HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 15



HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 15



Al’amarin ya taru ya yi ma Farida yawa, tunanin ta cak! Ya tsaya lokacin da taji bayanin inna, kukan ma ta daina yinsa, ya tsaya cak! Dama kuka wuri gareshi, zuciyar ta wani daci take mata, a hankali ta fara ganin jiri, ita kan ta bata san lokacin da ta mike tsaye ba, tsananin rudewa ce ko firgicewa oho, sai kuma ta yanki jiki ta zube kasa.     
  

              Masha Allahu laakuwwata illah billah.
Mu hadu a kashi na biyu don cigaban wannan littafi.
Na gode
Saratu M. Sani Makera
E-mail:saratsmak@yahoo.com

HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 14



HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 14




Farida kam tana tattare da RASH IN SANIN takamaiman inda maganar ta dosa, duk da haka ta razana, ta kidime,ta rude, harma da gigicewa. Jikin ta wani makarkata yake, kada dai ace   ba iyayen ta bane?. Ita kam taga tashin hankali, wani kuka ta saki mai tsuma zuciya, Dad din ya kasa koda motsi wurin da yake balle bakin shi ya iya furta wani abu. Shikam mukhtar hankalin shi ya kara tashi dama yasan hakan zata faru to amma yaso su fahimce shi bayin shi bane shikam haka Allah ya halitta mishi son ta tun tana karamar ta ya dai kasa furta hakan ne gudun irin wannan.
Tunanin farida ya katse lokacin da inna ke cewa, “dama nasan a kwana a tashi hakan zata faru, abin da nake wa gudu kenan, kada azo yarinyar nan ta girma wani cikin zuri’a ta ya kinkima, haba! Mukhtar da hankalin ka, da wayon ka Duk ina kaifin basirar da Allah ya ba ka? Shin ma ina tunanin ka? Ka rasa wacce  zaka ce   kana so duk fadin duniyan nan sai  shegiya. Mukhtar ya runtse idanun shi baya son kalaman nan da inna ke furtawa, “inna ki daina ce  mata shegiya alhali ba shigiya  bace,  , kin san hakan ba kyau” innar wata harara ta yi masa “ai sai ka nuna min iya yenta; yarinyar da aka tsinta zakace  ba shegiya  bace, to gaya min mecece? Yanzu ba wata matsala” inna ta dudi Dad din dake zaune ya rasa abin cewa bai so wannan katobarar da Mukhtar ya yi ba ya na tausayama yarinyar, innar ke cewa “Wallahi Ibrahim duk tausayin da zakaji na yarinyar nan sai ta bar gidan nan yanzunnan bawani abin da zakacemin. Ba yauba na sha gaya maka nifa irin wannan nakewa gudu to yau ga Magana ta.

HUMANITY IN LIFE

HUMANITY IN LIFE
By Sani Alkali

What is humanity? Is the quality of state of being kind and understanding humanity is the best key way of breaking any crisis. It cool hot minds, it eliminate the color of skin, it make difference to be put aside. Humanity is so vital for progressing of any society. No humanity no good leaving. The main reason for publishing the above topic is really disappointed to hear a leader or patriotism citizens make public speech in tribalism manner or prioting one zone to another in my country Nigeria. Allah was created us with different languages, tribe, nation. Because, he want us to interact with one another for our all progress and peace. I want to called attention of majority of our journalist, to stop publishing news which lead to tribalism crisis, their work has significant role in building the nation, if they utilize is correct way,
My honorable reader, did you observed, in Nigeria there is astonish things going on in our journalism professional, for instant in Maiduguri. Any criminal act, news paper will relate it to insurgency, my question. It can happen, they are army robbers. Are they not investigating the report or call the criminal at that location is  insurgent? Secondly, like Benue crisis always, reporters  said is Fulani, but investigation revealed they are not all Fulani, why our journalist divert from NBC guard lines? Is NBC not performing their responsibilities? Just recent statement by the of president of U.S.A  Donald  trump  mentioned  during Nigerian president visit (Muhammad Bukhari), trump call for stopping  killing of Nigerians either politically religiously or tribalism but some Nigerians news paper published that Mr. trump called for stopping killing Nigerian Christians, which is not correct statement of president trump of U.S.A please our journalist, stop following view of enemies of Nigerian progress because of just little and unblessed money.
O humankind was repeated 306 times directly and more than tow thousand times in over 6000 verse in the holy Qur’an, this means Qur’an encourage humanity so being a Muslim, you must have humanity to all your neighbors irrespective of their religion tribe or nation. Let look at the holy Qur’an statement “an pursue not that of which you have no knowledge; for every act of hearing or of seeing or of (feeling the) the heart will be inquired into (on the day of reckoning).
Qur’an 17:36 Oneness of humanity.
The holy books Qur’an give emphasis on the oneness of human being. It highlight us of common human origin and ancestry at quadrant place by saying humans have the same origin in a single soul or cell this suppose to encourage us to make humanity as a way of life so that a lot of Allah’s blessing cover us Allah respect and uplift any human being who practices humanity in his daily activities. The holy Qur’an stated strong emphasis on the dignity of human beings regardless of their gender or race or even status.
I don’t like even during conversation, to show tribalism between your guest, just take him as a human being respect each other, leave in peace and harmony.  Thus the purpose is  to  ensure  that the unity of humanity is never compromised and the differences that exist among people are resolved  through a process of mutual understanding on the basis of  ideas that are divine revealed. Thank you for your time.


HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 13



HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 13




Ganin tadan lallabeta mom din ke shaida ma ta Dad din ta na kira, mikewa tayi tare da Mom din suka nufi sashen dad din. Ta sami wuri ta zauna, dad din ya shiga bata Magana tare da bata hakuri da lallami, ran dad din har yanzu a bace    yake ya tsani abun da zai zo ya tada ma ‘yar sa hankali, duk da haka, ya nuna mata shima ba zai taba yadda ta auri Usman ba. Ta dan cije  lebe Allah sarki, bata so dad din ta ya dauki zafi da yawa ba , hawaye suka tararo mata, cikin tausasa murya take Magana Cewa tabi umurnin sa ta hakura da auren Usman, sam bata son saba ma iyayen ta, tana iya gwargwado don ganin ta faran ta rayukan su. Har yanzu tana son Usman sai dai ta riga tayi alkawali ta hakura da shi don ganin ta yi biyayya ga mahaifin ta tun da hakan shine farin cikin sa. Sai dai taci gaba da du’a’in Allah ya hada ta da miji na gari

Inna ce ta shigo ta same su “au ‘yar ce  aka saka gaba ana lallashi ce  kake karamar yarin ya? Koda yake ba wannan ya kawoni ba.” Ta dan gyara zama “Ibrahim dama Cewa nayi gara inzo da kai na idan ba haka ba, ko yanzu ba tada masa zancen nan na auren sa za kuyi ba, alhali yau ne cikar wa’adin da aka diba masa. Na ga alamar kunfi son ku biye wa yaron nan saboda haka ni yanzu ku kira shi gamu zaune a ji tabakin shi, idan har yanzu Allah bai hore ya hana shi ganin wadda zai aura, mu Allah yahore mana muna da wadda zamu hada.” Tun lokacin da inna ta fara magana ko tari ba wanda ya yi shi dai Dad hakuri ya shiga bata, yana fama da wannan matsalar ta farida ya ma manta ya tuntubi mukhtar ya ji tabakin sa, sai dai baisan ko mukhtar din yana gida ba hakan ya sa ya dauki waya domin ya kira shi. Mom kuwa indai maganar auren mukhtar ce, takan goyi bayan inna, ganin take yaron yana nema ya rena mutane, in dai Dad ne ba ruwan shi, ba inda zai sa kai balle ya damu har ya rika yi mishi fadan auren, saboda Cewar sa ba zaiyi ma ya’yan sa auren dole ba, kan haka baya son takura mishi. Wan da ga sa’annin sa nan sun yi uren wasu har da ya’ya daga mai biyu sai mai uku.
Bangaren mukhtar kuwa tunda safe da yaje office, kasa zama yayi, saboda rashin jin dadin jikin sa da bayayi.
Gida ya dawo idon sa rufe saboda ciwon da zuciyar shi ke yi, yana shiga dakin shi kwanci yayi saman gado bayan ya rufe dakin. A hankali ya rufe idanun shi, nan da nan ya kara shiga wani sabon tunani, ya tuna yaune cikar wa’adin da aka diba masa, ya gama yanke ma kan shi hukun ci a zuciyar sa, lokaci guda tsananin ciwon kai ya taso masa lamarin yabi ya rikece masa, nan kuma ya shiga ganin jiri Allah ya taimakeshi kwance, yake da ba a bin da zai hana shi faduwa.
Bai san irin hukuncin da za suyi ma maganar sa ba, zuciyar shi kamar zata buga yake ji, numfashi yake fitarwa a hankali, duk rigimar da ake ta farida baisan ana yi ba, saboda tsananin ciwo, ya dauko magunguna ya sha, Allah ya taimake shi ya shiga furta addu’o’i, da taimakon Allah kuma ya fara samun saukin ciwon, bacci kuma ya dauke shi.
Bai jima sosai da yin baccin ba kuma ya falka, cikin ikon Allah jikin shi yayi sauki, wanka ya shiga, ya fito, ya shirya tsaf dashi shigar kananin kaya ya yi, kwarjinin na shi ya kara fita. Yana cikin shirin ne wayar shi ta shiga nuna mishi alamar kira, ya sa hannu ya dauki wayar domin ya duba mai kiran na shi bayason a takura mishi, ganin number din Dad yasa ya yi saurin karawa ga kunne. Dad din bai tsaya wata doguwar Magana ba ya shaida masa yana neman shi duk inda yake, bai jira amsar da zai bashi ba ya tsinke layin.
Fitowa ya yi ya nufi kiran da ake masa, ya riga yasan ma’anar kiran nashi, ya same su zaune ya zube kasa hadi da bada gaisuwa , sannan ya gyara zaman shi, lokacin farida ta gaida shi ya amsa gaisuwar cikin fara’a hadi da dan murmushin da ya bayyana gareshi. Inna kam ta katse masa hanzari da cewa, “kai mukhtar ka dube mu nan, kada ka rika yawo da hankalin mu ka maida mu kamar sa’an nin ka, shin ina ka tsaida zancen ka?” Dad din ya kasa cewa koma, yana shirin jin yadda zata kaya  saboda yana kyautata zaton ko yanzu mukhtar bai zo da wata kwakkwarar maganaba don ya san kwanan zancen, ya san ko yan zu cewa zai yi bai tashi ba.
Mom kuwa daka masa tsawa tayi “ya ana maka Magana zaka wani sadda kai ka kyale mutane, ka tashi kaba mutane wuri idan har baka da abin cewa, tunda dama munsan kwanan zancen naka har yanzu maganar ka day ace, baka tashi ba, amma kasan cewa daga  yau ka yadda da auren Sadiyar.” Cikin razana ya dago fuskarshi wadda take sharkaf da hawaye, al’amarin nashi mamaki yake ba su.
Ya dan tausasa murya “don Allah mom ku gafarceni, ku tausaya min  wallahi ina  da wacce   nake son aure, Dad ku tausaya kada kuyi fushi da ni, nima kaina bansan yadda a kayi hakan ya faru ba. Nayi iyakar kokari na don ganin na kawadda wannan a zuciya ta, amma al’amarin dada karuwa yake, hakan yasa na yadda da cewa yin Allah ne ba yina bane. Dad ku iyaye na ne da banda tamkar ku, a duniya, nasan zaku so farin ciki na, kamar yadda zaku ki abinda zai zamo sanadiyyar salwantar rayuta, me yiyuwa idan na rasa farin cikin.” Hawaye keci gaba da tararo mishi yaci gaba da maganar da yake hadi da kara marairai cewa.
 Farida kam tausayin shi ya kamata dama ta raya a ranta cewa duk wannan abun na yayan ta akwai wacce yake hange, sai dai batasan dalilin da ya hanashi bayyana hakan ba, wata kila yana shakkar iyayen na su ko baza su amince da zabin sa bane.itakam bata taba ganin soyayya irin haka ba, kai amma ko wace ceta cira tuta,  yayan yana matukar kaunar ta da yawa cikin zuciyar ta take masa fatan  alheri duk da batasan ko wace  ce  ba amma tasan yayan ta ba zaiyi zaben tumun dare ba, tayi matukar farin ciki. Yadda yake maganar hawaye na zubo mishi ya kara bata tausayi itama bata san lokacin da hawayen suka shiga zubo mata ba, sam ta manta da duk wani bacin rai dake zuciyar ta, ganin yayan ta ya shiga wani hali, kai yaya da daukar lamari da tsawo uhm ...“ tunanin ta ya katse lokacinda Dad ke cewa, “ya isa haka mukhtar ka gaya mana wace   yarinya ce zaka aura? shi kenan mun huta, idan ma duk wannan magiya da kake ka na ganin kamar ba zamu goyi bayan ka ba, ka daina tunanin haka duk wacce   kake so za muyi kokari don ganin ka cimma burin ka kaji ko?” zuciyar shi na tattare da fargaba yak e cewa, “don Allah dad ku yafemin, ku barni in.. in.. auri…. sai kuma ya yi shiru, kayi Magana mana kayi shiru, muna saurarenka, ya danyi jim sannan yaci gaba da maganar tattare da fargaba, don Allah dad ku aura min  FARIDA.

Dad din bai fafimci maganar tashi ba “wace  farida kake nufi?” a hankali ya nuna farida dake zaune kusa dashi. Zumbur Mom din ta mike hadi da bashi wani wawan mari a kunci, Sai kuma ta shiga zubda hawaye ta na cewa, “Mukhtar yanzu abin da zaka saka min kenan? To wallahi baka isa ba bazaka tona mana asiri ba dama abin da kayi nufi kenan tun da wuri kayi saurin canza raayi.

HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 12



HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 12




Bai boye  ma ta ba ya gaya ma ta yadda suka yi da mahaifin shi, tsorace ta kalleshi, jin cewa idan ma ta aure shi ba ita kadai ceba, hawaye suka shiga zubo mata Usman din da ta kallafa rayuwar ta, kenan, wani kishin kuma ya tattaro yake kokarin dunkule zuciyar ta.
A hankali ta shiga yi masa Magana cikin tattausar muryar, wanda tun zuwanta wurin sai yanzu ta iya furta wani abu, “Usman ka daina wannan zance tunda Allah ya riga ya hukun ta niba matar ka bace” Sai da gaban shi ya fadi jin maganar da ta furta, zazzare ido ya yi kamar wani sabon kamun hauka, nan danan kuma wasu sirarrun hawaye suka zubo mishi bai yi zaton zai samu matsala a wurin ta ba, shi dai son na ta na neman azabtar da shi. “Farida ya zaki ce  haka? Don Allah farida kada ki ki ni lokaci daya, ki tallafi rayuwa ta ban....” Dakatar da shi ta yi lokaci daya zuciyar ta wani zafi take mata, saboda raradin kaunar shi dake neman dada karuwa gareta. Ta dan share hawayen da suka zubo ma ta.
Ya rasa dalilin da yasa take kokarin kawo musu hukunci daban a tsakanin su, sai ganin ta yi gwiwa bibiyu ya gurfana yana rokon ta duk kada ita ma tace   ta fasa auren shi. “usman ka dai na gurfana min  bana son irin  haka kai ne babba a gareni bai dace   kayi hakan ba, ta dan yi shiru sai kuma a hankali ta ci gaba, “shin da gaske ne kana kauna ta? Tambayar ta dirar mishi a bazata ya ji ta wani banbarakwai. “ Farida ba sai na gaya miki ba ni kaina ban san tsananin kaunar da na ke miki ba ni ka dai nasan yadda na ke ji” ta ci gaba, “tunda haka ne ka nuna min kaunar da ka ke yimin, ta hanyar yimin alfarma daya, amma sai ka yi alkawarin zaka yimin wannan alfarma.” Ba musu yake cewa, “ki fada farida na yi mikin alkawarin insha’Allahu ko raina ki ke bukata zan sallama miki in dai hakan zai faranta miki rai,” na gode”, tace mishi sannan ta ci gaba da cewa “Usman ba wani abu bane face  ka faranta ran iyayen ka hadi da biyayya ga zabin da suka yi maka, ka karba, ka rika amana hannu bibiyu, hakan ba karamin farin ciki zai sanya musu ba.

Usman nasan har yanzu Baba ba zai so auren nan nawa ba, tsananin tausayayin ka ne yasa ya amince  maka har da ka hada auren mu mu biyu. Ka yi hakuri idan Magana ta tayi maka zafi, ka gafartamin, ba abinda zan so kayi bayan wannan. Usman don Allah kayi wannan biyayyar ka gani, nasan zata zamo maka alheri, a rayuwa. Kasan ita biyayya lokacin da da ya yi ma iyayen sa, kai ko ba iyayen sa bane biyayyar bata faduwa banza. Kasa ce ma ta ko mai ya yi gaskiya ta kara sanya shi cikin wani tashin hankali, jin maganganun ta baya da niyar can za ra’ayi alhali yana matukar son ta. A hankali har yanzu magar tata ke fitowa cikin muryar ta mai dadin sauraro, “Usman” ta kira sunan shi ya dago kai yana kallon ta suka hada ido, bata son suna saurin hada idanu ita kadai tasan yadda hahan  ke haifar mata, ta tausaya mishi amma a ganinta gara a ce sun bi umurnin iyayen su mhm. Ta dan saukar da ajiyar zuciya hadi da dan sunkuyadda kai sannan ta ci gaba da cewa,”nasan duk wannan zaka yi tunanin na daina son ka,” lokacin kuma hawaye suka dan tararo mata bata kula da ta share ba, ta ci gaba da maganar ta “Usman inaa son ka hadi da kaunar ka bazan boye maka ba, usman son ka ya riga yamaye duk wani gurbi da kake zato a zuciya ta, ina  tausayin kaina, Usman ina son ka in kara jaddada maka son da banyi zaton zan sake yima wani da namiji irin sa ba.
Tsananin son da nake maka ne har ya haifarmini da kaunar ka, har nake jin zuciya ta ta yi sallama da duk wata soyayya idan ba taka ba. Ina son duk wani abin da kake so, sai dai kuma bazan taba son abin da zaisa ka bijirewa iyayen ka ba. Hmm saboda haka a ganina ya kama ta mu hadu mu hakura da juna, insha, Allahu wannan zai zamo alheri a garemu da fatar zumuncin mu bazai yanke ba.”? Ita ma kanta tasan karfin hali tayi da ta furta wannan magana don sai da zuciyar ta ta girgiza, tasan abu ne  mai wuya ta iya cire Usman a zuciyar ta, wani dan siririn kuka ta fara yi, ita ma kan ta bata san lokacin da kukan ya zo mata ba, ta riga ta gama Magana ta san kuma shima yanzu yana da maganar yi, amma gudun kada ya lallabe ta da kalaman shi masu ratsa mata zuciyar ta yasa tayi, saurin mikewa tsaye, da sauri ta kama hanyar shiga gida, kiranta yake, amma taki tsayawa bata son biye mishi ta riga ta yanke ma kansu hukun ci a ganin ta hakan zai fi musu.
Ya jima wurin tsaye, ya kasa dagawa da wurin duhu- duhu ya rika gani sai kuma tsananin ciwon kai da ya karu ga reshi, ya rasa inda zai saka kan shi. To wai me yasa zata yanke wannan hukunci alhali yana da tabbacin tana son shi 100%, ya kudiri niyyar shifa ba zai fasa auren ta ba, bai hana idan baya numfashi ba. Haka ya fito dakyar, cikin tsarin Ubangiji ya isa gida lafiya.
Tana shiga gida sashenta ta nufa, kwanci  tayi kan gado tana darzar kuka, nan kuma ta daina kukan ta shiga neman taimakon Ubangiji da ya sa hakan ya zamo mata alheri. Sai dai kam sai wani ikon Allah zai sa ta daina son Usman. Mom din ta ce   ta shigo dakin, ta shiga yi mata nasiha saboda ta samu ta kwantar mata hankali, farida ta dan yi murmushin karfin hali ganin hankalin Mom din ta a tashe, “ba komai mom, wannan duk cikin hukunci ne na Ubangiji.” Mom din ta ji dadi ganin ‘yar ta bata dauki al’amarin da zafi ba, koda yake ta riga ta san ‘yar ta Allah ya riga ya hore mata hakuri, ta shiga sa mata albarka.