© ZAINUDDEEN JIBRIL (ZAINUDDEEN ZAIN)
08034840276
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin halittu, wanda
yakeda mulki cikakke kuma mabuwayi a mulkin, salati marar adadi na yo, wurin
mijin Khadija Manzon karshe, wanda muke fatan gobe kiyama mu shige a inuwar
cetonsa, na hada da sahabbai nasa zarata hadi da iyalan gidansa da duk wanda ya
bi turbarsu ya zuwa ranar tsayuwa.
Wannan takardar na rubuta ta ne, saboda tambaya da wata baiwar Allah ta
yi a group na Zain’s villa a kan whatsapp, da cewa, “me ye matakan mallakar
miji”? kamar yadda na alkawaranta mata, na kalato wasu muhimman abubuwa guda
goma wadanda da ikon Allah idan aka kiyaye su zama zai daure a gidan aure, a
kuma ribaci ladar da auren ya tanada. Amma ba wai yana nuna cewa wadannan
abubuwan da na kalato su kadai ne sinadarai da za su gyara ko kawo armashi a
auratayya ba, saboda rashin lokaci da kuma karancin ilimi irin nawu, su na sami
kyalla idanuwana a kai. Ina rokon Allah da yayi mani jagora ya kuma bani ladar
da ke ciki, ya sa duk wanda ya karanta ya amfana mu kuma yi tarayya a lada. Duk
wanda yaga gyara a taimaka ayi ga lambata nan a sama.
Ga abubuwan da na fitar kamar haka:
1. GIRKI
2. TAUSAYI
3. TSAFTA
4. KWALLIYA
5. MU’AMALA
(MUSAMMAN DA DANGINSA)
6. TSARIN
KWANCIYA
7. IYA
MAGANA
8. KARE
MASA MUTUNCINSA
9. RIKE
SIRRINSA
10. GIRMAMA
SHI
1. GIRKI
Girki yana daya daga cikin
abubuwan da ke kawo daurewar aure, duk in da mutum ya kai ba shakka dole sai
yana sakawa cikinsa abinci, ba wai cin abinci ne kuma babban abu mai muhimmanci
ba, abin da ya fi kyau a lura da shi, shi ne, me aka dafa? Sai kaga wata ga
kyawu ga ilimi ga diri (mashaAllah) amma idan ta dafa abinci ba zai ciwu ba, ki
lura fa mijinki ya tafi kasuwa idan dan kasuwa ne, ko ya dawo daga office a
yunwace, sai kika kawo mashi abincin da sam ba dandano, in gayamaki duk haushin
da ya kwaso a office ko kasuwar a kanki zai saukar, haraka ce ta din-din-din
‘yaruwa yanada kyawu ki daure ki koyi girki, iyaye hakkinku ne ku tabbatar
diyanku sun goge ssosai a girki, tun daga girke-girken gargajiya har na zamani,
2. TAUSAYI
Daga cikin sinadaran rike miji
da tabbatar aure, akwai tausayi, ana so mace ta kasance mai tausayin mijinta,
tausayi anan shi ne, kar ta kasance komai ta gani tace dole sai ya siya mata,
kar ta kasance ba abin da ke ranta irin mijinta ya bata kudinsa a kanta, an fi
so idan da hali ma ki dan dinga taimaka masa a cefane, sosai zai ji kin kwanta
a ransa, ba kullum bani-bani ba.
3. TSAFTA
Tsafta ba sai an tsaya dogon
bayani ba abu ce da ke kara dankon soyayya ko shakuwa ba ma tsakanin ma’aurata
ba, har zamantakewa ta yau da kullum, amma fa kar mu dauka cewa tsafta ita ce
muyi wanka mu zo mu shafa mai da turare mu dinga yiwa maigida fari da idanu,
hatta tsara komai na gida in da ya dace tsafta ce, misali maigida ya dawo ya
tarar da takalmi kan gadon kwanciya, ko baki sun shigo gida tareda maigida sai
ga kamfanki (pant) a kan kujera, wannan ba tsafta ba ce sam koda kuwa kin fi
kowa iya wanka da saka tufafi, Allah ya bamu ikon kiyayewa. Kada maigida ya kusanceki
ya dinga jin doyi, zai ji gaba daya kin fita ranshi.
4. KWALLIYA
Bayan tsafta ana so mace ta
kasance ta iya kwalliya, kwalliya kuwa ta hada da kalar tufafin da ya dace ki
saka a kowanne yanayi, da kalar jagira, ja lebe, zungura kumatu da sauran
abubuwa da kun fi ni sanin su, kada azo da dare kan gado a ganki da lesi wai
sunan kwalliya kika sha, ko wadanmi tufafi ko kwaliiya da inda ake yin su, haka
ki kula da kalar kwalliyar da ta fi birge shi ko kalar daurin dankwali da
sauransu.
5. MU’AMALA
(MUSAMMAN DA DANGINSA)
Yanada kyau mace ta kasance
ta iya mu’amala kala-kala, dangin miji da kike gani suna taka rawar gani sosai
wurin daurewa ko katsewar aure, idan suna yabonki a gabanshi dole yaji kina
kwanta masa, idan kuwa sukarki suke yi, tun ba ya dauka har yazo ya fara dauka,
yanada kyau ki kiyaye nagartacciyar mu’amala tsakaninki da dangin mijinki.
Allah yasa mu dace.
6. TSARIN
KWANCIYA
Ba shakka matan hausawa a
wannan gabar anyi musu zarra, mun dauka kunya wai ana nunata ne a ko’ina, ko
kusa komai yanada muhallinsa, a wurin mijinki ki kasance marar kunya indai a
gun kwanciya ne, hakan zai sa a ransa ko wata ya gani a waje tayi fitar fitsara
ke zai tuna, abin bakin ciki sai ka ji Bahausa wai na gadarar ita wallahi sai
mijinta ya sha wuya kafin ya sami kanta, ko azo kwanciyar anayiwa maigida izza
da isa, wannan a musulunce haramun ne, kuma tsanarki ce kawai kike haifarwa a
zuciyarsa, domin namiji idan har ya bukaci matarsa ta hana ko ta ja rai ba zai
taba mantawa ko yafewa ba (a halin wasu). Yanada kyawu ayi karatu na Islama mai
zurfi, za’a sami wadataccen ilimi ta wannan fuskar, idan har yara sun yi aure
iyaye a daure cikin hikima a dinga fahimtar da su muhimmancin iya kwanciya,
domin rashinsa ne ke haddasa fitinar zinace-zinace tun daga mazajen auren har
su matan, domin idan basu gamsu ba sai kuma su koma neman yara kanana a waje,
wai anyi ba’ayi ba kenan.
7. IYA
MAGANA
Iya magana shima babban
gishiri ne da ke kawo daurewar aure, ya kamata mace tasan kalar kalamai da
zatayi amfani da su a kowanne yanayi, idan daga wurin aiki ya dawo ko kasuwa ko
gona ya kamata tasan kalaman da zata tarye shi da su, haka a lokacin da ya dau
zafi ya kamata tasan yadda zata kwantar masa da hankali, domin mace wata ni’ima
ce da ubangiji yayiwa mazaje , mata na dauke da baiwa amma sun kasa tsayawa
suyi amfani da baiwar, duk yadda namiji ya dau zafi kinada kalamai da
kwarkwasar da dole ya sauko. Ki gwada.
8. KARE
MASA MUTUNCINSA
Wannan ya hada da tsare mashi
kanki, yadda ba za kiyi tarayya da wani ba sai shi, ba za kiyi kwalliyar jan
hankali ki fita karnukan titi na shinshinar ki ba sai shi kadai, yadda dadadan
kalamnki shi kada zai sauraresu, kallon satar zuciya shi kadai za ki yi wa.
9. RIKE
SIRRINSA
Mata da yawa suna
faduwa a wannan matakin, sai kaga wata marar albarka hatta kalar kwanciyar da
sukayi da mijinta sai ta zo ta bayyanawa kawayenta, idan mijinta raggo ne ko
jarumi duka kawayenta sun sani, idan naira dari yayi mata cefane da ita duk
makota sai sun sani, idan sau biyu suka ci abinci sai kowa ya ji. Haba ‘yaruwa
kowa fa da karfin da Allah yayi masa, rike sirri yanada kyawu sosai musamman
tsakanin ma’aurata kuma yana sa mijinki yaji ba wata sai ke.
10. GIRMAMA SHI
Yanada kyau mace ta kasance
maigirmama mijinta, dama ko a addinance ana so ne ke ki dauke shi a matsayin
yaya shi kuma ya dauke ki a matsayin abokiyarsa, yayi maki wasa ke kuma ki
dinga girmamashi. Allah yasa mu dace.
ZAINUDDEEN ZAIN
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment