Ina Amfanin Karfin-Gwiwa?


Ina Amfanin Karfin-Gwiwa?
-Farfesa Salisu A. Yakasai
Sau da yawa, mutane kan dauki karfin-gwiwa a matsayin wani ma’auni da ake bukata a lokacin da ake cikin tsananin damuwa ko tashin hankali. Wato kamar dai a lokutan yaki ko kuma aukuwar wata annoba ko ibtila’i (jarrabawa). To amma kuma a gaskiya lamarin ya wuce haka, hasali ma batun ya wuce yadda muke tunani. Kai lamarin karfin-gwiwa wani alheri ne na yau da kullum. Ashe kenan karfin-gwiwa ba ma kawai daya ne daga cikin alhaire-alhaire ba, sai dai a ce alheri ne da dan’Adam yake tare da shi a muhalli da yanayin da ya dace. Abu ne mawuyaci ka aiwatar da wani abu na alheri ba tare da samun karfin-gwiwa ba, saboda mutumin da yake damfare da karfin-gwiwa ba ya da-na-sani a rayuwarsa. Wannan shi ne alkiblar tattaunawarmu ta yau.
A duk lokacin da na yi tunanin mutanen da karansu ya kai tsaiko a rayuwa (wato mutanen da karfin-gwiwarsu ya yi tasiri sosai a rayuwarsa), to mutum guda tilo da kan fado mani shi ne Wingston Churchill. Tun yana yaro karami ya shaki iskar samun daukaka a rayuwa. A lokacin da kuma yake makaranta, yakan amsa fatawoyin abokanan karatunsa game da makomar duniya. Ga misali, Churchill yakan ce yana hasashen duniya za ta samu kanta cikin canje-canje daban-daban da suka danganci tashin hankali da gwagwarmaya da kuma yake-yake. Ya ma taba fada karara cewa London za ta shiga mawuyacin hali, kuma za a kai mata farmaki, shi kuma zai samu daukaka a yunkurinsa na kare martabar London.
Wannan buri cikin gudummawar da zai bayar domin gina kansa da kuma al’ummarsa ba karami ba ne. Bayan faduwar kasashen turai a hannun ‘yan-nazi, sai da Ingila ta ci gashin-kai har na tsawon shekara biyu a karkashin jagorancin Churchill. A fili ya kalubalanci Hitler cikin goyon bayan al’ummarsa, duk kuwa da irin barazanar da suka fuskanta ta jefa bama-bamai da kuma mamaya. A shekarun alif dari tara da talatin kafin yaki, Ingila ba su da wata dabara face ta farantawa Hitler, amma kuma a fili Churchill ya kalubalanci hakan. A shekarun alif dari tara da arba’in kuwa, a lokacin da aka tunbuke shugaba Chumberain daga ofis, sai Ingila ta nemi wani jagora nagari domin ya maye gurbinsa. Mutumin da ya dace ya dace ya dare mulkin shi ne Halifad, to amma sanin cewa ba shi da karsashin da zai jagoranci Ingila a yaki sai ya hakura. Nan take sai aka kira Churchill domin cike gurbin.
To amma kuma don me aka zabo Churchill ya zamo shugaba? Shin don me mutane ke ganin ya dace da ya jagoranci kasar da take ganin karshenta ya zo? Ya dai riga ya samu karbuwa a tsawon shekaru da suka gabata, saboda haka an gwada karfin-gwiwarsa a lokuta daban-daban, kuma sakamakon hakan ne ya tabbatar da himma da kwazonsa da kuma jajircewarsa. Dangane da burin yin fice a rayuwa kuwa, tun a lokacin da yake dan makaranta ya kasance dan gwagarmaya da son samun nasara a dukkan abin da ya sa a gaba.  Daga nan kuma sai ya shiga aikin soja, ya kuma sami nakaltar makamar aikin sosai da sosai. Babban burin da ya dade a birnin zuciyarsa shi ne zama dan siyasa kamar yadda mahaifinsa ya yi, to amma da farko burinsa shi ne ya yi fice a aikin soja. Hakan kuwa aka yi domin babu matsayin da bai hau ba a cikin kayan sarki.
Duk abin da zai aiwatar, yakan tunasar da kansa cewa “Na kuduri niyyar yin wannan aiki iyakar yina, idan ban samu nasara ba, to da alama ba zan kuma samun nasara a kowane aiki ba”. Wannan wata hikima ce ta kara samun kwarin-gwiwa a cikin ruhi da jiki duka. Ta hakan ne kuma cikin jajircewarsa a dukkan lamuran da ya sa gaba, ya yi samun nasara har karansa ya kai tsaiko. Wannan ne ma dalilin da ya sa yakan tunasar da kansa cewa “Na fi damuwa da burin yin suna cikin kwarin-gwiwa fiye da komai a duniya”.
Daga baya ne ya bar aikin soja kuma ya shiga kogin siyasa. A nan din ma dai, haka ya yi ta fadi-tashi (yau nasara kuma gobe faduwa), har dai lokacin da ya zamo shugaba a shekara ta alif dari tara da arba’in. A nan ne kuma mutane suka san cewa ba su yi zaben tumun-dare ba. Wato suna da yakini dangane da irin himma da kwazo da kuma jajircewarsa. Hasali ma, rayuwarsa kacokan ya salladar da ita ga burin da ke cikin zuciyarsa, kuma karsashinsa ya tabbatar da nasararsa.
Gaskiyar maganar ita ce, daga na gaba ake gane zurfin ruwa, wato dai akwai abubuwa da yawa na izina da za mu amfana da su daga tarihin rayuwar wannan bawan Allah. A tattaunawarmu ta gaba, za mu yi kokarin gano dalilan da suka mutum kamar ni da kai da ita da su zamu bukaci karfin-gwiwa!    
08035073537, 08154615357 (Tes kawai)   Syakasai2002@yahoo.com

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment