GABATARWA
Kwamfuta ta taka muhimmiyar rawa cikin rayuwarmu ta yau da kullum. Bugu da ƙari kwamfuta ta taka rawar gani a harkar sadarwa na yaɗa labarai kamar talabijin, rediyo da kuma jaridu. A halin yanzu mun sami mafi sauƙin hanyar sadarwa. Muna amfani da kwamfuta don mu tura saƙon imel, hira da ƴan uwa da abokan arziki, muna kuma gudanar da bincike a yanar gizo muna amfani da ita wajen tattauna abin da ya shafi harkar ilimi. Amfanin kwamfuta ba a nan kaɗai ya tsaya ba, muna amfani da ita makarantun zamani wajen koyarda ɗalibai, haɓaka tattalin arziki da kuma gudanar da kasuwanci da aikin gwamnati, sayen tikitin jiragen sama, da sauransu.
Abubuwan da sukafi burgeni a wannan harkar ta na’ura mai ƙwaƙwalwa sun haɗa da; a duk lokacin da muke mu’amalantar waɗansu kafafen yaɗa labarai, kamarsu gidajen talabijin, rediyo, jaridu da sauransu,kai tsaye sai mu sami bayanai masu gamsarwa a lokacin da muka ziyarci shafukansu dake kan yanar gizo da kwamfuta.
Wannan littafi mai suna “Kimiyar Na’ura mai ƙwaƙwalwa (Kwamfuta)” shine matattakala ga kimiyar Na’ura mai ƙwaƙwalwaa wannan zamani.Dukkanɓangarorin ilimi suna da alaƙa da harkar kwamfuta.
Wannan kundin, ya ɗauki kaso mafi tsoka wajen ganar da mafi sauƙin hanyar koyar da ɗalibai na kowane ɓangare na ilimi da ka sani.
Na’ura mai ƙwaƙwalwa muhimmiyar abokiyar tafiya ce kuma babbar hanyar gabatarwa ce don cimma nasara ga ilimin kimiya.
Sharahbil Muh’d Sani
10th June, 2015
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment