tayi gardama daga baya mitayi tunani ta amince naso inyi shishigi
intambayeta amma sunyi rayuwa a iran ko amma sai nafasa nace bari in barta
kawai maji daga baya... Tun safee nazo inji gulma nikadai nazo saboda nasan
idan nazo da zeenah khalifa to labarin bazaimun dadiba, Nayi sa'a tagama
aikinta gaskiya zainab tanada kazar kazar batada son jiki ko kadan, Takawomin
fresh milk nashanye, Ta gyara zama ta fara bani labari kamar haka.........
Sunana zainab Abdullahi mahaifiyata gurin hai huwata Allah yamata cikawa,
Mahaifina mutum ne mara kulawa sosai, Sam bai damu da tarbiyarmu ba baidamu da
chin muba bai damu da shanmuba, Gamu mu mu shida ne a gidan ni kadai nake agun
mamata data rasu sauran biyar din duk yayan kishiyar mamanmune maza uku mata
biyu,Agurin kishiyar mamata na girma, kishiyar mamata mutumce wacce batayi dan
Allah idan kikayi mata zata miki idan baki mataba to bazatayi mikiba,Amma bata
cutar da kai sai ka cutar da ita, Tana dauramin tallan kayan miya ranar da
nasiyar to zamuji dadi idan kuwa yayi kwantai to bamu ba abinci sam saboda da
dan ribar da take samune take bamu abincin safe dana rana, Nadare kuwa baba
yake bayarwa, Bata ta6a dukanaba kuma bata cika yimin fadaba amma tanacin uban
yayanta sosai nice babba agidan, Banta6a sanin hanyar makarantar bokoba balle
ta addini har nakai shekara goma sha daya bana karatu sai yawon talla, Ina
sha'awar boko sosai inada wata qawa wacce muke yawon talla tare da ita amina s
bawa, Ita tana dan boko ta bani littafinta daya tafara koyamin A B C D.... Ina
ganewa sosai saboda inada hazaqa duk ranarda muka saida kayan miya da wuri to
ranar zamu zauna muyi boko wasa wasa har nafi amina iya karatu sai tafara jin
haushi saboda musun da nake mata akan wannan haka yake tace a'a ba haka yakeba,
Haka yake tadaina koyamin komai ataqaice duk wata takardar qosai ta unguwarmu
idan nagani sai nakaranta na iya hada kalmomin english inkaranta amma bansan
ma'anarsuba ke intaqaita miki jabo duk wani karatun indai karantawane ina iyayi
da rubutawa..... Akwai wata rana na fito tallan wara saboda yanzu nadaina tallan
kayan miya wara nake talla yafi kasuwa ina tafiya naga wata qatuwar mota baqa
baka ganin waye aciki,Anyi parking dinta a gefen hanya, Kusan wata daya Kullum
sainaga motarnan wani yaro yace wai mai motan yace ki kawo wara na kalli motan
lokacin iya tunanina nasan mai Wannan qatuwar mota bazai ci waraba, Nace
bazanje, Shegiya matsiyaciya arziki yana kiranki kina gudu kar kije miya dameni
wannan mutumin duka yake siya yace kikai masallaci.... kukasance tare dani a
AURE KO ZAMAN GIDA part 3 ♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥•••••••• ••••••PART
3•••••••••• …Abinda yasa naqi zuwa kuwa kiranshi maman jamila (kishiyar maman
mu) tace koda ban saida tallan da ta dauramin ba kada in kuskura wani ya bani
kudi yamun juye ko in bishi gida duk ranarda nayi haka sai ta yankani,Kuma zata
riqa dukana kamar yanda take dukansu jamila (yayanta kenan )Ashe su jamila juye
suke ana ta6a lalubarsu shiyasa take chin ubansu.. naceto, Zo karakani muje
tare har yace bazai jeba sai kuma yace kawo inkaimuki na bashi ya kai ya dawo
yace waranki na dari shida da talatinne ga kudin kikai wa almajirai waran. Yace
min ko ki saida rabi kikaiwa almajirai rabi ki boye sauran kudin. Har na yarda
da shawaransa sai kawai naga idan maman jamila tagane zataci ubana tace ina
nake samun kudi, Nakoma gida da wuri akace ya akayi nadawo da wuri nayi bayani
tace kar dai in kuskura in shiga motarsa kuma duk abinda ya bani kar inci, Nace
to, Tun daga ranar idan nafito talla nan zan tarar da motar mutuminnan nan kuma
zan barta, Banta6a zuwa jikin motanba sai na jira audu abokin tallana yazo
yakai asaye abani kudi... Yanzu babana ya chanza yana bamu kulawa sosai kuma ya
sakamu islamiya dukanmu, Inada qoqari sosai amma su jamila sai a hankali cikin
shekara daya na sauke qur'ani nashiga bangaren hadda,Namma banyi qasa a guywaba
wata tara na haddace qur'ani da tajwid da komai, Nice tafarko atarihin
makarantarmu da ta haddace qur'ani cikin wata tara dama tun lokacinda nake
karatu kamin in iya na haddace shiyasa da nazo sai yamin sauqi nandanan na
haddace, Akayi gagarumin bukin yaye dalibai hadda shugaban makarantarmu yazo
nay karatu da muryar nan tawa nasamu kyaututuka sosai agurin malamanmu da
manyan baqi, Yanzu na daina talla saboda baba yana iya bakin qoqarinsa yachanza
sosai yanzu baya barinmu da tsumma kamar da mun wadata sosai, Ranar nadawo daga
islamiya baba yace inzo naje gunsa sai yacemun wai aure zai nida ko nono banida
za'ayimin aure gani da qaramin jiki saboda ta dade da fara nono amma ni yar
qwaila dani, Bance komaiba nace to, ko kinada wanda kikeso nace a'ah, Aka sa ranar
aurena aka dauramin aure da mijin da banta6a ganiba bansan ko waye shiba…
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 4 ♥♥♥AURE KO ZAMAN
GIDA♥♥♥°°°°°°°°°°° °PART 4°°°°°°°°° …Iya tunanina aurena da wani dan mashukurin
mai kudi rana daya akayi shi dan jama'ar da suka taru sunfi qarfin suzo aurena
amma daga qarshe mungane gurin auren nawa sukazo,Har bayan daurin aurena ina
gidanmuban tareba, Bana fita ko ina, Sai taya maman jamila aiki, Ke in gayamaki
jabo wllhy saida nayi shekara biyar agidanmu ba miji ba labarinsa kuma ba
zancen tarewa, Har na balaga, Ba miji inason inyi magana amma kunya ta hanani
yin magana duk qannena mata jamila da hafsatu an musu aure jamila da wani har
ta haihu da wani ciki ajikinta hafsatu kuma da cikinta tsoho, Nigani agida farko
abin baya damuna kuma sam ban fuskantar tsangwama agurin maman jamila, Yanzu na
girma nasan miye aure saboda ina zuwa wata islamiya dadare ta matan aure a
unguwarmu, Inajin abubuwan da ake koya mana mata da wuri suke zuwa dan suyi ta
tadi, Mijina kaza mijina kaza nidai bana ce musu komai, Abin duniya ya isheni
nayanke shawarar zan yiwa baba magana sai dai kuma kunya nakeji nace ko infara
yiwa maman jamila maganane inji abinda zatace, Haka kuwa akayi, Ina biya mata
karatun qur'ani bayan munqare muna hira saina cemata wai maman jamila waye
mijina..? Naji kamar bata jini ba namaimata tambayar, Ta d'ago ido ta kalleni
tace mun kitambayi babanki, Nayi shiru, Ban qara cewa komaiba, Munqare karatu
da ita na shige daki, Sai tunani kala kala nakeyi gaskiya inason sanin miye
matsayina matar aure ko bazawara? Zaman aure nake ko zaman gida? Shekara biyar
ba miji ba labarinsa sai wani niqab da baba yasani sakawa tunda aka dauramin
aure, Yan kwanakinnan nashiga damuwa sosai sai nake tunanin ko dan banida uwane
aka yimin haka, Lallai maraici hadarine, Nashiga rera kuka mara sauti nayi wata
biyu Kullum sai nayi kuka duk wata walwala ta gushe mini banida aiki sai tunani
da damuwa nashiga tsaka mai wuya narame, Na kode, Nayi baqi, Duk wata halitta
ta jikina saida ta chanza.. Na yi alwashin zanyiwa babana magana, Bayan yadawo
daga kasuwa nace inada magana dashi yace to naje gurinsa, Inson inyi magana sai
muryata ta fara rawa bansan lokacinda kuka ya subucemin ba nayi kuka sosai baba
ya rasa gane kaina gashi ba kowa agidan saini nima dan banje islamiya bane,
Daqyar nasamu nayi shiru amma nakasa tambayarsa, Can baba yace nasan zaki damu
ace shekara biyar da watanni da daura miki aure amma bakisan mijinkiba.! kuma
baki tare Gidankiba ba ,Amma kiyi haquri nasan banmiki adalciba, Nafarko ban
baki damar zabar mijin da ranki yakesoba ban tambayi ra'ayinkiba inji shin kina
sonsa ko yaya,! Bakisan wayeba bakisan komai akansaba hasalima bakisan
wayeshiba ban barki kinyi karatun bokoba, Sannan shekara biyar dai dai da rana
daya bakimin magana ba Allah yayi miki albarka kuma mijinki wannan shekarar zai
dawo insha Allah, Idan ya dawo tare gidanki tashi kije ki kwanta Allah yayi
miki albarka, Koba komai raina yayi sanyi najin cewa mijina zai dawo wannan
shekaran dan wllhy na gaji da zama da igiyar aure akaina… Kukasance tare dani a
AURE KO ZAMAN GIDA part 5 ♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥•••••••• •••••PART 5•••••••••
…Na rogi alfarmar baba ya barni in riqa zuwa wata yar makaranta da ake lesson
anan qasa da gidanmu baba ya amince, Kuma yace inci gaba da kare mutuncina,
Nafara zuwa lesson abubuwa da yawa nasan sunansu amma bansan ma'anarsuba
malamin da yaga inada hazaqa sosai sai ya bani kyautar wani littafi sunayen
abubuwa da hotonsu cikin sati daya na haddace su duka dama nasan sunayen
abubuwan kawai bansan sunayensubane sai yanzu, Ahankali nafara iya magana da
english cikin wata biyu.. Hauwa jabo ko kin gaji mu bari sai gobe nace a'ah
muci gaba kawai, Tayi murmushi taci gaba.... Ranar nadawo daga lesson dina tun
zauren gidanmu naji wani qamshin turare mai rudarwa qamshi sosai naji wata
sassanyar murya ana wani yare bansan mi suke cewaba a lokacin (to namifahmi
hamun juri k to hamsari man hasti uwn ham hamsari mani to modare bachem hasti,
chira mutawajji nisti ) adaidai lokacin nabi gefensa na wuce fuskansa na kallon
yamma so baisan nashigoba na shigo tsakar gida natararda baba fuskarsa cike da
fara'a nima nayi murmushi nace baba miya faru naganku kuna jin dadi yace ABDUL
AZEEZ ne yadawo.Waye kuma abdul azeez baba? mijinkine, mijina? Eh Sai ban sake
cewa komaiba yayiwa su baba sayayah sosai ina tsaye ina kallonsu, Na wuce
dakina nan natarar da kaya niqi niqi naci dana sha dana shafawa tufafi kala
kala turaruka kala kala na kira maman jamila na nuna mata tatayani buda wasu
naji dadin kayan koba komai nasan wanda yasiyo kayan mai kudine, Wasu kayan
irin na qasar wajene bana nigeria bane hadda waya a cikin kayana (LG G Flex)
wayan ta hadu iya haduwa sai wani envelope nagane wasiqace naqi budawa saida
maman jamila ta fita .... Hello my wife Sai kuma number sa daya rubuta a qasa
banta6a ganin letter irin wannan ba, Naji dadi koba komai nasan cewa inada
miji, Tun safee baba ya kirani yace in kunna wayan da aka bani na kuwa kunna ko
minti hudu ba'ayiba kira yashigo naga ansaka AZEEZ nidai bansan ko wayeba na
dauki wayan nayi sallama ingayamiki jabo bai amsaba saida nayi sallama biyar ba
amsa nayta danne danne har na gane yanda ake kashewa karo na biyu ya sake kira
na dauka namma ba magana nasake kashewa karo na na uku naqi dauka har ta qare
ringing ya turo sms (I luv d way u r talk,ur voice is agreeable ) Kwana shida
da dawowar azeez aka fara shirye shiryen tarewana anyi min duk abubuwan da suka
kamata maman jamila ta gyarani iya qoqarinta, Aka kaini gidan mijina in
taqaitamiki labari, H jabo saida nayi wata shida cur agidan nan bansaka Abdul
azeez a idonaba komai na gidan ya wadata ba abinda nake nema, Duk sati za'a
kawo min cefane da kudi ko zan buqata kuma aka bani mota da driver duk inda
nakeson zuwa akaini, Ingayamiki jabo saida na gwammace zama gida da zaman gidan
aure, Rayuwa ta sauya bana zuwa ko ina sai gida zubi zubi tun inajin tsoro har
nadaina jin tsoro nabarwa Allah komai, Nayi magana da malaminmu mai mana lesson
akan yasamomin wanda zai riqa zuwa gida yana mini lesson, Yasamomin wata mata
tana koyamin dan science da wasu subject na seconds skul naba kaina wahala
sosai wajen ganin na iya karatun science Kullum ina duba internet ina daukar
lecture a internet malamar har mamakin basirana takeyi dan kuwa har tamun hanya
inje in zana waec idan naci zata nemamin admission a university dinsu, Sai da
na zana waec naci ina zancen zuwa kenan sai ga saqo daga mijina inje za'amun
international passport, Wata mata takaini immigration office akamin passport
aka kar6o min ticket da visa na barin qasa..… Kukasance tare dani a AURE KO
XAMAN GIDA part ♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥★★★★★★PART
6★★★★★…Wai ashe jabo duk zaman da nakeyi. Abdul azeez baya nigeria
gabaki daya yana iran abinshi, Ni ya zan bar wata qasa ni kadai alhalin ban
banta6a zuwa koda airport ba, Haka nayi kuka nayi bankwana da yan uwana dan
bantabm6a tunanin zan dawoba nashiga mota sai kaduna, Ina ganin jirgi jikina ya
mutu na tabbatarda bazanyi raiba matsawar na hau wannan gangaramar, Wasu
zafafan hawaye suka zubomin tunda nashiga jirgi nake kuka har muka isa Lagos,
Daga lagos zamuyi fly 6:30 har aka gama shiga jirgi ban saniba saida wata mata
tamun magana sannan nagane cewa jirginmu saura 7mnt ya tashi tataimakamin
nasamu nashiga jirgi ina shiga idon kowa akaina har ina tuntu6e nazauna ga
fitsari inaji ina tsoron tashi, Da ya matseni haka nan na lalla6a naje nayi
amma ba ruwan tsarki naga zan batawa kaina lokaci nasaka tissue na goge na
fito, A daddafe muka isa Beirut a Lebanon kenan, Na sake shiga wani jirgi sai
emirate dubai kenan, Nasha kallo a dubai qasar ta burgeni sosan gaske a dubai
nasamu transit 18 hrs wllhy haka na zauna a airport ga yunwa kamar zata kasheni
na daddafa naje naci wani abinci $50 bangane komaiba ba dadi sai dan banzan
tsami nayita amai sai zazza6i anan bacci yayi awon gaba dani ban farkaba sai
9:12 kuma 8:30 zamuyi fly ataqaice nayi missing din fly naci kuka har na gode
Allah naje gun ma'aikatan gun namusu bayani sukace jirgina ya wuce sai na sake
sabon bucking suka min komai da komai, Ina nan zaune abin tausayi sai ga wata
mata da mijinta zasuje iran kuma hausawa ai kamar ansakani aljanna haka naji
nadan gaya musu yanda akayi nayi missing din fly sukaita dariya nima saina
wayance nayi dariya amma nasan sungane ni dibgaggiyar local ce ni, Dan kuwa
kina ganina kinsan sai a slow ko a shigata, Sun taimakamin mun isa iran nanma
nayi wani qauyanci dan kuwa anbani number akace idan na iso airport din tehran
inyi waya sai kawai nabaiwa maman nargees kudi nace ta siyamin ticket nabisu
garinsu mashhad saida muka isa maman nargess tasiyomin sim card nasaka nakira
numbar da aka bani, Nayi sallama aka amsa da wata sassanyar murna mai ratsa
jiki dajin muryar nagane cewa antsorata ana tunanin na6atane kina ina yanzu,?
Airport kisamu wani mutum cikin ma'aikatan gurin inyi magana dashi nasamu wani
mutum na bashi yagayawa. Abdul azeez cewa ina mashhad, Yaji haushi sosai kaman
in kar6i wayaya kashe nakira ba'adauka qarshe ya kashe wayanshi natsorata sosai
naje gun wani mutumi shi ba England ba sai surutu daga wata gasa nake (az kuzo
omadid ) Ni ba gane yarensu nakeba su kuma ba wani gwagwaran turanci ba haka
dai nasamu har ya gane me nake nufi ya siyamin wani ticket daga mashhad zuwa
tehran inkoma inda nafito yamun komai mutanen gasar iran akwai tsoron Allah
tare dasu ga kuma amana natashi nakoma tehran ina isa nasake kiranshi naji
wayan akashe can naji wayan yayi ringing na dauka kina ina? Nadawo airport
dinda na sauka daga farko yayi shiru ina hello naji shiru sai na kashe wayan
ashe wai ya biyonine ni kuma nakoma garin haka na qama zama a airport ga qasar
da wani mahaukacin sanyi wayata ta mutu nasamu wani mutum ya nuna min masallaci
nayi sallolin da ake bina nasaka chaji sai bacci da gurin akwai dumi ban
farkaba sai asuba shima yanwa ta tayar dani ina duba wayana naga 38 miss call.
Banji haushiba nayi sallah asuba na tashi na nemi gurin chin abinci ina chin
abinci naji ance min ke.!!… Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 7
♣♣♣AURE KO ZAMAN GIDA♣♣♣:::::::: :::::::::::PART 7:::::::::::::::: …Ban waigibo
hasalima banjishiba saboda na tafi duniyar tunani, zainab ce.?? Na waigo sai
naga wani kyakyawan mutum dogo fari tareda yan sanda guda biyu, Sukayi yare sai
naga sun juya suntafi, Ina dago kaina ya kwasheni da wani wawan mari saida na
fadi qasa, Anan nace Lallai ma mutuminnan dan iskane ya aureni ya ajiyeni gidan
ubana shekara biyar, Sannan yakawoni gidansa wata tara, Ba kulawa, Yaturoni
daga qasa zuwa qasa ni kadai saida na hau mutuwa(jirgi) sau shida sannan inyi
kwana hudu ina garari qasa da qasa inzo ya rasa mizai sakamin dashi sai mari
gashi banida lafiya , za'ayi ta kuwa dan wllhy sai ya sakeni yanzu kuma ya
maidani gidan ubana nagaji da Wannan bala'een tun banida wayo nake hadiyar
baqin cikin sa har yanzu na tashi na dauki wayata naja kujera na zauna, Bai min
maganaba yaja hand lgt dina ya tafi yana jiran in biyoshi nayi banza dashi,
Shiru sai da yakai gate din fita yaga bani ya dawo, Na daura kaina akan table
din gurin ina kuka yazo ya ta6ani ban motsaba ya girgizani ya matso kusa dani
yace kizo muje gida, Wani dum naji, Araina nace dan yasan muryarsa tanada
dadine shiyasa baya magana, Ashe duk abinda mukeyi a police din gurin suna
kallonmu a cameran dakinsu yazauna bai sake maganaba sai ga yan sanda sunzo
suka ja shi gefe suka tattauna suka dawo police yacemin (he is ur husband?)
Araina nace inaga mutanen wannan qasar basu iya turanciba sai yarensu, Nace
masa (no he is nt my husband ) Ya zare ido ya kalleni da idonsa, Nasaukar da
nawa idon, Suka sakeyin yare police ya qara tambayata mijinkine nace musu a'ah,
Suka jamu mukaje wani daki suka fara masa question wai idan matarsace ina
certificate din auren mu? Nan yayi turus baisan nigeria basa wani certificate
ba nan nafahinci bayason magana sosai duk yarasa mezai musu, Suka kar6i
passport dina sukaga sunana da sunansa suka kar6i passport dina da nashi sukace
mutafi kamin suyi bincike,Intashi muje na sake fashewa da kuka, Yayi bala'een
daure fuska yayi musu yare sosai sai ya miqa min hannu na kalli yanda ya daure
fuska na saduda na miqa masa yamatse sosai ya jawo jikinsa ya rungumeni na
natsu sosai ban ji komai a rungumar da yamunba saboda ina masa kallon
azzalumine kuma ga tsoronsa da ya kamani sai qamshin turarensa da yake dukan
hanchina, Mukaje yatari taxi muka shiga munyi tafiya sosai sannan muka isa inda
zamuje muna isa ya bani key yace ga gidanki nan. Tofa… Kukasance tare danu a
AURE KO ZAMAN GIDA part 8 ♦♦♦AURE KO ZAMAN GIDA♦♦♦°°°°°°°°° °PART 8°°°°°°°°°°
Miyake nufi da ga gidananan yana nufin ya tafi kenan wani sabon kuka nafarayi
ga sanyi inaji harna tashin hankali amma ba yanda zanyi naduba gabas da yamma ba
wani mutum na lalla6a na bude gidan nashiga gidan qaramine zaman mutum daya na
zauna nayi kuka har na gode Allah ga sanyi kamar me saboda anyi snow sosai
gashi ni bansan yanda ake kunna heater room ba danaga zan mutu da sanyi natare
kitchen da zama, Wato ya raboni da iyayena yakawoninan dan yaudara garama
nigeria ina ganin iyayena idan naso ganinsu amma yanzu idan naso ganinsu sai na
kashe over half million sannan zangansu, Lallai ina cikin tashin hankali mara
iyaaka, Satina uku bansakashi a idonaba narame nadaina chin abinchi ranar naji
hayaniya ashe maqociyatace mijinta ya rasu naje sunata kuka sun bani tausayi
talakawane ba laifi yar budurwar yarta tana gane English kadan kadan shima idan
ta kwa6a sai cikin mutum yayi ciwo kan dariya, Ahankali nasaba dasu sosai suna
koyamin yare kadan cikin sati biyu nafara fahimta Abdul azeez kullum sai yamun
sms ya nake amma bana bashi amsa wai ashe akwai camera a gidan wacce duk wani
motsina yana gani a gidanshi shiyasa yashareni watana uku bansakashi a idoba na
yanke hukuncin komawa gidan su makwabciyarmu da zama tunda yanzu nasaba dasu
sosai kuma batada yaro namiji a yaranta mata biyune. Na kashe wutar gidan gaba
daya na tafi abina yare kam alhamdu lillah nagama iyashi tsab, Nagayawa mai
kawomin kayan abinci idan ya kawo min kayan abinci nan gidan zai kawowa komai
nawa nan nake yinsa arayuwa kwata kwata namanta da abdul azeez hankalina kwance
nakashe banzar wayar da yakemin sms, Ashe yayi tafiyane shima shiyasa bayi gane
bana gidanba yaje Turkey wani aiki na wata daya yadawo ya kunna cameransa yaga
wayam basa aiki anma kasheshe gaba daya yayi forwarding din karsheb zamanta
gidan yaga tana hada kaya da komai dakomai ta kashe wuta yaji tsoron ko ta gudu
ya tuna passport dinta na hannunsa hankalinsa yayi bala'een tashi bashiri ya
dawo gida qofa a gargame nan ya zauna ya fara danasanin abinda ya aikata tabbas
bai yiwa zainab adalciba koda yasan shi yayiwa matarsa alqawarin bazai kula
wata maceba matsawar tana raye, Zainab itace za6insa tun tana yar shekara 9
yanemi aurenta aka bashi ita, Itace za6insa, Ita yakeso, Dan yanasonta ya
aureta, Ya auretane dan kar wani ya gwace masa ita yasata zaman kulli shekara
hudu ya ajiyeta gidansa a naija wata tara ya kawota qasar da batada kowa
batasan kowaba ya tafi ya barta yana ganin halinda take ciki amma dan kar ya
batawa matarsa uwar yayansa rai yaqi za6insa wacce sonta yake neman kasheshi,
Yamanta itama zata haifamasa yarane, Yanzu ina zai sameta..? Ina zuwa zainab
kina nufin Abdul azeez mijinki yanada wata mata?? Kibari kawai wllhy mata harda
yaro daya inna lillahi wa inna ilaihi rajiun... Hauwa jabo muje muyi sallah
mudawo in qarasa miki.… Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 9 ♥♥♥AURE
KO ZAMAN GIDA♥♥♥°°°°°°°°°° °PART 9°°°°°°°° Jikina a mace nayi sallah dan abin
ya dauremin kai jin cewa azeez yanada mata harda yaro, Muci abinci sai muci
gaba ko jabo nace ai ina azumi ta kwashe da dariya, kinmanta kinsha fresh milk
dazu nima abin ya bani dariya dan kawai insha labari nace ina azumi tamana
girki indomie mukaci a gurguje taci gaba da bani labari... In gayamiki jabo
kamar ance fito dan ba inda nake zuwa sai wani park na bayan gidana shima
mutane suka fara damuna suna cemin (siya pust)Baqar fata kenan nadaina zuwa ina
gida abina ina fitowa naganshi zaune dirshan cikin sanyi yana kuka wllhy jabo
ko kwaya zarra banji ya bani tausayiba hasalima wani tsanarsa da nayi duk
lokacin bansan yanada mataba, Ina kallonsa miyaji sai naga ya daga kai da qarfi
ya kalloni hadi da wata irin kyakyawar aziyar zuciya, Ya miqe tsaye ya bude
qofar gidan ya shiga kai tsaye na koma inda nake har magriba ban shigo gunsaba
nama manta dashi inachan gurin makwabtana yar tsohuwa dai tagane akwai wani abu
(chi shod dokhtaram?) Miyake faruwa yata ( hech) ba komai (pas chira shoharat
omada wali to khushhal na shodi ?)To miyasa mijinki yazo bakiyi murnaba(Hech
momon alan miram pishash)Ba komai mama yanzu zanje gurinsa(Affarein dokhtari
khub zud baro guna dore az rahi dur omade istiqbalash ham na karde)Da kyau yata
yi sauri kije, Bazaiji dadiba ace yadawo daga tafiya amma kinqi kije tarbarsa,
(Boshe momon)To mama. Na fito sumi sumi na shigo a parlour naganshi zaune yayi
wujiga wujiga dashi ya kalleni ina shigowa ya miqe tsaye naja natsaya na dauka
zai kwasheni da wani marine kamar yanda yayimin a airport, Amma sai naga
sa6anin haka, Durqusawa yayi gabana yana kuka kaman qaramin yaro yana bani
haquri ya cutar dani yayita surutansa har yagama bance masa komaiba, Yatashi
yagoge fuskarsa wai inshirya zai maidani wurin aikinsa nanfa aka fara sabuwar
rigima dan bazan yarda yakaini wani sabon guri ya ajiyeniba alhalin bansan kowa
agurinba, Nan nashiga rera kuka yazo yana lallashina amma naqiyin shiru, Yayi
yayi naqiyin shiru sai shima ya zauna ya fara kuka lokacin abin ya bani mamaki
ace kamarsa yana kuka sai ya bani tausayi ahankali na daina kukan natashi na
bashi guri intaqaita miki jabo saida yayi nasarar barin wannan gidan dani...
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 10 ♥♥♥AURE KO ZAMAN
GIDA♥♥♥<×><×><× >PART 10<×><×><×> Nayi kewar
maman sumayyah maqociyata sosai amma yana iya sai haquri, Zamana dasu na waye
sosai kuma nayi clean coz sumayya yarta yar duniyace irin shigar datake agida
da yanda take hulda da mutane nima na koya dama nima ba bayaba gurin shed'ana
lokacin idan kika ganni sai kince nayi karatu ne wata university jabo.... Mun
isa gidan da zamu zauna, Gida qaton gaske yanada part biyu a dayan gefe muka
wuce da kayana gidan yaci uban gidan da na zauna sau dubu, A parlour na zauna
fuskata a daure yaqare gyara komai ya siyomin pizza inajin yunwa dole naci, Yazo
yazauna yaci gaba da bani haquri har ya gaba ban ce mishi komaiba, Ina kwance
ina game da wayata najiyo hayaniya awaje kuma ga dukkan alamu da hausa ake
fadan hayiniyar tayi yawa kamar ma gidana ake yinta ina fitowa nayi karo da
wata mata yar lukuta da ita dan takaiki jabo an, Ina zuwa abdul azeez yachanza
yare yakoma farsi yace (turu khuda ba zabani khudamun juluyesh harf nazan
namikhom alan bi fahme)Dan Allah karkiyi magana da hausa dan banason yanzu ta
gane abinda muke ciki, Matar itama da yaren tace (khub agyar nami khod bi fahme
y kari kun)Idan bakason ta gane kasan yanda zakayi dani, Sukayi ta magan ganu
da yare inajinsu basusan adaqe nake kallonsuba dan duk inajin abinda suke
fadaba gashi batama iya yaren ba, Abin yabani dariya sosai yanda take cewa sai
ya maidani inda yadau koni ita bazata zauna daniba, Araina nace nima bari in
ta6a nawa iskanci dana koya agurin sumayyah, Na matso kusa dashi na rige
hannunsa yanda koda yayi qoqarin kwacewa bazai iyaba nace masa eshqam (my dear
) Wannan matar da ka samo tazo tana mana haushi agida kaman karyafa?? Ta juyo
da qarfi da daga hannu ta wankeni da wani wawan mari, Kaji tassss itama ya
wanketa da mari nima na wanketa da mari sai tayi sololo tana kallonmu dan
gaskiya ta mata yawa nima nasan nayi jarumta jabo, Dan matar agirme ta girmeni
takai 34yrs fa nasaka hannuna na damana rungumeshi ta baya na kwanta a
qirjinsa, Nace mata duk iskanchin da zakiyi karki kuskura kice zaki dagawa
mijina hankali najawoshi shiko solon sai ya biyoni nashiga daki na kullu qofa
ni na barta a parlour tana zage zage ta fasa abunda zata iya fasawa ta gaji ta
tafi, Ingayamiki jabo tunda nashiga daki na wuce bayi na kulle kaina shiru har
yakirani na kunna ruwa yaji qaran ruwa yasan dai cewa inajinsa yayi jira yayi
buga gofa har ya gaji nayi banza dashi, Kinsan wannan matar wai matarsace ashe
dama yayi aure har sunada yaro, Ke wllhy jabo haka nasamu kaina ina bala'een
kishi da matarsa dukda nasan cewa banasonsa, Amma matar ta bani haushi, Nayi
kuka har na nagaji, Nidai bansan bala'een da yake biye daniba niba uwaba dasai
ingayamata haka nayi ta fama da baqin cikin kishiya amma duk da haka tsorona
take dan duk bala'een da zatayi bata zuwa kusa dani saidai tayi nesa dani,
Ataqaice ingayamiki hauwa jabo, Matarnan maza takebi ke hatta yaron da ta haifa
ba na azeez bane kuma duk ni na ganesu, Yanda akayi kuwa shine.... Kukasance
tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 11 ♥♥♥AURE KO ZAMAN
GIDA♥♥♥<<•>•<•> •>>PART 11<<•>•<•>> …
Ina gaya miki jabo kullum idan abdul azeez ya fita sai tayi wata baquwa da qaton
hijabinta kinsan Iranian akwai saka hijabi kaman larabawa to haka baquwarta
take zuwa kullum, Kuma sai mijinta ya fita ranar ina wajen swimming pool ina
kallon ruwa sai kawai naji maganar namiji amma da farsi suke magana tana
cemishi.... Kaima kasan ina sonka kuma nafisonka akan Wannan mutumin wllhy abu
kadan nake jira in kama gabana dan nagaji da zama dashi,Nidai duk wuya duk dadi
karki manta dani kinsan idan baki bazan iya rayuwa ba, Duk wannan maganar da
yaren farsi sukeyi, Basusan inajinsuba, Abinda yasa ban gara tantacewaba kuwa
shi yaren farsi bashida mace ba namiji suna zuwa tace mishi karyayi magana ga
yar iskar yarinyar nan sukayi dariya a hankali suka wuce kinga zargi bashida
kyau jabo, So banyi saurin zarginsuba duk da haka amma abin ya dauremin kai
matuqa dan kuwa muryan namiji sosai naji, Bayan kwana biyu yaqara zuwa ita kuma
tadan fita sai nace masa batanan yayi kaman bayajin hausa inata magana ba amsa
sai kawai namishi na kurame najawo hannunsa nashigo dashi sassana na zaunar
dashi a parlour har tadawo, Tunda muka shigo parlour na yake bina da kallo duk
inda nayi, Naji tsoro sosai dan kallon da yakemin kallon da saurayi yakema
budurwarsane, Nashare kar yagane, Ya miqe tsaye yamin alamar zai tafi inda
nayarda namijine takalminsa dana gani number 46 nasan ba qafar maccen da zata
saka wannan takalmin nakwashe dadariya nashe da shigiyar qafa taki kamar ta
masu kwasan kashi, Yajuyo ya kalleni rai abace amma baicemin komaiba na sake
cewa kinsaka hijabi kin rufe rabin fuskarki kamar munafuka daganin yanda yakeyi
nasan yanajin abinda nake cewa amma ba halin yamin magana asirinsa ya tono
naqara cewa tsawo kamar palwaya nace duk mijin da ya aureki yayi asara mace
kamar namiji ga munin bala'een dagani kin hada dangi da bare bare wannan uban
muni haka kai amma duk yayi qawance dake yaji haushi itama maryam din asara ne
yasa tayi qawance dake, Wannan magan ganun da nake masa inayine dan kawai yayi
magana inji shin namijine ko mace amma yaqi yayi saima daure fuska da nayi muka
kawo kofar shiga gidan ta nace mishi (khuda hafee) Sai anjima yanda nafada irin
nayan koyo kar yayi tunanin na iya yaren, Yamin murmushi ya daga hannu araina
nace kinga gardin banza wllhy wannan namijine kuma saina tona musu asiri abin
duniya ya isheni sai wata dabara tazomin kamin suzo lambu suyi hira sai insaka
wayata agurin inyi recording din abinda suke cewa hausa da farsi duk ina ganewa
ranarda nasami abinda nakeso kuwa ranarda sukayi maganar cewa shi ya gaji
gaskiya zai sace mustafa (sunan yaronta kenan) Dan yana buqatar dansa agidansa
tanata faman roqon ya rufamata asiri har taqare hada dukiyarta sugudu tare sun
saka ranar da zasu gudu nikuma nashirya tona musu asiri karkiyi tunani cewa
wani abu yana shiga tsakanina da Abdul azeez aah ba komai tsakaninmu dashi sai
sallama, Sai sannu da zuwa, Ranar da safee natashi yana fitowa nace masa inada
magana dashi yau misalin qarfe biyu na rana yazo gida kuma banason idan zaizo
yagayawa uwar yayansa zaizo kawai idan lokacinda nakeson ganinsa yayi zan
kirasa yakuwa amince yanajin dadi, Yadauka wani abune kwarton maryam yana zuwa,
Da kamar awa daya nakira Abdul azeez nace yazo da sauri kuma kar yazo da
motarsa………… Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part AURE KO ZAMAN GIDA
*PART 13 Na Hauwa M Jabo. Tunda muka iso nake tunanin yanda zan bullowa plane
in mishi magana amma nakasa saboda banga fuskaba sai nayanke shawarar bari in
toneshi ingani haushi zaiji idan yaji haushi sai inbashi haquri haka kuwa akayi
bayan sallar isha yana zaune kamar wani gunki nazo ina kur6ar tea ahankali nace
masa kana tunani uwar yayanka maryam ne...!??? Ya waigo ya kalleni cike da
mamaki da al'ajabi nasake maimaita abinda nace naqara da cewa ko in samo maka
pic dintane ka kalla ko kaji sanyi,? Namiqe tsaye nace ko kawai kabita qiyama
ku soye acan zaifi kazo nan kana tunaninta ko ka kar6o yaronka agurin kwarton
matarka nasan shi yake damunka.!, Na kama hanyar dakina naji an kamoni ta baya
da qarfi wllhy jabo saida cup din da yake hannuna ya fadi, Kinsanni akwai
iskanci amma akwai tsoro, Ya jawoni daf dashi ya d'ago kaina da qarfi yana
kallona har inajin nunfashinsa yana dukan fuskata yace wllhy wllhy Wllhy..!!!
Idan kika qara yimin maganar maryam da mustafa sai kingane baki da wayo a
gidannan ya dallamin wata muguwar harara sannan ya sakeni, Nace nasan zaka iya
kasheni ma tunda na rabaka da uwar yayanka da danka da kake tunanin ita kadai
zata iya haifa maka yaya, A fusace na fadi maganar ashe mutumin yagane kishi
nakeyi, Sai yayi murmushi kawai yaje yazauna, Nasha jinin jikina na wuce daki
sumuy sumuy kamar munafuka, Bayan kamar awa uku sai gashi yashigo dakina naji
tsoro sosai, Yazo daf dani yazauna ya sunkuyar dakanshi yacemin zaki'iya zama
dani zainab.? Araina nace miya kawo wannan tambayar? Kinyi shiru ina tambayarki
zaki iya zama dani ko yaya?? Nanma ba amsa ba, Ya d'ago kai ya dubeni yace,
Zainab arayuwarki na cutar dake fiye da tunanin duk wani makhluqi, Zainab
banta6a son wata ya maceba sai akanki, Tun kina yar shekara tara na nemi
mahaifinki ya bani aurenki kuma ya amince inda na fara ganinki kinje wani gida
kina talla sai wasu yara suka qwace miki cinikin da kikayi duka suka gudu kina
kuka na hadu dake natambayeki kikamin bayanin yanda akayi na biya kudin nakuma
rakaki har qofar gidanku idan zaki iya tunawa, Wllhy tun lokacin Allah ya
dasamin sonki azuciyana nagayawa babanki yace yamun alqawari zai bani ke da
yake lokacin ina boarding school nakoma makaranta duk abokaina sun san sunanki
har naqare karatu naje university ina university Kullum sai inzo da mota inyi
parking inda kuke tsayawa talla inyi ta kallonki har ki saida waranki har nazo
nafara sayen waran ina cewa kiyi sadaka amma darana daya baki ganni ba bakiga
fuskataba lokacinda naga kinfara tasawa nayi tsoron kar wani ya kwaceminke nayi
magana da iyayena dagyar suka amince kuma nagayamusu yanda nashirya za'a
dauramin aure dakene dan kar wani ya gwacemin ke nacewa babanki ki riqa saka
hijab hadda niqab kuma duk suka amince da hakan akan zanje wani..... Kukasance
tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 14 AURE KO ZAMAN GIDA 14 Na Hauwa M. Jabo
…Course idan nadawo saiki tare Kullum kina raina amma nayiwa iyayena alqawarin
saina qare karatu zanyi maganarki, A iran na hadu da maryam maryam tanunamin
qauna ta gaskiya tun kafin muyi aure muke harka da ita kuma banta6a ganinta da
alamar cewa tanada saurayiba nandanan nayi maganar aurenta ba musu aka amince
dan dad dinta abokin dad dinane sosai, Ban ta6a son maryam ba saidai sha'awar
ta da nakeyi saboda ta iya duk wata kissa da mace zatayi taja hankalin namiji
matuqar yanada lafiya, Tanada abubuwan da nakeso ajikin mace wato nonuwa Kullum
su suke rudani ajikin maryam sam ba ita nakesoba, Ta haifi Mustafa Allah ya
dauramin son yaronnan har nake ganin idan bashi bazan iya rayuwa ba inason
mustafa sosai lokackin nasami kaina kamar baniba, Sam ban damu dakeba sam ban
damu da inji labarinkiba kullum daga maryam sai yaronta mustafa nima ina
mamakin kaina sosai da yanda na cutar dake bayan aurenki na auri maryam amma
maryam bata qaunarki mustafa yayi wani ciwo aka kaishi asibiti Dr yace damuwar
mahaifiyarsa ce ta shafeshi kuma idan bamuyi hankaliba zan iya rasa mustafa nan
dana hankalina ya tashi na rude ina tambayarta miyake damunta nan tace ita sai
na sakeke nagaya mata bazan iyaba dataga ba nasara sai tace in mata alqawarin
bazan kula dakeba matsawar tana da rayuwa Wannan ne na amince dashi dan gudun
6acin ranta ya shafi mustafa nadaina kulaki. Tun daganan nadaina kulaki duk dan
mustafa yasamu lafiya amma ina shan azabar rashinki sosai sai gashi wacce na
cutar na wulaqanta itace tazo ta fitarda rayuwata daga hadari ta ceceni zainab
kiyafeni pls wllhy nayi danasanin abinda na aikata muki Kullum damuwar hakan ke
sakani damuwa inasonki sosai zainab amma na cutar dake ya fashe da kuka mai ban
tausayi wllhy hauwa jabo bansan lokacinda na rungumeshi ba ta baya ina
rarrashinsaba lokacin na gama wayewa duk wani makirci na mata na iyashi duk a
tv na iyasu wani channel (muharati zandagi) Rayuwar aurecekawai da zama da
iyayen miji ake koyarwa, Duk wani rarrashin miji da tsokano mishi sha'awa na
iyasu a lokacin, Na juyo dashi na lashe masa hawayensa na daura hannuna akansa
cike da mur mushi nace masa duk abinda kamun na yafemaka nima ka yafemin tun
daga ranar muka shirya da abudl azeez, Kinji tarihin rayuwata hauwa jabo,
Hmmmmmmmm.. Kinyi mantuwa zainab bamu qareba baki gayamin first night dinki ba,
hahaha ke hauwa jabo miye naki aciki tarihinane kuma na baki, Kiyi haquri ki
qarasa min kinsan zee khalifa idan na bata labarin bawannan bayanin bazataji
dadinsaba, Dan nasan tafison nan da ko ina, hahahaha, Owk zan fadamiki ne
saboda namesake dina amma bari muyi sallah ko jabo...? Kukasance tare dani a
AURE KO ZAMAN GIDA part 15 ♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA 15 Na Hauwa M. Jabo …Bayan mun
qare sallah mukaci abinci taci gaba da bani labari, Ingayamiki jabo ranar tare
muka kwana da abdul amma ba abinda yamun, Mun kwana biyu da shiryawa ranar na
uku ina bacci sai na farka ashe mutumin naki idonsa biyuu daganandai aka raya
sunnai Tun taga ranar muka shirya da mijina sai Kinga yanda muke rayuwa dashi
gwanin ban shi'awa yana bani muhimmanci fiye da tunaninki jabo, Duk wata al'ada
ta Iranian ita yake mun dan kuwa duk inda zamuje shi yake daukarmin jaka shi
yake daukan beby kuma yana riqe da hannuna, Wllhy hauwa jabo nikaina banason
yanda yakemun kinga nan Nigeria idan akaga mijinki yana miki hidima sai ace kin
mallakeshi yazama mijin hajiya alhalin ba haka bane so da soyayyah ne ya haifar
da haka, To ina kika iya Turkish?? Kai hauwa jabo akwai son labari to honeymoon
mukajeyi Turkey achan na iya tukish, Gaskiya labarinki yamun dadi sosai zainb,
Muna zaune sai ga mijin yashigo inaga baisan cewa akwai baqi agidanba taje da
gudu ta rungumeshi yafara kissing din bakinta ina kallo hannunsa na murza
basawanta ahankali bashiri nayi gyaran murya, Sai yasauke hannunsa akan
basawanta ya juyo yace baquwa mukayi nace eh sannu dai jabo nace yauwa, Zainab
tace nabata labarin wahallada ka banine kaida uwar yayanka taga ya lumshe ido
yace yazanyi son maryam dina ya rufemin ido banaji bana gani sai ita a really
miss u my mery.!! Tuni naga ta chanza fuska na tabbatarda kishine yake damunta
tajuya zata tafi yabi banyanta da gudu yana dariya nakai 30mnt ni hauwa jabo
ina jiran sufito amma shiru sun mayar dani kwalin taba nadauki yar wayata
naqara gaba amma naji haushi sun manta dani Lallai yau naga aya, Inama ace
nice.. Laifin dadi qarewa Hauwa Muhammad jabo take muku sai wata rana sai mun
hadu a sabon littafi mai suna qarin jini
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment