5.3 ILLOLIN AMFANI DA YANAR GIZO/KAFAFEN SADARWA (INTERNET)
Babushakka illolin da yanar gizo ke haifarwa suna da yawa
sosai, don haka sai dai mu ɗan tsakuro kaɗan daga
cikin matsalilin da take haifawa kamar haka: -
ü
Sau da dama mutane suka lalace a
sanadiyyar wannan kafar yada bayanai ta yanar gizo (internet).Yana daga cikin illolin amfani da yanar gizo tawajen
kafafen sadarwa na zamani ga mata. Babu shakka mun sani cewa mata mutane ne
masu son kyale-kyali da jin dadin rayuwa, kuma a cikin irin waɗannan guruf-guruf din za a iske da akwai matan masu kudi
ko kuma ‘ya‘yan masu kudi da basu da wani zance sai irin jin dadin da suke ji a
gidan mazajensu ko kuma gidan iyayensu. Wanda
hakan yake haifar wa da wasu daga cikin membobin guruf din kishi ko kuma jin
ina ma ace sune suke cikin irin wannan jin dadin rayuwar. Da akwai wani guruf
da wata daga cikin membobin guruf din take cewa ai ita da mijinta sun fahimci
juna sosai da hatta kudin albashinsa idan ya dauko zuwa yake ya zube mata, kuma
suna yin kasuwanci tare, kudin kasuwancin sai yadda ta ga dama ta yi da su ba
zai ce mata komai ba, duk abin da taga dama za ta yi da kudin, idan yana buƙatar kudi kuma wajenta zai zo ya tambaya. Ai kuwa kafin awa ashirin da
hudu membobin guruf din da dama sun lalubi mijinta a facebook suna ta tura masa
sakonni da dama suna son sa. To yanzu a nan laifin wa? Ita ta zo tana tallar
mijinta, mutane kuma su kaga tabbas ba wanda baya so ya sami irin wannan miji
da sai abinda matarsa ta ba shi ya saka aljihu. Wasu matan kuma zaki ga sai su
rasa inda za su je a basu shawara sai a dandalin sada zumunta. Idan mace ta yi
fada da mijinta ko kuma wani abu ya faru tsakaninta da iyayen miji sai ta zo
dandali tana neman shawara ko mafita. Ko kuma ka ji mace tana tambayar yadda
ake rayuwar zaman aure, duk a cikin dandalin sada zumunta, wannan ai shi ne kin
kwance wa kan ki da kan ki zani a kasuwa. Domin kuwa a cikin irin wannan taro
ba za a rasa wanda ya san ki ba ko kuma wanda ya san wani naki. Haba mata ai
ciki ba don cin tuwo aka yi shi ba kawai, shi ya sa dai auren iyayenmu ya fi
namu karko domin akwai su da iya adana sirrin da ke tsakaninsu da mazajensu.
Amma mu namu auren bayan shekara biyu zuwa uku ya kare saboda rashin hakuri da
iya tattalin miji , uwa uba kuma adana sirrin dake tsakani.
ü
Da yawa daga cikin matan aure yanzu sun gamu da mugayen kawayen da suka
saka su a cikin harkar shaye-shaye da neman mata ‘yan uwansu duk a ganin wayewa
ce, idan baka yi wannan harkar ba to kai ba ka waye ba. Don haka mata a rage
buri da son a san ke ma wata ce ko matar wani ko ‘yar wani ko kawar wani, domin
daga karshe ba abin da zai haifar sai da mara ido. Rayuwar duniyar nawa take da
har zaki saka kan ki a irin wannan masifar, ki batawa kan ki da ‘ya’yanki suna ki jawowa danginki
abin magana. Kowa ya yi da kyau zai ga da kyau.
ü
Sau da dama zaka shedi mutum da sheda mai kyau; amma akwana a tashi
kaji ance ya zama cikakken zingiki ko takagari wanda bashida aikinyi sai zinace
– zinace ko shaye – shaye kuma wannan yana faruwa ne ta dalilin amfani da
yafukan internet imma wajen haduwa da miyagun abukai ko kuma ziyartar shafukan
batsa kuma yana daga cikin illar amfani da yanar gizo, mutum kai tsaye zai iya
fadawa a wani guruf na mashaya jini ko ‘yan sihiri, wata kila shi baima sani ba
kawai wajen shige-shige ya jefa kansa a cikin mummunan hatsari.
ü
Yana
daga cikin illolinta mutum ya zama cikakken makaryaci misali; idan kama amfani da kafafen sada zumunta sai kaga mutum ya
dagargaje ya shirga wata irin karya da kai kanka sai hankalinka ya tashi idan
kaji ta. Wani zaiyi karya a fanni addini wani ko don ya burge ne kawai yake
karya a shafukan internet wani kuma bashi da aiki sai kuƙarin tayar da hankalin al’umma. Misali; lokacin da ake yada magana kan
ciwon ibola, masu ƙoƙarin yada wannan basuci
nasaraba harsai da sukayi amfani da kafafen internet da shafukan sada zumunta
na yanar gizo.
ü
A halin da muka tsinci kanmu a ciki a yau, yanar gizo (internet)
ta zama wata hanya ta yada miyagun akidu da kuma yada farfaganda don cimma wata
manufa imma ta ni kadai ko kuma ta wasu daidaikun jama’a don su cimma wata
manufa tasu ta su kadai.
ü
A yanar gizo (internet) sau da
dama ake lalacewa a sanadiyar finafinan batsa da mujallan batsa da ake samu
akan shafukan internet. Muna fatar Allah Ya karemu ya kuma shirya mana
al’umarmu baki daya.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment