BIKIN VALENTINE BY ZAINUDDEEN JIBRIL


BIKIN   VALENTINE

© ZAINUDDEEN JIBRIL ZAIN (DR. ZAIN)

Gabatarwa


         Bukin soyayya ɗaya ne daga cikin bukukuwan zindiƙai a ƙasar Roma, fiye da ƙarnoni sha bakwai (17 centuries) da suka wuce. Daga ciki akwai cewa; ‘Romulus’ wanda shi ya kafa Roma, wai macen kyarkeci (she wolf) ta tsotse shi, wanda ya yi sanadiyyar zamansa Jarumi mai Hikima. Wanda ya sa ‘yan Roma suke bukin wannan taƙddamar da ta faru a duk tsakiyar Febreru (February). Daga cikin ababen da ake aikatawa cikin bukin, akwai, za a yanka kare da akuya sai a sami ƙarti majiya ƙarfi su shafe jikinsu da dabbobin da aka yanka, sai su wanke jinin da madara. Sai su dinga yawo cikin gari ko a zindir ko kusan hakan, su nutsa wani yanki na fatar waɗannan dabbobin sai su dinga bugawa mata a fuska da cewar wata shekara matan ko da juya ne to zasu haihu.
          A lokacin da kiristoci  suka ɗauki wannan bikin suka fara yin sa a 14 ga watan Febreru malamansu sun tsawata kan wannan mummunar al’adar wadda suka ce tana ɓata tarbiyyar maza da mata.
         An hana wannan bikin a Italy, sai daga baya a ƙarni na sha takwas  da na sha tara (18th -19th century) a ka mayar da bikin.
         Abin mamaki musulmi da yake da kykkyawan addini ya kuma mallaki yanda ake soyayya daga karantarwar fiyayyen halitta, sai ga shi ya fara aiwatar da wannan bikin. Abin lura a nan shi ne asalin wannan bikin wato valentine daga marasa addini ne (pagans) waɗanda sunayi ne don girmama gumakansu.
         Don haka ba shakka duk wanda yayi wannan bikin ya ba da gudummuwa ne wajen girmama gumaka.

Inda ta fito

          Ka kalli wannan bikin a matsayin wanda aka kashe shekaru da dama a garuruwan turai, sai daga baya aka raya shi a Biritaniya da Amurka, cikin sauri ya zagaye ƙasashen musulmai.
            Tambaya a nan ita ce, waye valentine? Me yasa ake yin bikin wannan ranar?       
Bikin wannan ranar ya fara ne tun ƙarni na huɗu  kafin haihuwar annabi Isah (A.S), anayin bikin ne don girmama ubangijin Romawa ‘Lupercus’.
           Abin da ke jan hankalin mutane a wannan bikin shi ne yanda ake raba mata tsakanin mazaje don suyi lalata har zuwa wata shekara, (kamar yanda muka anbata a gabatarwa), za’a bada mace ɗaya ga waɗannan ƙartin mazajen da suka shafe jikinsu da jinin kare da akuya, za su bugesu a gefen kunce wai don su sami haihuwa zuwa wata shekara. Bayan mazajen sun ɗaukesu sunyi lalata ta kwana ɗaya ko shekara ko tsawon rayuwarsu.
           Kiristoci sun yi yunƙurin su canja wannan biki, amma abin ya ci tura, Nasara ɗaya suka samu ita ce, ta canja sunan bikin daga ‘Lupercalia’ zuwa ‘valentine day’ a shekara 496 CE, wanda shugaban kiristoci na wannan lokacin ‘pope Gelasius’ ya yi.
           Duk da cewa kiristocin sun so su canja yadda bikin ke tafiya daga raba ‘yan matan zuwa kwaikwayar halayyar malaman kiristoci. Amma sam wannan ya ci tura.
           A shekara ta 1776 gwamnatin faransa ta hana wannan bikin a ƙasarta, haka su Italy da Austria da Hungary da Germany, haka abubuwan da ke gudana a bikin suka ɓata tsawon shekaru.
            A kiristance, a kwai tarihin valentine har sama da hamsin, duk da cewa guda biyu sun fi zama sanannu a idon duniya.
            A shekarar 1660 charles 2 ya raya wannan bikin, ya sabuntar da shi cikin sabuwar duniya ya kuma mayar da shi hanyar samun kuɗi ta hanyar sayar da katutukkan valentine.
            Esther A. Howland ita ce ta fara yin katin valentine na farko a duniya  ta sanyawa katutukkan suna ‘what else’
            Valentine wani malamin kiristoci ne wanda ya ƙare rayuwarsa a gidan kurkuku, inda ya kamu da soyayyar diyar wanda ya saka shi a gidan yarin.
            Duk da cewa a yau ana so a mayar da abin na kiristanci, har yau abubuwan da ake aikatawa a bikin za su koma ne ga abin da zindiƙai suke aikatawa a asalin wannan bikin.
            Da yawa mutane ba su san cewa coci ta yi faɗa da wannan bikin ba, da ta gaza ne sai ta canja mashi suna da zimmar wai ta ɓatar da shi, sai dai kash, da mowa da bora duk ubansu ɗaya, ko da kalar jikinsu ta ban banta.



Asalin valentine daga zindiƙai


             Farkon wannan bikin ya samo asali ne daga Romawa kafin shigar kiristoci a cikinsu, lokacin da zindiƙai suke yin bikin ‘feast of the wolf’ a Febreru, kuma suna kiran bikin ‘feast of Lupercalia’ don girmama uwargijiyarsu ‘Februata Jona’ wai ita ce ‘goddess of women and marriage’ (uwargijiyar mata da aure), haka suna yi domin girmama ubangijinsu ‘pan’ (allahn Romawa na yanayi) ‘god of nature’
               A wannan ranar, mata zasu saka sunayensu cikin wani abin zuba ruwa ko kwano, wanda maza zasu zo su zaɓa domin ganin wa ye zasu sadu da shi (zina) a wannan yinin ko tsawon wannan shekarar, wani lokaci har tsawon rayukansu.
               waɗannan mutanen biyu zasu yi musanyar kyauta tsakaninsu, da zimmar nuna ƙauna.Wani lokacin sukan yi aure.


Shigar kiristanci cikin bikin


                Lokacin da kiristanci ya shiga  ƙasar Roma, ya yi yunƙurin canja wannan bikin da abin da ya fi dacewa da karantarwarsa. Kiristoci da yawa sai suka yanke zasu yi amfani da 14 ga watan Febreru don cimma yunƙurinsu, wannan ya faru ne lokacin da babban bishop na Italy wato valentine aka kama shi saboda yana aurar da sojojin sarkin Romawa a ɓoye, a lokacin sarki Claudius2 a shekara 270.
                A lokacin Claudius 2 ya hana sojojinsa da suyi aure, a cewarsa sojan da ba shi da aure, ya fi mayar da hankalinsa wurin yaƙi saɓanin sojan da ke da aure.
                Ya so valentine ya fita addinin kiristanci ya kuma daina aurar da sojojin, amma sam ya faufaye, sanadiyyar haka ya fiile masa kai a 14 ga watan Febreru shekara ta 270.
               Idan ka duba Encyclopedia akwai labarum valentine har guda uku, waɗanda dukansu, kiristoci ne, waɗanda sun yi shahada (a kiristance) a 14 Febreru. ɗayan shi ne muka kawo a sama, na biyu shi ne bishop of Interamma sai na uku daga Africa.
               Sai a shekara 496 pope Gelasius ya canja Febreru 15 bikin lupercalia zuwa Febreru 14 bikin valentine, don a kiristantar da bikin.
               Hutun wannan bikin ya zama sananne a Amurka a 1800’s lokacin ‘civil war’
               Haka pope Gelasius ya canja zaɓar matan da ake yi a bikin na zindiƙai. Maimakon mazan su zaɓi matan don aiwatar da masha’a, sai ya mayar da bikin, za’a saka sunayen malaman kiristoci cikin kwano, sai mutane su zo su ɗauka, duk sunan malamin da ka ɗauka za ka kwaikwayi halayyarsa har ƙarshen shekara.
               Amma idan muka kalli yanda valentine ke tafiya a wannan zamanin tuni wannan ya zama tarihi da aka bizne a juji.


Mahangar musulunci


                Ya zama tilas ga musulmi ya nisanci duk wani mummunan aika-aika daga ɗabi’un zindiƙai, musulmi ba ya buƙatar ya yi biki saboda mutuwar wani babban kirista, haka musulunci bai aminta da soyayyar sharholiya ba kafin aure.
               Soyayya tsakanin ma’aurata da iyali ba wai a rana ɗaya za’ayi bikin ta ba, mafi muni ma bikin da ke da asalin arna da kiristoci.
               Musulunci shi kaɗai ne addinin da bai bar komai ba face sai da ya yi bayaninsa , soyayya da yadda ake yinta da inda ake yinta, yana cunkushe cikin karantarwa fiyayyen halitta Muhammad (SAW)
              A Qur’anance, a sunnance, a Ijma’ance, wannan bikin haramun ne.
              Ba shakka yin bikin yana jawo soyayya tsakanin musulmi da kafiri, wanda ko wannan haramun ne.
     Allah ya kiyaye.




Kammalawa


            14 ga watan Febreru wanda aka sani da valentine’s day, wani yanki ne na shekara wanda ake jinginawa da soyyya da holewa, wannan ranar an mayar da ita ranar raba katutukka na valentine da raba kyaututukka tsakanin maza da mata, kamar su teddy bears, da jajayen filawowi da sauransu, a jami’o’I har party ake haɗawa domin nuna murnar zagayowar wannan ranar.
            Sau da yawa da za ka binciki masu wannan aikin, abinda za su gaya maka shi ne wannan ranar murna ce kawai, ba wani haramun da muke aikatawa cikin ranar.
            A mahangar musulunci valentine, ba dai-dai ba ne, ga hujjoji kaɗan gudun kada mu tsawaita.
1.     Tana ingiza mutane zuwa aikata zina. Qur’ani ya hane mu da kusantar duk abinda zai iya kaimu ga aikata zina 17:34
2.     Bikin valentine daga al’adun marasa addini ne. hoton wannan da ke jikin valentine card (cupid) yana zaman matsayin Venus ne. venus shi ne Roman god of love and beauty ubangijin Romawa na soyayya da kyawu. Annabi Muhammad (SAW) ya umurce mu mu saɓawa yahudawa da nasara balle marasa addini.
3.     Kwaikwayon abu, idan ba umarnin Allah ko manzonsa ba ne, ba ya halarta a musulunci.
4.     Al-mubazzaranci a Qur’anance da Sunnance haramun ne. a wannan ranar ana ɓannar kuɗaɗe wurin sayen gifts haka ana ɓarnar lokaci.
5.     A wannan ranar ana yin party a cakuɗe tsakanin maza da mata, a sha giya ayi zinace-zinace, wanda duka haramun ne a musulunci.

Zaiuddeen Jibril Zain (Dr. Zain)
08034840276

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment