HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 11
Ta dan yi jim sài dai kuma bata damu da text din ba, illa har yanzu ta kagu tasan mai wannan text, ta dan ja tsaki mts a ganinta da yana da niyyar bayyana kan shi da tun tuni ya bayyana, batasan dalili ba ta na yawan jin tausayin ko waye, sai dai kuma a ganin ta lokacin sa ya kure, ba ta tsammanin a kwai wani da namijin da za ta so kamar Usman din ta.
Me zai faru Iyayen Usman ne suka zo gidan su cewa sun janye zancen aure da dan su. Rayuwar Dad ta yi matukar baci, haka ya shiga gida rai bace, Mom din kuma taga tashin hankali, lokaci .guda tausayin ‘yar ta ya dira zuciyar ta. Farida kam lamarin ganin shi take kamar almara, gani take Usman ne ya yaudare ta, tun da sai da ya bari ta yi dumu- dumu, cikin kaunar shi zai ce ya fasa ba tare da wani dalili ba. Kuka ta saki mai shiga rai dole a tausaya ma ta.
Usman kam tun da ya ji aiken da Baban shi ya yi gidan su Farida, nan da nan ya kidime, kuka ya rika yi ma mahaifiyar shi rokon ta ya ke, “Mama don Allah ku tausaya min ku ceci rayuwa ta, Mama Farida ta riga ta zamo wani muhimmin bangare a zuciya ta, Mama ina ku ke son in saka rayuwa ta ne? Kukan nashi ya kara tsanan ta. Maman tashi ta kasa cewa komai ba ta san ta inda zata bulloma lamarin ba, gaskiya ta tausaya ma yaron in son samu ne zata goyi bayan sa ya auri farida, to amma ta san hakan ba zai yiyu ba saboda Alhajin kaifi daya ne, kuma a ganin ta tunda ya yi wannan hukunci tasan da abun da yake hange, hakuri ta rika ba Usman.
Lamarin na neman ya maida shi wani tababbe, haka Alh Umar ya shigo ya sameshi, tsaye Alhajin ya yi ya kasa zama saboda ganin ikon Allah, Usman gwiwa bibiyu ya durkusa gaban mahaifin shi yana ci gaba da rokon shi. Ganin Baban na shi ba yada niyyar janye magarsa, a hankali ya sassauta murya hawaye na zubo mi shi yake cewa, “Baba na yadda da zabin ku, amma don Allah Baba ka gafarceni, ka tallafa min kabarni in auri Farida sai a hada auren rana daya. Alh Umar ya ji tausayin yaron matuka baya son tauye shi ko kadan, ya taki sa’a ya yarda da magarshi, amma kash! Gani yake lokaci ya riga ya kule tunda har an sami mahaifin Farida an shaida masa an fasa auren ‘yar sa yanzu kam ba wata mafita.
Tun da ya ga mahaifin na shi ya sauko, cikin rudu ya bar gidan su zuwa gidan su Farida, da ka ganshi kasan hargitse yake. Ba ta yi niyyar fitowa ba dakyar Mom din ta ta lallaba ta, gara taje batasan dame shi kuma ya zo ba, hakanan ta fito ba don ta so ba. Ta isa wurin da yake wanda a lokacin ya fada zurfaffen tunani, dago kanshi da zaiyi ya gan ta tsaye firgice ya ida isa wurin ta, bai jira wata magana ba ya marairaice, “Farida don Allah kada ki guje ni, ki tausayama rayuwa ta don Allah.” Ya kara taku kamar biyu sannan ya ci gaba, “Farida kin sani ina matukar kaunar ki, bansan halin da zan shiga ba idan na rasa ki” kallon ta yake kallon da ke kokarin sanyaya gabobin jikin ta, bata iya jure kallon da yake mata a ganin ta duk yaudara ce, tana jin takaicin kanta da har yanzu son shi ke kokarin kara shiga zuciyar ta. Kalaman shi ya rika gaya mata hadi da magiya, maganganunshi sun samu yin tasiri a zuciyar ta, a hankali kaunar shi ke kara mamaye zuciyar ta, ta san tsananin son da zuciyar ta ke masa tausayin kanta take ji. Ta fahimce shi sai dai ita kam ba zata yi jayayya da hukun cin iyaye ba.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment