MA’ANAR ILIMI



MA’ANAR ILIMI
Ilimi shi ne; Sanin abu a bisa hakikaninsa, sani na yanke ba na shakka ba, ko rudu. (Wikipedia, 2018) za mu iya bawa ilimi ma’ana da cewa “Ilimi shine sanin wani abu wanda baka san shi ba”.
Shi ilmi wata irin baiwa ce da Allah Ya ke bayarwa ga bayinSa. Hakika ilmi ya na tabbatuwa acikin kwakwalwar dan Adam. Mutum mai Ilmi ya sha banban da jahili ta kowacce fuska, saboda mai ilmi yana aiki ne ko barin aiki a sakamakon umarnin da ilminsa zai bashi, wato dai ilmin zai kasance tamkar shi ne linzamin dake jan ragamar hankalinsa da al'amuransa.
Lallai ilmi fitila ne dake haskaka Rayuwa. Duk mutumin da bashi da ilmi to hakika zakaga rayuwarsa acikin kunci take.
ILIMI A MAHANGAR MUSULUNCI
Annabi (S.A.W.) ya ce: "Neman ilimi wajibi ne a kan dukkan musulmi da musulma". Saboda haka ya kamata mu tashi tsaye wajen neman ilmi. Don haka matukar mutum yana raye neman ilimi a gare shi ba ya karewa na addini ko na zaman duniya domin cin ma wasu bukatu na rayuwa, kamar su sanin kimiyya ko fasaha da makamantan su.
"An karbo Hadisi daga Anas dan Malik Allah ya yarda da shi ya ce: "Na ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: Mai neman ilimi shi ne mai neman rahama, kuma neman ilimi yana daga cikin rukunan musulunci" (Dailami ne ya Ruwaito).
Wannan Hadisi yana nuna mana cewa rahama ba ta samuwa sai an samu ilimin nemanta a duniya, kuma shi kansa musulunci ba ya yiwuwa ga mutum sai yana da ilimin bautar Allah. Haka ita kuma rayuwa takan tafi a hagungunce ne ga jahili wanda ba shi da ilimin sanin yadda duniya da lahira ta dosa da kuma yadda za'a sami zama lafiya a nan duniya da Ranar gobe kiyama. (Al-kanawi, 2015)
ILIMI DA TARBIYA
Ilimi da tarbiya abubuwa ne guda biyu da daya baya tafiya sai da daya. Ilimi al’amuri ne mai girma da matsayi da daukaka, kuma shine ginshikin rayuwa da yake kai mutum ga kyakkyawar rayuwa da samun cikan kamala. Hakika mutum wani halitta ne da ke bukatar ilimi a fagen rayuwarsa kuma sakamakon kyakkyawan ilimi  zai iya kai wa ga babban matsayi na tsarkakan ruhi da yalwan ilimi a rayuwarsa ta duniya da lahirarsa. Hakika tun daga yarantar mutum har zuwa girmansa da kuma zuwa karshen rayuwarsa yana rayuwa ne a kan matakai masu bibiyar juna kuma a tsawon matakan rayuwarsa yana da damar kai wa ga mataki madaukaki, kamala da cika. (Porstoday, 2015)
A cikin wannan bayani da zan gabatar zan yi kokarin bijiro da muhimman neman Ilimi ne musamman a mahangar addinin Musulunci.
A fili yake cewa ilimi abu ne mai matukar muhimmanci da daukaka a rayuwar mutum musamman daga lokacin yaranta zuwa lokacin samartaka, kuma wadannan matakai biyu na yaranta da samartaka suna kunshe da tarin matsaloli na musamman, sakamakon haka tarbiyya da ilimantarwa suna da matakai, kuma kowane mataki yana da nashi matsayi da muhimmanci na musamman.
Tarbiyya a ma’anarta ta lugga tana nufin karuwa, girma da habaka a kan tafarkin da ake bukata, ko kan tafarki mai kima. Yayin da neman ilimi hanya ce da take kai mutum ga samun tarbiyya da kyakkyawan sakamakon rayuwa. Don haka a fili yake cewa neman ilimi da samun tarbiyya sune shimfida kuma ginshikai da suke kai ga inganta rayuwar bil-Adama tare da taimaka masa wajen cimma burin rayuwarsa na kai wa ga matsayin cika da kamala da ake bukata.
Hakika duk wata halitta da take kan doron kasa tana da kebantacciyar hanyarta ta kai wa ga cikan halitta da aka kebe mata, kuma wannan ita ce manufar samar da ita a fagen rayuwa. Don haka manufar neman ilimi a rayuwar mutum ita ce kokarin samun saukin kai wa ga cikan halitta da daukaka da aka kaddara masa a fagen rayuwa, kuma mutum yana matsayin khalifan Allah ne a kan doron kasa.
Allah Madaukaki a cikin Suratul-Baqara a aya ta 30 yana fayyace mana cewa: “Kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce ga Mala’iku; hakika Ni mai sanya wani wakili ne a kan bayan kasa, sai suka ce; Shin zaka sanya wanda zai yi barna a kanta kuma ya zubar da jini alhalin mu muna maka tasbihi da godiya tare da tsarkake ka, sai (Allah) ya ce lallai Ni na san abin da ba ku sani ba”. Hakika dan Adam ba kawai halitta ba ne da zai iya zama mai tarbiyya, a’a halitta ne da yake bukatar samun ilimi da tarbiyya. Tabbas bukatar dan Adam ga ilimi da tarbiyya a rayuwa; bukata ce mai girma, kuma da zarar ya rasa wannan albarka a rayuwarsa, to tabbas ya yi hasarar babbar dama mai kima da take matsayin fitila mai haskaka hanya gare shi.
Sakamakon haka duk mutumin da ya rasa ilimi a rayuwarsa, to babu makawa zai zame ya rasa gishirin zaman rayuwar duniya kuma rayuwarsa zata zame ta dogara da sauran mutane.
Immanuel Kant masanin ilimin falsafa dan kasar Jamus da ya rayu a karni na goma sha takwas yana da imanin cewa: “Batun ilimi da tarbiyya al’amura ne biyu masu girman muhimmanci a rayuwa, kuma sune mafiya matsala da suke addabar mutum a fagen rayuwa”. Har ila yau Kant yana da akidar cewa: “Daga cikin kirkirar mutum akwai samar da daula da tsarin gudanarwa da kuma tsarin neman ilimi da tarbiyya, amma wadannan abubuwa sun fi zama matsala a gare shi a kan sauran al’amura”.
A bisa dabi’ar duk wani mutum kafin girmansa, dole ne sai ya kai ga wasu matakai masu muhimmanci a rayuwarsa na cikar hankali da kamala. A yau sabon ilimi da ake kira da “Ilimin halayyar dan Adam mai zurfi” yana dauke da bangarori daban daban misalin ilimin sanin girman jiki, zamantakewa, sanin halayya, ruhi da dabi’a, jin kai, harshe da sauransu.
A mahangar masana ilimin halayyar dan Adam, matakin tarbiyya yana fara wa ne tun daga lokacin da aka haifi jariri, kuma haka tarbiyyar zata ci gaba a matakan rayuwar dan Adam daban daban. A misali Jean Piaget masanin ilimin halayyar dan Adam dan kasar Faransa yana cewa: Bunkasar ilimin mutum ta rabu zuwa matakai hudu ne, kuma ta kan zo karshe ne da zarar mutum ya cika shekaru goma sha shida a duniya”. Shi ma Erik Erikson masanin ilimin halayyar dan Adam dan kasar Amurka yana cewa: “Fadada da zurfin hankalin mutum da ke rayuwa a tsakanin al’umma tun daga haihuwarsa har zuwa karshen rayuwarsa ya rabu zuwa mataki takwas ne”. A takaice dai masana ilimin halayyar dan Adam sun kasa matakan tarbiyyar mutum zuwa matakai takwas kamar haka:-
1.      Kafin haihuwar mutum wato tun daga lokacin farkon samuwarsa a cikin mahaifa a lokacin da yake maniyi a cikin mahaifiyarsa har zuwa lokacin haihuwarsa.
2.      Lokacin da yake jariri har zuwa cikan shekaru shida.
3.      Lokacin yaranta daga shekaru shida zuwa shekaru goma sha biyu.
4.      Matashi daga shekaru goma sha biyu zuwa shekaru ashirin.
5.      Samarta daga shekaru ashirin zuwa talatin.
6.      Tsaka-tsakar shekaru daga talatin zuwa shekara hamsin.
7.      Matakin cikan hankali daga shekaru hamsin zuwa shekaru sittin da biyar.
8.      Tsufar mutum daga shekara sittin da biyar zuwa sama.
Har ila yau masana ilimin zamantakewa sun yin maganganu masu muhimmanci dangane da ilimi da tarbiyar dan Adam. A bisa mahangar masana ilimin zamantakewa: Tarbiyya hanya ce da ta gare ta al’umma zasu kai ga inganta lafiyar jikinsu da na ruhinsu, kuma har su kai ga yin tasiri ga al’ummun da zasu zo a bayansu. A fili yake cewa kowace al’umma tana kokarin ganin duk wadanda zasu zo a bayanta sun dauki irin salon tarbiyya da tunanin da ta tafi a kai. Sannan iyalai suna daga cikin tushen tarbiyya a tsakanin al’umma. Haka nan mafi yawan manazarta suna bada muhimmanci ga tushen tarbiyya a tsakanin iyali misali mahaifa musamman ma mahaifiya.

HANYOYIN SAMUN ILIMI

  • Iyaye: Hanya ta farko: Iyaye; Ana fara samun ilimin farko ne daga iyaye, musamman Mahaifiya. Daga gare ta ne mutum yake fara koyar abubuwa iri-iri. Kamar su cin abinci, sanya tufafi, tarbiyyar rayuwa, tsafta da sauransu. Da taimakon mahaifi kuma yaro ya ke samun Juriya, Dogaro da Kai, Nagarta da kuma tabbatuwa a kan turba ta gari.
  • Dandali: Hanya ta biyu: Itace Dandali ko kuma muce wuraren wasan yara. Ananne yaro yake koyon gane wadansu mutane daban da na gidan su. Kuma a nanne yaro yake koyon wasanni da koyon zama da jama'a daban.
  • Makaranta: Hanya ta uku: Makaranta; Daga hannun Iyaye kuma, sai makaranta. A nan mutum ya ke koyon ilimin Addini da Duniya. A Makarantar ne za a koyawa mutum ilimi daban-daban, tun daga Firamare zuwa Sakandire, har zuwa Jami'ah. A nan a ke samun shedar karatu babba da karramawa da samun daraja wanda akan ne za a iya samun hanyar da za a cimma ribar rayuwa.
·         Bincike: Bincike bincike hanya ce tasamu ilimi a wannan zamani da ba kamarta.
NAU’UKAN NEMAN ILIMI
Muna da nau’ukan neman ilimi guda uku kamar yadda masana suka tsara.
  • Ilimin Addini
  • Ilimin Zamani (boko)
  • Ilimin Gargajiya
REFERENCES
Wikipedia, (2018): Ilmi https://ha.wikipedia.org/wiki/Ilmi
Ibrahim M. Inuwa Al-Kanawi (2015): Muhimmancin Neman Ilimi a Musulunci https://web.facebook.com/voahausa/posts/muhimmancin-neman-ilimi-a-musulunci/10153204380208499/?_rdc=1&_rdr
Porstoday (2016): Muhimmancin Ilimi da tarbiyyar Yara da Matasa http://parstoday.com/ha/radio/programs-i412-muhimmancin_ilimi_da_tarbiyyar_yara_da_matasa

Mr. Nasir (2012) Ilimi Shine Gishirin Rayuwar Al’umma http://mrnasir.blogspot.com/2012/11/ilimi-shine-gishrin-rayuwar-al-umma.html

 (2018) Muhimmancin Neman Ilimi ga Mumini a Addinin Musulunci https://alummata.com/blog/muhimmancin-neman-ilimi-ga-mumini-a-addinin-musulunci/

5 comments:

  1. Men we ýanýoldaşym 8 ýyl bile ýaşaýarys, indi iki çagamyz bar we baky ýaşamak üçin ýüregimiz birleşdi, bagtly maşgala öýümiz bar, ýöne bir wepaly gün daşary çykdy we öýüne gaýdyp gelende bagtly görünmedi, men bu barada oýlanýardy we meseläniň nämedigini bilmäge synanyşýardy, ýöne ol hiç zat aýtmakdan ýüz öwürdi we şol gün maňa bolan söýgüsi azaldy we aýrylyşmagyny isledi, ýöne men boýun towlaýaryn we mundan beýläk bile ýaşamaýarys, şonuň üçin durmuş we çagalar üçin aňsat däldi. . bir gün öýe gaýdyp barýarkam, bir gowy dostum bilen tanyşdym, ol adamsy hakda sorady, oňa geň galdyryjy zatlary düşündirdim, indi adamsymy yzyna alaryn öýdüp gorkma, maňa Dr Aýaýy hakda gürrüň berdi Maşgala meselesinde oňa kömek eden we maňa habarlaşmak üçin maňa beren güýçli jadygöý ussady, ýöne men onuň bilen habarlaşmaga şübhelenýärdim, bir wepaly Dr Dr Ajaýi bilen habarlaşmaga synanyşmagy makul bildim. Meselämi oňa düşündirdim, ol problemanyň nireden gelýändigini we nikamda täzeden düzelmek üçin edilmeli zatlaryň bardygyny aýtdy, maňa söýgi jadysyny berdi we üç günüň içinde adamym maňa jaň etdi we ötünç sorady. başyna gelenini bilemok we öýüne gaýdyp barýar, şol günden şu güne çenli öý hojalygym söýgi we rahatlyk bilen doldurylýar, ähli minnetdarlyk güýçli jadygöý doktor Ajaýä gidýär. Haýsydyr bir mesele bilen ýüzbe-ýüz bolsaňyz we çalt çözgüt isleseňiz, Dr Ajaýi bu iş üçin dogry adamdyr. Aragatnaşyklar E-poçta: drajayi1990@gmail.com ýa-da Whatsapp / Viber belgisi: +2347084887094

    ReplyDelete
  2. Masha Allah hakika wannan bayanikan ilmi yanada matukar muhimmanci, Allah yasakada alkhairi maassalam.

    ReplyDelete
  3. Masha Allah hakika na karu da wann ilimi mai albarka, Allah ya bamu ikon neman ilimi mai albarka

    ReplyDelete
  4. Wannan am'anar ta ilimi ta gamsar Dani sosai.

    ReplyDelete
  5. Allah yasaka da alkhairi

    ReplyDelete

Thank You for Your Comment