GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki, kuma aminci ya tabbata a
bisa zaɓaɓɓen jakada, Shugaban Annabawa Muhammad ɗan
Abdullah wanda aka saukarma fiyayyen littafi (Alƙur’ani) domin ya zamo shiriya da kuma waraka ga
muminai.
Yarda da aminci su ƙara tabbata a bisa iyalan gidansa, da sahabbansa, da
kuma muminai har ya zuwa ranar ƙarshe.
Ina ƙara godiya ga Allah da Ya yarda Ya ba ni dama, ilmi da
fahimta tayin rubuce-rubuce da kuma samun nasarar rubuta wannan littafi mai
suna “Kimiyar Na’ura mai ƘwaƘwalwa (Kwamfuta)”.Iyayena ke da alhakin duk abin da na zama a rayuwa,
kuma ina alfahari da su. Su suka ƙasance
masu yi mini tarbiyya. Da alhakinsu ne na kai ga wannan matsayi, don haka ina roƙon Allah Ya yarda da su,Ya kuma saka musu
da mafificin alherinSa.
Ina so in godewa mafi ƙaunatuwar malamai a rayuwata, musamman mahaifina
wanda a sanadiyyar shi da kuma damar da ya bani na samu cimma nasarar samun
ilimin kwamfuta a aikace. Ina miƙa godiyata ga Malam Atiku Shehu Faruq da Alkhafiz
Yusuf Abubakar Suru da kuma Malam Sa'idu Muhammad a dalilinsu Allah Ya fahimtar
da ni wani kaso mai yawa daga cikin yadda ake bauta maSa, da kuma kaɗaitaShi Shi
kaɗai.Ina roƙon Allah
Ya yarda Ya sãka musu da alheri.
Ina so in godewa Maigirma Hajiya Aisha Atiku
Bagudu (Matar Gwamnan Jihar Kebbi), musamman ga irin ƙoƙarin da ta
nuna na jajircewa da take yi na ganin ta taimakawa harkar matasa zuwa ga
matakin cin nasara.Da wannan ne nake yi mata fatan alheri da cigaba a cikin
rayuwarta mai dorewa.
Ina miƙagaisuwar bangirma ga masõyana da irin ƙoƙarin da suke
na bibiyar littafai na da kuma fatan alkhairi da nake samu daga gare ku ta
hanyar saƙo, ko kira ta wayar hannu.Ba abinda zance
da ku sai dai ince Allah Ya sanya alkhairi a cikin rayuwarku baki ɗaya amin.
Bazan rufe ba har sai na miƙa godiya ta ga dukan Ƴan uwana maza da mata daga iyalin Muhammad
Sani Nuhu, saboda abin da suka nuna gareni na soyayya, fahimta da kuma ƙarfafawa.
Sharahbil Muhammad Sani
8th
April, 2015, 18th
Jimadal Sani, 1436AH
***** ***** *****
***** ***** *****
***** ***** *****
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment