WANI HANIN 1
© *MISS HAFCY*
*TAK'AITACEN LABARI*
NOTE: WANNAN LABARIN K'AGAGEN LABARI NE NAYI SHINE BADAN KOMAI BA SAI DAI IN FADAKAR DA AL'UMMA BANYI SHI DAN CIN ZARAFIN WANI/WATA BA ALLAH YASA ZAMU AMFANA DA WANNAN D'AN TAKAITACEN LITTAFIN NAWA, SANNAN INA BAWA MASOYA LITTAFIN
*DALILIN SO* HAKURI SABODA NA DAKATAR DASHI ZUWA WANI D'AN LOKACI NAGODE.
★★★★★★
Da yammacin rannar Alhamis gari yayi kyau gwanin sha'awa dayake yanayin damina ne, anyi ruwa sai gari yayi Sanyi ga wata ni'imtaciyar iska dake k'adawa me d'adin gaske ina zaune a d'an madaidaicin falon mu nayi tagumi ina kallon abincin dake gabana shinkafa da wake ce da mai da yaji hadda salad ga jelar kifi a gefe, na tsurawa abincin ido ina ta tunanin rayuwata, Mahaifiyata ce ta fito daga d'akin dake had'e falon namu, takai minti d'aya tana kallona cike da tausayi sannan tace " Yanzu 'yar nan wai bazaki dena wannan tunane tunanen ba? Kibar komai ga Allah yana kallanki kuma ze kawo mana mafita, dubi yadda duk kika rame, dan Allah ki dena wannan damuwar ko so kike hawan jinin ki ya tashi ne?" Na runtse idona hawayen danake ta boyewa karsu fito suka kwararo na kalli Mama nace " Mama dole na damu, ni kadai nasan irin abinda nake fuskanta, ina cikin mawuyacin hali Mama" Mama tasa hannu ta share min hawayena " yu hakuri 'yar nan yanzu dai kici abincin kinji" nace toh sannan na fara cin abincin a hankali ina matsar kwala.Da daddare ina zaune akan doguwar kujera ina muraji'ar Alkur'ani yayin da Mama ke zaune akan sallaya tana addu'oi, Ji mukai an shigo falon bako salama, Mama ta d'ago ta kalli wanda ya shigo din wanda yake kawuna ne k'anin mahaifina, tace " Ahh kawu kaine tafe kuma ba salama?" Harara ya dala mata sannan yace " ke malama saurara min, ina ruwanki in nayi salama ko ban yi ba?" Na d'ago na kallehi " Ina wuni Kawu?" Ya dala min harara sannan yace " ni ban ma san dame zan kira kiba, ke dai kin wuce a kiraki da budurwa kuma ke ba aure kika tab'a yi ba balle na ce miki matar aure ko kuma in kin tab'a aure na kira ki da bazawara, kodayake nasan tuni kika gama zubda mutunciki a waje dan bazai tab'a yiwuwa ba ace mai kamar shekarunki har yanzu bata san waye namiji ba!" Mama cike da fushi ta daka masa tsawa " *Ado*! Ya isa haka ya isa nace, yanzu kai ko kunya bakaji ba, ace yarka wadda a haife zaka haifeta kuma 'yar yayanka dakake bi uwa d'aya uba d'a kake fad'awa
wannan kalamar marasa dadin ji, ka ci amanar yayanka wallahi kuma Allah se ya saka masa" nikuwa tun daga jin kalaman Kawu na sunkuyar dakaina ina ta sharara kukana. Kawu ya kalli Mama shima a fusace yace "ke dai kika sani, kuma dama nazo na sanar dake ne gobe insha Allah bayan Sallar juma'a zan sanar a massalaci ga duk wanda kesan wannan 'yar taki yazo ya samemi zan bada ita *AUREN SADAKA* kowa ma ya huta! Ko kunaso ko bakwa so! Yana gama fad'an haka fuuu ya fita daga gida, yayin da nikuma na sake fashewa da kuka, Mama kuwa kasa magana tayi shiru kawai tayi tana kwalar bakin ciki.
Ta taso ta dafa ni tace " kiyi hak'uri 'yar nan komai yayi zafi maganinsa Allah, inaso kisa a ranki wannan abinda kawunki ke kokarin yi shine mafi alheri a wajenmu kin tuna fa
*WANI HANIN GA ALLAH BAIWA NE* sai kiga shi yayi da niyyar ya cutar dake sai Allah ya tura masa anniyarsa ke ya zamo mafi alheri a wajenki, inason ki toshe kunnuwanki daga maganganun mutane ki yarda wannan itace *K'addarki* Allah yana nan tare dake 'yata ki cire komai a ranki addu'a ya kamata kiyi domin itace *makamun mumuni* Kalaman Mama sune suka kwantar min da hankali nayi murmushi wanda na dade banyi ba domin ko ada in nayi murmushi sai dai ya zamo na yak'e, godewa Allah nayi daya bani uwa kamar Mama, d'aya tamkar da dubu wadda samin uwa kamarta sai an tona( kamar Mamana♥) Na kalli Mama nace " Insha Allahu Mamana nagode kwarai a kullum ina godewa Allah daya bani uwa kamarki, Insha Allahu na dena sa komai arai kuma a shirye nake na karbi kowani namiji da Kawu ya kawomin a matsayin Mijina, na yadda cewa *WANI HANIN GA ALLAH BAIWA NE*! *KUBIYONI*
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment