Mujallar Masoya: Soyayya - Shamsuddeen Ibrahim Fatimiyya

SOYAYYA
Soyayya, tushen jin daxin rayuwa ce, sannan soyayya rayuwace ta jin daxi da annashuwa da kuma fahimtar juna. Yanda matuqar mahimmanci masoya su san cewa ita rayuwar soyayya wata irin rayuwace mai tattare da kulawa a koda yaushe idan har ya kasance masoya basa kula da rayuwar juna nan su to soyayyar zata dinga samun bayyanar matsaloli sosai. Amman idan masoya na kula da hakkin soyayyarsu to zasu kasance masu jin daxin yafiyar da soyayayyar su cikin sauki.

IRE-IREN SOYAYYA
Soyayya dai guda xayace amman yanayi kansa ta canza salo ta zama wata iri ta daban. Soyayya ta yaudara Soyayya ta gaskiya Soyayya ta sha'awa Waxannnan sune vangarorin da soyayya ta rarraba kuma dukaninsu suna gudana cikin duniyar masoya. Ka wadata zuciyata da soyayya Koda yake wasu daga cikin masoya za su so suji cikakken bayani gamsasshe dan gane da waxannan nau'oi na soyayya. Masoyiya ce
SOYAYYA TA YAUDARA
Wannan soyayya ce mai jirwaye da kamar wanka. Yaudara aduk inda take to bata da wani amfani domin kuwa zaka samu karya, ha’inci, zamba, cutarwa duk a cikin wannan soyayyar ta yaudara. Masoyi za ya zo yanuna maka gaskiyarsa a fuska amman a zuciya ba haka abin yake ba, akowane lokaci zaya bayyanar da qaryarsa gareka sannan kuma yaso ka aminta da shi a matsayin ya ambaci gaskiya. Masoyi xan yaudara yanada wahala ganewa, to saidai alokacin da qarya tayi yawa, alokacin ne kuma gaskiya zata yi halinta na bayyana.
SOYAYYA TA GASKIYA
Soyayya gaskiya, soyaya ce ta mu samman, wace akanyita da zuciya xaya kuma tsakani da Allah. Ita wannan soyyya itace soyayyar da mnasoya kanyi juriya gami da hakuri a duk yanayin da suka samu kansu ciki. Soyayyar gaskiya itace soyayar da masoya kan ba junansu shawara ta gaskiya a cikin dukanin abinda zasu aiwatar. A cikin ita wannan soyayya ta gaskiya zaka samu gaskiya, Riqon Amana, kulawa, kyautatawa,, gami da qoqarin son cikawa juna alqawari.
SOYAYYA TA SHA’AWA
Itace mafi haxari daga cikin jerin soyyaya Soyayyar sha’awa…

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment