5.8 SAKO TA HANYAR SADARWA (I-MEL)
Abin da yake nufi shi ne saƙo ta
hanyar sadarwar yanar gizo (Electronic Mail) (E-mail).
I-mel wata hanyace da ake iya bi
domin musayar wasiƙu tsakanin kwamfutoci guda biyu ko fiye da
haka. Waɗannan saƙwannin da mutum zai iya
aikawa sun haɗa da rubutu, hotuna, sauti, da kuma hoto mai
motsi (video) a lokaci guda.

Ɗalibai suna amfani da
akwatin i-mel dinsu
domin ajiyar takardunsu, da kuma bincike da suka yi domin sake amfani da shi,
kuma aikawa malamansu. Masu neman aiki suna amfani da akwatin i-mel wurin ajiyar takardunsu
da na shaidar kammala karatunsu domin aikawa zuwa ga
kamfanoni masu neman ma’aikata.
Kwamfutocin da ake amfani da su domin zama
uwar-garken saƙwannin sune (maiframes computers) da (minicomputers). Irin waɗannan kwamfutoci guda biyu
suna da tsarin da yake basu damar karɓa da kuma iya aikawa da saƙon da mutane ke aikawa zuwa
ga abokanan huldarsu.
Bayan mutum ya gama rubuta wasikar da zai
aika yana buƙatar adireshin wanda zai aikawa, ta wannan hanya ce
kaɗai wanda
ake son ya sami wannan sako zai iya samu. Aikawa mutum guda sako ko kuma aikama mutane da yawa shi ake
kira da “Broadcasting” a tsarin ilimi na i-mel. Sannan saƙwanni da
zasu iya zuwa ta hanyar imel suna da alama ta ‘@‘.
Cikakken yadda kowane tsarin
sunan akwatin mutum na i-mel yake shi ne kamar haka:sunanka@misali.com wanda sunanka shi ne sunan da
ka zaba ya wakilce ka a duk lokacin da za a aiko maka da saƙo.
Alamar @ wacce
itace ke biye da sunanka ita wannan alamar na nuna cewar wannan zai tafi ɗakin ajiya da kuma kai saƙone, duk saƙon da ake son a aika matuƙar ba a saka wannan alama ba
to ba zai taɓa tafiya ba.
Misali.com shi kuma yana fadar uwar-garken
da zai aika da saƙon, saboda haka duk saƙon da ba a saka uwar-garken da
za shi ba to ba zai tafi ba. Saboda haka kana buƙatarwaɗannan abubuwa guda uku kafin saƙonka ya zo gareka ko kuma ya tafi wurin wasu mutane. Sannan kuma babu sarari (space)
tsakaninsu.
Ba zaka iya aikawa da wani saƙon i-mel ba sai idan ya kasane kana da akwatin da zaka iya amfani da shi
wajen aikawa da kuma karbar saƙo na email. Wannan akwati shi ne ake
kira da “email account”. Misalin akwatin sakon shi ne www.yahoo.com ko
www.naij.com ko www.hotmail.com ko kuma www.gmail.com da sauransu.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment