3.1
TSARIN NA’URAR KWAMFUTA (SYSTEM UNIT)
Tsarin
na’urar kwamfuta shine kamar yaddamuka ganshi a gefen hagu, wani akwati ne na ƙarfe da ya ƙunshi duk wani abu
da ya ƙunshiharkar
lantarki.
Ga jerin kayyayakin da suke a cikin akwatin kamar haka:-
3.1.0 Na’ura mai ikon wadatar da wuta (Power Supply):Na’ura mai ikon
wadatar da wutar lantarki, na maida wutar lantarki yadda nau’urar kwamfuta zata
iya amfani da ita batare da wutar ta fi karfintaba.
A
duk lokacin da aka kunna kwamfuta na’urar wuta (power supply) na
juya wutar lantarkin yadda zata yi amfani ta ko ina asassan kwamfuta, sannan
kuma ta kai wutar ga sauran kayayyakin dake cikin kwamfutar.
3.1.1 Shimfiɗaɗɗen Allo (Motherboard):Shimfiɗaɗɗen allo (System
board) ana nufin shimfiɗaɗɗen allon da ya
kewaye ko ina, wanda ke riƙe da abubuwan dake
cikin na’urar kwamfuta, ya kuma haɗa su a kwamfuta suka
zauna tare.
A jikin shimfiɗaɗɗen allon, akwai manya-manyan
kati ko katuna guda uku; Katin murya wanda shi ke kula da abinda ya shafi
sautin murya. Katin hoton bidiyo da ke ɗauke
da nauyin kula da hotunan da ake gani a kan majigi ko abin kallo (monitor)
sannan kuma shi katin zamani irin na kwamfotucin yanzu na bada damar saduwa da
wasu mutane a kwamfutar ka kai tsaye. Bugu-da-ƙari,
ga shimfiɗaɗɗen allon,akwai (central processing unit). Shi CPU yana
kula da bayanai, sannan ya sanar da sauran kayayyakin dake cikin kwamfutar abin
da zasu aiwatar ko a ce zasu aikata.
3.1.2 Ƙwaƙwalwar kwamfuta (Central Processing Unit)
(CPU) ko kuma a kira shi da (Processor) wani
lokaci kuma shi ake kira da ƙwaƙwalwar kwamfuta, aikin da yake yi shine; yanakasancewa
mai fashin baƙi da fassara ga dukkan abin da yake faruwa a cikin kwamfuta.
Iyakar abin da zanyi misali dashi shine, mutumin da ya je ƙasar da ba sa jin yaren shi,kuma
shi baya jin yaren su, dole yana da buƙatar tafinta kenan; wannan tafinta
shi ke jin yarenshi kuma yana jin yarensu. Idan yayi magana
shi ne zai fassara musu.Idan sun yi magana shi ne zai fassara mishi. To, abin da yake fassarawa
kwamfuta abin dake faruwa tsakanin (hardware) da (software)
dake jikin ta shine (processor) ko kuma (CPU). Saboda haka
dukkan waɗannan (hardware)
da suke haɗe ga kwamfuta suna samun
taimakon (CPU) ne domin su gabatar da ayyukansu.
To, kamar yadda mutane suke iya ganin (CPU) wani ɗan ƙaramin karfe robaroba ne wanda yake ɗauke da ƙananan (conductors) waɗanda su suke yin wannan aiki. To, shi wannan (processor)
an ƙasashi
kashi uku, wato dunƙulallen (processor) guda amma kuma a
cikinsa, an ware masa ɓangarori guda uku, waɗannan bangarorin kowanne da abin da yake jira ya ji ya
shigo, yayi aikin da ya dace da shi.
Su waɗannan ɓangarorinda aka ƙasa kashi uku, wani baya
shiga aikin wani, sannan kuma kowannensu aikin da yake yi wani ɓangaren ba zai iya yinsa ba. Sannan kuma dukkansu za
su iya yin aiki a lokaci guda domin biyawa kwamfuta buƙatarta, domin kai mai
amfani da ita ka yi aiki ba tare da ka samu wata matsala ba. An kasa CPU gida
uku wanda suka haɗada: -
·
(Control Unit)
·
ALU
(Asthmatics/Logic Unit)
·
Register
Waɗannan sune ɓangarori guda
uku da ake samu a cikin (processor) ko kuma CPU wanda zamu yi cikakken
bayanin aikin kowane daya daga ciki.
3.1.3 Ɗakin Sarrafa Abubuwa
Ɗakin sarrafa abubuwa ɗaya ne daga cikin gidajen da ake samu a cikin CPU,
kuma yana da ɗakuna guda huɗu. Amma kuma aikin da ɗakin sarrafa abubuwan ke yi a dunƙule
shine ke jan ragamar gudanar kusan rabin aikin da CPU ke yi a cikin kwamfuta.
Amma kuma idan muka ɗauki waɗannan ɗakuna guda huɗu da muka yi magana,ɗakin sarrafa abubuwa na da ɗakunan da ake sarrafa bayanai (data)
kamar haka:
·
Karɓo bayanai daga
cikin ƙwaƙwalwar CPU
·
Sarrafawa da
kuma yin tafinta ga ita kwamfutar ta yadda zata fahimci saƙon da aka ɗauko daga ƙwaƙwalwa (memory)
·
Gabatar da
umarni kamar yadda ake son ayi shi
·
Ajiyewa ko kuma
rubutawa ƙwaƙwalwa (memory)
sakamakon abin da aka gabatar na bayanai ko kuma umarni
Waɗannan ayyuka da
ake gabatarwa a cikin waɗannan ɗakuna na ɗakunan sarrafa abubuwa, shi ake kira da yadda mashin
ke rayuwa (machine cycle) a turance. Yadda wannan ɗakunan suke yin
aiki yayi kama da aikin gona, kama daga shuka zuwa sarrafa shukar zuwa a ci.
Ɗakin da yake karɓar ko
dibo umarni ko bayanai (data) daga cikin ƙwaƙwalwar CPU, shi
neɗakin
farko da yake jira da zarar yaji an taɓa wani maɓalli na (keyboard) ko linzamin
kwamfuta (mouse) a jikin kwamfuta sai ya karɓi wannan saƙo (signal) da ya ji, ya kuma rike
sakon, sannan ya aika ɗaki na gaba.
Shi kuma
wannan ɗaki na gaba shine yake sarrafawa da kuma
yin tafinta ga ita kwamfutar yadda zata fahimci sakon da aka ɗauko daga ƙwaƙwalwa (memory),
wato a wannan ɗakin kawai ake fassarawa kwamfutar, wannan saƙon (signal) zuwa ga yaren da kwamfutar ke fahimta (Machine
Language). A lokacin da kwamfutar ta fahimci wannan saƙo dayake an fassara mata shi a wannan ɗaki sai ta aika
shi ɗaki na gaba. Wannan ɗaki na uku shi
kuma da zarar wannan saƙo ya
shigo sai ya gabatar da shi, abin da kuma ake nufi da gabatar da
sakon shine ; a fitarwa mai amfani da kwamfutar ya ga abin da yake yi.
Misali idan ka danna maballin (S) bazaka iya ganin shi ba har sai ta bi
waɗannan ɗakuna ta wuce
sannan kai ka iya ganin abin da ka danna, Allah Ya sa mu gane.
Daga nan bayan
bayanan sun bayyana a gare ka sai ɗaki na huɗu wanda shi kuma shine zai ajiye wannan aiki a cikin
(memory)
na CPU.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment