3.3 SOFTUWAYAN
KWAMFUTA
Kwamfuta
ba ta aiki idan ba softuwayaa cikinta. Idan aka ce Softuwayaana nufin tarin wasu bayanai
da ake sakawa a cikin kwamfuta ana sarrafa ta da dasu, ko kuma shiri ko shirye-shiryen da ke bada umurni ga kwamfuta don sanar
da ita aikinda zatayi da kuma yadda zatayi aikin.
Softuwayan da muke dasu suma sun kasu gida biyu kamar haka:-
·
(System software)
·
(Application
software)
3.3.0 (System Software): - Shi dai (system software) ana kiran shi da
suna (operating system) (OS), a zahirance yana
tafiyane tare da kwamfuta. Ma’ana, duk lokacin da ka sayi sabuwar kwamfuta zaa
tarar da (OS) (operating system) a ciki.Kuma
wannan softuwayana (OS) shike kula da duk wani aiki na kwamfuta da
kayayyakin da kwamfuta take ɗauke da su. Mai karatu ya sani
cewa, kowace kwamfuta tana
aiki da (system software) sannan kuma idan har babu
(OS) shi kanshi (application software) bazai yi amfani
ba.
(OS)
ɗin
da yafi sauƙin in misaltawa mai karatu dashi shine (Windows Operating System)da
za a iya samun shi a kowace kwamfutar
tafi-da-gidanka (Personal Computer), ita kuma kwamfutar (Mac) tana amfani da (Mac Operating System).
3.3.1(Application Software):- Waɗansu tarin bayanai
ne da zasu ba mai amfani da kwamfuta damar gudanar da wani takamaiman aiki da
su ga kwamfuta. Akwai (application software) mabambanta waɗanda zamu iya gudanar
da takamaiman ayyukanmu dasu, kamar misalin waɗannan da
suke mafi
shahara da za a zayyanawa mai karatu, tare da bambance-bambancen ayyukan su
kamar haka: -
ü (Internet Application):-(Internet
Explorer) ce tsarin dake ba da
damar haɗuwa da yanar gizo,
sannan a iya bincikar wani adireshi na yanar gizo, ko
shafin yanar gizo kamar www.sharhamakinfo.tk ko www.signtechdp.com
ü (E-mail Application):- (Outlook
Express) na
ɗaya daga cikin
tsarin dake ba mai amfani da shi damar aikawa da karɓar sakon I-mel.
ü (Word Processing
Application): (Microsoftword)
shiri ne dake ba mai amfani da shi damar rubuta wasiƙar da zai iya turawa zuwa i-mel ko wani shafina yanar gizo.Ana
kuma iya ɗab’inabin
da aka rubuta kai tsaye,ana
kuma iya gudanar da duk wani abu da ya shafi harkar rubuce-rubuce
a cikin shi idan yana cikin kwamfuta.
ü (Spreadsheet
Application): - Za a
iya cewa (Microsoft Excel),
ita ce misalin wannan (application).
Tsarin (Microsoft Excel) na
ba mai amfani da ita dama wajen yin lissafi.
3.3.2 ABIN KIYAYEWA: Wannan nada muhimmanci ƙasan cewa idan ka
sayi sabuwar kwamfuta,
tana zuwa da (Operating System) da kuma wasu daga cikin (application Software) da za a iya samu a
cikinta. Dole ne ka sayi wasu ƙari n (application software) ka sanya a cikin
kwamfutarka.Sanyawa ko shigarwa na nufin shigar dasu a cikin hard disk din kwamfutarka
mai yuwa ne ka yi amfani da su nan zuwa gaba. Kuma duk wani kayan aikin da
kwamfuta ke buƙata yakamata a kula dasu sosai.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment