HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 14
Farida kam tana tattare da RASH IN SANIN takamaiman inda maganar
ta dosa, duk da haka ta razana, ta kidime,ta rude, harma da gigicewa. Jikin ta
wani makarkata yake, kada dai ace ba iyayen ta bane?. Ita kam taga tashin
hankali, wani kuka ta saki mai tsuma zuciya, Dad din ya kasa koda motsi wurin da
yake balle bakin shi ya iya furta wani abu. Shikam mukhtar hankalin shi ya kara
tashi dama yasan hakan zata faru to amma yaso su fahimce shi bayin shi bane
shikam haka Allah ya halitta mishi son ta tun tana karamar ta ya dai kasa furta
hakan ne gudun irin wannan.
Tunanin farida ya katse
lokacin da inna ke cewa, “dama nasan a kwana a tashi hakan zata faru, abin da
nake wa gudu kenan, kada azo yarinyar nan ta girma wani cikin zuri’a ta ya
kinkima, haba! Mukhtar da hankalin ka, da wayon ka Duk ina kaifin basirar da
Allah ya ba ka? Shin ma ina tunanin ka? Ka rasa wacce zaka ce
kana so duk fadin duniyan nan sai
shegiya. Mukhtar ya runtse idanun shi
baya son kalaman nan da inna ke furtawa, “inna ki daina ce mata shegiya alhali ba shigiya bace, ,
kin san hakan ba kyau” innar wata harara ta yi masa “ai sai ka nuna min iya
yenta; yarinyar da aka tsinta zakace ba
shegiya bace, to gaya min mecece? Yanzu
ba wata matsala” inna ta dudi Dad din dake zaune ya rasa abin cewa bai so
wannan katobarar da Mukhtar ya yi ba ya na tausayama yarinyar, innar ke cewa
“Wallahi Ibrahim duk tausayin da zakaji na yarinyar nan sai ta bar gidan nan
yanzunnan bawani abin da zakacemin. Ba yauba na sha gaya maka nifa irin wannan
nakewa gudu to yau ga Magana ta.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment