HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 4
*** *** ***
An kammala komai na auren farida da kuma Usman, hadi
da sanya ranar aure nan da wata biyar, anyi hakan ne ko yaya mukhtar zai fidda wacce, ya ke
so a hada auren, wanda anashi bangare sam zuciyar shi ta kasa nuna mishi wacce zai
zaba balle ya sa ran auren.
Zaune take cikin falo ta na
kallo Yaya Mukhtar ya shigo shi ma ya zauna, sai dai s hi ba kallon ya ke ba ya
dai tsura mata ido, a hankah ya lunshe idanun shi ya kwanta cikin kujerar, ta
dube shi “yaya Iafiya?” “me ki ka gani” ya tambaye ta “naga kamar baka da
Iafiya” murmushi ya yi “lafiya ta lau, farida kewar rabuwa dake ta fara kama
ni.” Tausayin yayan na ta ne ya kama ta “haba!
Yaya ka daina damuwa mana, ko yanzu da sauran lokaci kuma cekake zanbar gari.”
Bai yi Magana ba sai ma kara lunsashe idanun da ya yi, ta sake kallon shi ta
rasa me ke damun yayan na ta, ta dan tausasa murya “Yaya” ta kira shi “na’am
yar kanwa ta ina sauraren ki” sai dai kuma ya tashi zaune saboda alamar kiran
yasan Magana za ta yi da shi, ta dan saukar da numfashi a hankali ta ci gaba
“yaya don Allah me ya sa ka ke baya- baya da maganar su Dad ne? ka daure yaya
ka sanya musu farin ciki ka fitar da mata kayi auren nan ko hankalin su zai
kwanta, duk wadda aka ce, za’a Hada ka
nan take za ka ce, a’a sam! Kai baka
tashi ba. Yaya iyayen mu basu son takura mana to me yasa kake son abun da kasan
zai dame su? Yaya me yasa kake yin haka?, yaya mukhtar ya dan yi murmushi hadi
da cewa”in ban da abin ki farida ba sai mutum ya samu wacce, yake so zai yi
auren ba? ta dan yi murmushi ta san yayan na ta cikakken mutum ne, mai kamala
da kuma kwarjini, mutum ne wanda ko wace mace,, za ta yi guri, ta san yadda ‘yan mata ke kururuwa
a kan shi, wa su har kawan ce, su ke kullawa da ita a kan shi. Ko wace daga
cikin su ba makusa a gare ta, amma abin takaici ko gaisuwa ba zai yadda ya yi
da su ba, hotuna kam ya sha aiken su. Ta kauda wannan tunani ta ce, to yaya ka bani dama in zaba maka yarinya son kowa kin wanda ya rasa, insha’Allahu za
ka yaba da zabi na.” wani dan lallausan murmushi ya yi “Farida na yadda da
magar ki, sai dai kuma ni kaina nasan bayi na bane yin Allah ne. Nafison mata mai
kama dake matuka, halayyar ki da sauran dabi’un ki. Farida ina son dabi’un ki
sai inga ba ko wace mace ake samu haka ba, abin da yafi kawai ki bar wannan zance ki
tayani du’ai”.
Kanshi ya dauki zafi ya koma
cikin kujerar ya kwanta, idanun sa sun sauya zuwa ja baya so ana tada masa zancen
aurennan an rasa dalilin wannan al’amanin
nashi. Mom din tun tana kiran sa tana yi masa Magana har ta dangana ta koma yi
mishi du’ai.
*** *** ***
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment