HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 10
*** *** ***
Usman ya dawo gida, bayan ya
fito daga office, ba wani jimawa ba duka duka idan ya yi minti arba’in da dawo wa,
Baban nashi ya kira shi.
Ya nufi kiran da ake mishi,
ya sami iyayen na shi, cikin nuna alamar biyayya ya sami wuri ya zauna.
Alh umar ya dan yi gyaran
murya ya fara yi mi shi Magana, da farko nasiha ya rika yi mishi, usman kam ya
rasa inda maganganun suka dosa. Alh ya ci gaba “Usman ka yadda da yin Allah
komai na duniya yakan tsara shi ta yadda ya so ko ba haka ba? Usman ya ce,
“haka ne Baba” “yawwa” Alh yace, da shi sannan ya ci gaba “Usman karnar yadda
nasan ka tun farko kai da ne mai biyayya da kuma bin umurnin, na gaba da kai
wanda nake fata ka dore da hakan har illa ma sha Allah.
Usman ba wani abu ba ne face auren
nan na ka, gaskiya yanzu zan so ka janye maganar auren nan na ka, na san
yarinyar da kake nema yarinya ce, mai
mutun ci, da kamun kai. Wanda hakan aka samu banban ci a wurin mahaifin ta, bai
dauki mutum da daraja ba, kai ma kan ka zaka so a ce sirikin ka na tattare da
dabi’u na gari. Mutane da dama sun san ya’yan Alh Ibrahim, suna da halayyar kirki,
wasu har mamaki suke yi basu yo halin mahaifin su ba ko kadan.
Gaskiya nayi nadamar barin
ka har maganar auren nan tayi nisa, yarinyar ta cancanta, sai dai gaskiya
halayyar mahaifinta bata yimin ba ko kadan, Usman ka nemi aure gidan mutun ci
wayan da kuma suka san darajar dan Adam zai fi mutun ci, ni kai na zan samu
kwanciyar hankali. Saboda haka maganar aure kai da Farida babu ita daga yau.
Kan haka naga ya dace in hada ka da diyar aminina Alh Abubakar, kuma har nagama
Magana da shi, kai ma kanka ka sani mutum ne mai daraja ga jama’a , ya’yan sa
shima gwargwado sun sami tarbiya ta gari. Saboda haka na riga na zaba maka mata
da yau, dama hakkin iyaye ne auren fari su zaba ya’yan su, imba yanzu da zamani
ya canzaba.
Duk maganar da Alhajin keyi
ba wadda Usman yaji, tun lokacin da kunnen sa yaji Alh nacewa, “zan so ka janye
maganar auren nan naka....” Wani zazzare ido ya yi saboda ya ji maganar a
bazata, bai taba tunanin Alh zai masa haka a ran shi ba, sai gashi rana daya al’amarin
ya zo mishi. Numfashinsa har wani kokarin daukewa yake, zuciyar shi na kokarin
bugawa, saboda lokaci guda ta shiga yi mishi matsanan cin ciwo. Shi ma kanshi
Alhajin hankalin shi ya ta shi, hakika ya tausayamishi sai dai kuma maganar
gaskiya ya riga
ya fada ba zai canza ra’ayi ba.
Shi kam Usman ya riga ya san
ba zai iya rabuwa da Farida ba, shi ka dai yasan irin son da yake mata, yana
matukar kaunar ta, tariga ta zamo mai wani gibi na zuciyar sa, bai yi zaton duk
fadin duniyannan akwai wata macen da zai so tamkar ta ba. Sai dai kuma a
tunanin shi kila mutuwar shi ta zo shi yasa ake kokarin raba shi da Farida. Da
kyar ya iya tashi da zaunen da yake ba tare da y ace wani abu ba ya nufi
bangaren shi. Kwantawa ya yi yana tunano soyayayar shi da Farida, soyayya ce mai
tsafta da natsuwa, lokaci guda wani tsananin son ta ya kara dira a zuciyar shi.
Zumbur ya mike zaune kamar wani tababbe, ya rike kai saboda tsananin ciwon da
yake mishi, ya fara gani dishi- dishi saboda jiri- jiri da yake gani, ya koma
ya kwanta ko zai samu sauki, amma ina! Har yanzu zuciyar shi zafi take mishi,
ya rasa inda zai saka kanshi.
Wasu zafaffun hawaye suka
tararo mishi, wai me yasa za’a yi mishi haka? Shifa gaskiya ba zai fasa wannan
auren ba, zaiyi iya kokarin sa don ganin ya shawo kan mahaifin sa, ji yake da a
raba shi da farida gwanda ma ace, ya rasa ranshi gani yake hakan zaifi masa
sauki, lokaci guda kuma zazzabi ya zo ya rufe shi.
Farida kam faduwar gaba take
yawanyi ba abinda ta ke sai yawan ambaton Inna lillahi wa inna i sai kuma ta
rika jin bata jin dadin jikin ta. Dare ya yi ta kasa bacci haka kawai, ita kan
ta abin ya bata mamaki, ganin ta kasa baccin, dauro alwalla ta yi ta zo ta yi
nafila, sannan ta bude kur’ani ta ci gaba da karantawa, a hankali ta ji ta fara
samun natsuwa, ta yi addu’o’in ta ta shafa ta koma ta kwanta. A hankali bacci
ya dauke ta.
Yaya Mukhtar kuwa sam kasa
baccin ya yi, shima yana tunanin tashi matsalar, da yaga tunanin ba in da zai
kaishi, shima alwalla ya yo ya ci gaba da sallar nafila yana rokon Ubangiji
cikin kaskantar da kai har kusan subahin.
Washe gari Usman ya sami
mahaifin shi, AIh Umar tausayin dan na shi ya kama shi sai dai kuma maganar shi
kaifi daya ce ba canji, har yanzu yana
nadamar barin Usman da ya yi nisa wurin neman auren, bai san dalilin da ya
hanashi ya hana dan tun farko ba shima yana zargin kanshi da yin kuskure. Usman
ya kaskantar da murya yana ba mahaifin shi hakuri cewa, kada ya raba shi da
farida kuka ya saka mishi tamkar karamin yaro, amma duk a banza, nan danan Alh. Ya shiga yi mishi fada
ce wa ya na son mai da shi mutumin banza.
Dole Usman ya fito, daki ya
shiga ya kulle kansa, hawaye ke ci gaba da zubo mishi, ya lalubo wayar shi ya
kira Farida, jin muryar ta ke kokarin mantar da shi halin da yake ciki, ya jima
yan a Magana da ita. A je wayar keda wuya tunani ya dawo masa sabo fil! Ya rasa
hanyar da zaibi ya shawo kan wannan matsalar, nan danan zuciyar shi ta rika yi
mishi wani zafi, mirgina ya rika yi kan gadon hadi da hawaye, sai kuma ya mike
ya rika safa da marwa cikin dakin.
Bangaren farida kuma bayan
ta aje wayar, haka kawai ta shiga zurfaffen tunani wanda ba ta iya cewa ga
dalihin yin shi ji take yau ta tashi da bacin rai, ba ta jin dadin zuciyar ta,
kamar ta saka kuka. Yawaita addu’o’i ta rika yi, ta na neman sassauci da kuma
tsari a wurin Ubangiji. Tunanin ta ya katse lokacin da text ya shigo wayar ta,
har yanzu ba number kamar haka:
Farida ki tallafi rayuwa ta kada ki juya
mini baya a lokacin da ki ka San ainihin ko ni waye.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment