3.2 RAM DA ROM
3.2.0 RAM:Yananufin (Random Access Memory).
Wannan ƙwaƙwalwa ce mai ɗaukar bayanai a lokacin da ake amfani da kwamfuta idan tana buɗe. A duk lokacin da aka rufe kwamfutar to, duk bayanan dake cikin (RAM)
zasu tafi.
3.2.1 ROM:Yananufin (Read Only Memory) shine mai
karanta abin dake cikin ƙwaƙwalwa
kawai. Shi kuma Wannan ƙwaƙwalwa
ce da ke ɗaukar
bayanan da ake iya karantawa, amma basu gogewa. Bayanan dake cikin ROM basu
gogewa, kuma kullum suna nan, hasali ma koda an rufe kwamfutar suna nan ba zasu
fita ba.
3.2.2 Mashigar Fai-fai
(Disk Drives):Mashigar fai-fai wani abu ne dake iya karanta
bayanan dake kan fai-fai. Wannan maganace da akayi ittifaƙi a kanta, cewa dukkanin
kwamfuta ta mallaki nata mashigar fai-fan;
ta kuma mallaki (hard disk drive) da (floppy
disk drive) da
kuma (CD-ROM
drive).
Duk da haka, wasu ana samun su da
(DVD-ROM
drive).
Amma shi (hard disk) a ɓoye yake can cikin kwamfuta, shi kuma mashigar (floppy) da
mashigar(CD-ROM) ko
(DVD-ROM) zaa
iya ganinsu anan gaban akwatin na’urar kwamfuta (System Unit).
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment