Sajna:
■■■ BAZAWARA(THE WIDOW)■■■
©MISS HAFCY ®NWA ■ TAK'AITACEN LABARI■
Yau ta
kasance Laraba ta bawa rannar samu, gashi kuwa gari yayi kyau sosaii sakamakon
ruwan sama da'aka idar a yammacin yaran, gari yayi sharrr gwanin sha'awa, a
cikin wani madaidacin gida, wata matashiyar mace tana zaune a wani d'an
madaidaicin d'aki, gefenta kuwa yaro ne dabe wuce shekara shekara d'aya ba,
yana kwance akan katifa yana bacci ita kuwa tayi tagumi ta fad'a duniyar
tunani. Wata dattijuwar mata ta shigo d'akin fuskarta sam ba alamar fara'a, ta
kalle ta tace " ke BAZAWARA in kinga dama ga abincinku can a d'akin girkin
kije ki d'auka ki ci,kuma ko da wasa kar kizo kina neman k'ari domin umarni ne
daga babanki abincin da'ake baki da a dinga raba shi a biyu, ana baki kaso
d'aya, kina dai jina ko BAZAWARA?" wadda aka kira da Bazawarar ta sunkuyar
da kai sannan tace " Iya dan Allah dan annabi idan bazaki kirani da sunana
ba, to gwanda kice min "KE" amma dan Allah ina rok'onki da ki dena
cemin BAZAWARA" Iya ta juyo da mamaki " iyeh lallai yarinyar nan
wuyanki ya isa yanka ni kike fad'awa wannan maganar?" Cikin sanyayar murya
tace " Iya kinsan a iya zamana dake ina miki biyayya, daidai da ranna
d'aya ban tab'a sab'a miki ba, wannan ma dan naga abin yayi yawa ne kuma bana
san suna ko kad'an shiyasa na miki magana amma ki yafe ni" ganin an bud'e
kofa an shigo Iya ta fashe da kuka " yanzu yarinyar nan duk irin abinda
nake miki sakayar da zakimin kenan? Ni zaki kalla ki zaga? Na shiga uku yau ni
Indo" Mutumin daya shigo ya k'araso da sauri " lafiya Indo kike kuka
meya faru?" Iya ta k'ara fashewa da kuka " yanzu Mal duk irin
k'ok'arin dana ke akan yarinyar nan ni zata kala ta zaga?" Malam yace
" zagi?!" Ta share hawayenta "kwarai kuwa" Malam yace
" lalllai lokaci yayi da zan fara dukanki a gidanan(ya kalli Iya) samo min
bulala, Iya da sauri ta shiga ta d'auko ta mik'a masa ita kuwa BAZAWARA ba
abinda take sai kuka,ya shigo d'akin ya shiga lafta mata bulalar tana kuka,
tana bashi hak'uri amma sam be kulata ba, ihuntane yasa yaron ya farka, ya
tashi shima ya k'ank'ameta yana kuka, a zatona Mallam ze dena dukanta amma da
mamaki sai naga ya cigaba da lafta musu bulallar ita da yaron sai kuka suke suna
ihu, sai daya musu akala guda goma sannan ya fito daga d'akin yana huci "
'mutuniyar banza kawai, kina zaton da kin kashe aurenki kin fito hakan zesa na
saurara miki, to duk sanda makamancin haka ya sake faruwa ko ma wanda be kaishi
ba saina miki yafi haka, mutuniyar banza kawai, ya fita ya fara lallashin Iya.
Ita kuwa tana kuka tana rarashinta yaronta ta duba hannuwansa duk sunyi shatin
bulala ta sake fashewa da kuka shima kuwa kukan yake abun tausayi, tashi tayi
ta goya shi tana jijiga shi ko zeyi shiru amma sam yak'i ta bankad'a akwatinta
tana duba wani abu kona wasa ne da zesa yayi shiru, can ta hango alawa lolipop
da murnanta ta sako shi ta bashi aikuwa abinka da yaro sai yayi tsit ya cigaba
da shan alawarsa hakan ya bata damar sake maida shi baya be dad'e ba kuwa yayi
bacci ya barta nan tana ta sharbar kukanta, bayanta duk yayi rud'u-rud'u yayi
ja abinka da farin mutum, ga zafin bulala da ya isheta, ganin yaron yayi nisa a
bacci ta sauko shi ta rungume shi tana hawaye "ina sonka d'ana, kai kad'ai
ne me share min kukana, nasan kai kad'ai ne bazaka guje ni ba, Allah ya raya
min kai MUHSIN, ta kwantar da shi ta share hawayenta sannan ta tashi ta nufi
kitchen domin ta kauda yunwar data addabeta, futowar ta keda wuya sukayi karo
wata budurwa, ai kuwa budurwar ta juyo cike da fushi ta wanka mata mari, "
ke har kin isa ki bangajeni na kyaleki dan kina tak'ama kin girme ni, to
wallahi kika kuma bangaje ni sai na miki fiye da haka, banza BAZAWARA kawai,
taje ta kaso aurenta zata zo ta dami mutane mtsw" Bazawara ta juyo cike da
fushi ta.......... DEDICATED TO ALL MUSLIMS WIDOW'S http://hafcy.mywapblog.com
[4:40pm, 3/21/2016] Sajna: ■■ BAZAWARA■■ ©MISS HAFCY ®NWA ■ TAK'AITACEN LABARI■
`2` Ta wanka mata mari ji kake tas! " hak'urina ya kai mak'ura na gaji,
BILKI kar ki manta fa ke k'anwata ce na girmeki , amma zaki d'auki hannu ki
mare ni? To ki sani shiru-shiru ba wasa bane gudun magana ne , dan haka ki
kiyaye," tana gama fad'an haka ta wuce kitchen ta d'auko abincinta sannan
ta koma d'akinta, tabar Bilki tsaye tana mamaki dan bata tab'a zaton zata tanka
mata ba, balle har ta rama. Tayi kwafa sannan tace " Allah ya taimakeki
Iya bata nan da sai kin gane kuranki, woooo BAZAWARA kawai " ta shige
d'aki tana zage-zage. ■ASALIN LABARI■ Malam Ahmad Muneer,shine sunan mahaifin
NUSAIBA BAZAWARA, d'an kasuwa ne wanda yake saida atamfofi a kasuwar kwari dake
kano, yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado, Asalin iyayensu fulanin adamawa
ne amma shi a kano aka haife shi a nan ya tashi. Matarsa ta farko itace BINTA,
sunyi auren soyayya na saurayi da budurwa, sun zauna tsahon shekara biyar ba
haihuwa ,sannan Binta ta haifa masa d'a namiji lafiyaye aka sam mai suna
MUNEER, bayan shekara biyar(5) ta sake haifa masa yarinya kyakyawa aka samata
NUSAIBA, daganan kuma sai haihuwar ta tsaya, suna zaune cikin rufin asiri
kwatsam Malam Ahmad ya k'ara aure ,ya auro wata hatsabibiyar mace mai suna
INDO, cikin shekara uku(3) ta haifa masa "yaya mata guda biyu babbar me
suna FALMATA,wadda a yanzu haka tana can Jigawa tana aure, sai kuma auta BILKI
wadda ita budurwa ce ko auren fari bata yi ba. Tun bayan haihuwar 'yayan Indo
sai ta shiga kula mak'ircin yadda zata raba Malam da Binta saboda taga Malam
yafi san Binta kuma d'ad'in d'ad'awa gata itace mahaifiyar tilon d'ansa namiji
wanda yake ji dashi, dan haka ta shiga wajen bokaye da malamai dan su raba
auren, watarana kuwa kwatsam sai Mal ya saki Binta, ya kuma ce karta sake ko da
wasa ta tafan mai da 'yayansa, haka tana kuka suna kuka, ta rabu da su ta koma
gidansu, cikin ikon Allah tana gama iddar ta, ta sami wani Alhaji dake aiki a
Lagos ya aure ta , yanzu haka tana Lagos da zama hadda yaranta suna zaune cikin
kwanciyar hankali. Gida ya rage sai Indo kawai ,sai abinda tace za'ayi Malam
kuwa ko kara ta saka tace kar ya tsalake to ko kusa da karan baze zo ba , balle
har ya tsalaka shi, Muneer da Nusaiba kuwa sun zamo kamar wasu bayinta, sune yi
mata wanki ita da 'yarta Bilki, sune shara, wanke- wanke, aike, kai da komai ma
na gidan, girki ne kawai bata barinsu suyi. Malam kuwa ko k'ala baya iya cewa don
dama ta riga tasa boka ya rufe masa baki. Muneer ya kamala karatun sakandire a
dadafe, cikin ikon Allah ya samu gurbun karatu a ABU ZARIA inda ze karanci
Medicine, murna a wajensa ba'a magana,amma in ya tuna ze tafi ya bar k'anwarsa
cikin wani hali duk sai yaji ba d'adi, cikin ikon Allah kuwa Malam ya biya
komai da komai, Muneer ya tafi makaranta, ba'a san ransa ba, dan yana hangen
irin wahalar da k'anwarsa zata sha bayan baya nan, domin wani lokacin in yaga
aiki ya mata yawa shine ke tayata suyi su gama, Nusaiba ma tasha kuka da kyar
ya lallasheta tare da yimata nasihar ta dinga addu'a sannan tasa hak'uri a
zuciyarta domin wataran sai labari kuma mahakurci mawadacu ne, bayan tafiyarsa
Nusaiba a gida kullum cikin wahala take aiki kuwa haka take yinsa kamar jaka
bata hutawa sam, sai lokacin kwanciya, wani sa'in abincima gagarata yake ta
zamo abin tausayi ga uwar rama datake yi. Sannu bata hana zuwa har Muneer ya
kamala karatunsa na Medicine ya fito da sakamako me kyau, ita kuma Nusaiba tana
aji na hud'u a makarantar sakandire (Ss1) kuma tana da shekara goma sha
biyar(15) duk da karatun a dadafe ta keyinsa kullum cikin makara da fashi dan
ma tana da k'ok'ari. Muneer kuwa nan da nan ya sami aiki ya fara samun kud'i,
indai kuwa ya sami kud'i ko nawa ne a gida hud'u yake rabi shi, kaso d'aya ya
kaiwa mahaifiyarsa( duk da tana auren mai halin amma hakan be hanasa bata duk
abinda ya samu ba) kaso na biyu kuma ya bawa Malam domin yayi cefene da saurarn
abubuwa, kaso na uku kuma ya siya k'anwarsa Nusaiba kayyayki dama duk wani abu
datake buk'ata, sauran kuma ya rik'e, haka yake a kodayaushe, hakan ba k'aramin
k'onawa Iya rai yake ba, hakan yasa ta shiga kula tugun makirci ta yadda zata
dawo da Muneer tafin hannunta ya zamo ita ke juya shi sai abinda tace, hakan
kuwa akayi ta kashe kud'i masu yawa kan asirin nan yayi don har gonarta ta gado
ta siyar takaiwa boko kud'in domin yayi aiki, cikin k'ank'anin lokaci Muneer ya
dawo ba shida wadda yake girmamwa yake bin umarninta kamar Iya, Nusaiba kuwa
duka da tsangwama ta hantara shine ke had'a su, ya zamanto ko biyar bata shiga
tsakaninsu yana ganin Iya zata dinga dukanta tana zaginta tana azabtar da ita
amma bashida ikon cewa komai sai dai ma ya taya Iya fad'an, ko kuma ya tayata
dukan ta, kud'i kuwa duk albashinsa akan Iya da 'yayanta Bilki da Falmata yake
k'arewa, Nusaiba kuwa kullum haka take cikin kunci babu mai taimaka mata
abincin ma wani sa'in gagarata yake sauk'inta d'aya in taje makaranta
k'awayenta dayake sunsan halin datake ciki suna taimaka mata, kuma suna d'ebe mata
kewa, Muneer kuwa ya zama d'an Iya na k'arfi da yaji mahaifiyarsa ma ya manta
da ita, Iya kuwa dama tuni ta raba Binta da Nusaiba. A da Binta takan aikowa da
Nusaiba kaya, kayan kawalliya da d'an kud'i amma dagabaya sai ta dena
kwata-kwata, Nusaiba kuwa tun tana damuwa har ta dena. `3` Nusaiba ta taso
yarinya kyakyawa kuma ga farin jinin samari amma duk da haka bata kula kowa duk
wanda yazo mata da zancen soyayya ce masa take yayi hak'uri karatu zatayi aure
ba yanzu ba, sab'anin Bilki duk da k'aracin shekarunta gata yarinya ce bata isa
budurwa ba a lokacin, hakan be hanta kula ko wani kolon saurayi ba, ko yace
yana santa ko bayaso, yara wani sa'in har ihu suke mata suna mata wak'a "
ta maza, ta maza, mai wasa da maza karya" amma tak'i denawa. Nusaiba fara ce
mai madaidaicin tsahon tana da manya idanuwana, sai bakinta d'an madaidaici,
bata da hanci sosaii amma hancinta mai kyau ne, tana da gashinta dai-dai
misali,kyakyawa ce dai Masha Allah. Nusaiba bata da wani buri a rayuwarta daya
wuce ta zama Lawyer hakan yasa take k'ok'ari a makaranta bata wuce ta d'aya a
position, ta maida hankalinta zuwa karatunta, duk wannan halin data shiga amma
sam baya hanata karatunta ba. Watarana Kausar k'awar Nusaiba ta kawo mata
ziyara suna d'aki suna hira, sai suka fara hirar wata k'awarsu da'aka cire aka
mata aure, Nusaiba tace " ai ni insha Allahu sai na shiga jami'a na fara
karantar Law na tabbatar da cewa zan yi kuma mijina ze barni na cigaba sannan
zanyi aure, domin ni yanzu banida wani buri daya wuce naga na zama Lawyer kuma
kullum cikin addu'a nake akan Allah ya cika min burina, Amin" Kausar tace
" Allah ya cika miki burin ki k'awata ni kam kinga banda matsala nasan duk
tsiya sai na kamala sakandire, in ma za'a min aure, kuma wanda za'a aura min
insha Allahu ze barni nayi karatu, dan nima kinsan burina be wuce na zama
ma'aikaciyar Lab ba", Nusaiba tace " to Allah ya cika mana
burukanmu" Kausar tace " Amin" Duk wannan hirar da suke a kunne
Iya tana kofa ta kasa kunne tana sauraronsu,suka cigaba da hirarsu ta
makaranta, kana Kausar ta mata salama ta tafi. Iya ta koma d'akinta tayi kwafa
sannan a zuciyarta tace " dama abinda nake san ji kenan, da yardar Allah
yarinyar nan na kusa aurar dake kuma jahili zan aura miki in yaso naga ta yadda
za'ayi ki cika burin naki, ja'irara yarinya tanaso ta b'ata min
pilas(plan)" ta d'an yi jim tana tunani sannan tace " yarinyar nan ta
Sa'idu mai walda ta dace!
Http://hafcy.mywapblog.com
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment