HAUSA NOVEL BOOKS RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 2



RASHIN SANI…1 

BY SARATU M. SANI SERIES 2


*** *** ***
Ta shiga gida ta nufi  bangaren mom dinta, ta gaida ita mom din ta dan yi murmushi harkin dawo? Ta ce, “eh” sai dai hajiyar ta ce, ingaya miki idan an sake dauko wasu kayan wannan satin tana bukatar gold mai kyau, koda yake zata kiraki ta waya ta kara yi miki bayani. Dama aiken ta mom din ta yi, tashi ta yi ta nufi bangaren ta. Yaya Mukhtar ne ya dawo, daga office,  ya gaida mom din ta su, ya dan kalli mom din ya ce, “ina Farida  ne”? tana sashen ta ita ma yanzun nan ta dawo da aiken da nayi mata, bai sake magana ba ya nufi nashi bangaren.
Da shigar ta bangaren nata ta sami abincinta, nan tadan taba ci, sannan ta shiga wanka ta fito, ba tayi wata doguwar kwalliya ba ta dauko atamfa  ta saka, atamfar ta yi mata kyau matuka dinkin yayi cif! cif! Da ita,  ta fito falo, yayan na ta ne ya fito ya same ta; ta dan fadada murmushin ta ta gaida shi ya sami wuri ya zauna kusa gare ta. Hirar su suke cikin nishadi a lokacin wayar ta ke nuna ma ta alamar kira, Usman din ta ne tana matukar son shi a ra ta, kamar yadda shima yak e kaunar ta. Ta dauki wayar suka gaisa daga baya suka ci gaba da hirar su, akarshe yake shaida ma ta gashinan zuwa gidan na su. Sam ta manta da yayan ta dake wurin, tashi ya yi ya haye sama ya barta ita kadai. Bada wani jimawa ba sai ga Usman din ya zo, lemu iri – iri ta aje masa da sauran kayakin mutsa baki. Hirar su suke cikin nutsuwa tare da jaddada ma juna irin  kaunar da suke wa juna, akar she ya yi sallama da ita hadi da mika ma ta manyan ledodi guda biyu kayakin cosmetics ne a ciki ta yi godiya.
Bayan fitar Usman din ne ta sami yayan na ta cikin falon, ta dan dube shi sai dai ga alama fuskarshi  ba walwala kamar dazu, ta dan zauna kusa dashi cikin nuna alamar damuwa ta ce, “yaya lafiya na ganka haka?” ya dan yi murmushi “ba komai Farida kinsan akwai yanayi na rayuwa” to amma….. “ text ne ya shigo wayar ta shi ya katse ma ta maganar ta karanta text din dauke yake da kalaman soyayya ma su ratsa jiki ta duba da kyau ba number anyi hiding. Ta danyi gajeren murmushi lokacin da zuciyar ta ke tabbatar ma ta Usman din ta ne, ya na dai son tsokanarta. Text din ya shiga zuciyar ta sosai ta ji dadin kalaman, tayi saurin kawar da wannan ta ci gaba da Magana da yayan na ta.
Da dare misalin 8:45pm text ya sake shigowa wayar ta ta duba har yanzu ba number sai dai text din kamar yafi na dazu, ta danyi jim ta na nazari ita dai ta san ba tada wani saurayin da zai rika turo ma ta text dauke da sanyayyun kalamai fa ce,  Usman, to idan kuwa shine meyasa yanzu zai rika hiding number alhali bai saba yin haka ba? Ta kauda wannan tunani ta nufi bath room wanka tayi ta fito, mai kadan ta shafa ma jikin ta, ta dan feshe jikin ta da turare, sannan ta dauko rigar baccin ta itama ta kara feshe ta da turare sannan ta sa, bakin gado ta zauna ta karanto addu’o’in da ta saba karanta wa idan zata shiga bacci, tabi lafiyar gadon ta t a kwanta hadi da rufe jikin ta kadan da tattausan bargo. Uhm ‘yar gidan Daddy kenan.
Da safe bayan ta tashi ta yi sallah ta koma baccin ta, sai  kusan karfe tara ta tashi ta yi wanka, ta fito ta zauna bakin madubi ba wani dogon make-up ta yi ba, powder ta dan shafa a fuskarta, sai man lebe data shafa, iya kacin kwalliyar kenan bata cika shafa kwalli ba sam bai dame ta ba, ko bata shafa ba ba zaka gane ba da yake girar idanun ta nada tsawo da kuma baki sosai. Sam ra’ayin ta ba ta cika  fuskar ta da kwalliya amma duk da haka zaka ga ta fito fes da ita, duk inda ta gifta ya zama dole a dubeta saboda jan hankali da ke gareta.
Doguwar riga tasa sai dai kan na ta ba dan kwali hakan ya bada damar kan nata da ya sha gyara ya zuba gadson baya, ta duba agogo goma da minti ashirin da sauri ta fito a hankali ta isa wani makeken falo, tanan ta nufi bangaren Mom din ta, ta gaida itacikin girmamawa da yake Dad din nasu baya gari ya yi tafiya. Ta sake bin wata hanya zuwa wurin da suke break fast ita da Yayan na ta tasan yanzu haka yana zaman jiran ta, tana isa shima yana isowa wurin, ya dan ja daya daga cikin kujerun dake zagaye da dinning table ya zauna fuskar sa dauke da murmushi ta gaida Yayan sannan ta zauna zaman ta keda wuya kamar jira ake text ya shigo wayar ta har yanzu ba number kalaman sun fara daga mata hankali fuskar ta tanuna alamar damuwa. Yanzu kam abun ya fara bata mamaki zuciyar ta a yanzu ta riga ta bata tabbacin ba usman bane, to waye? Amsar da tayi kokari ta lalubo sai dai ba hali domin zuciyar ta ta kasa fahimtar da ita komai. Haka suka kammala break din zuciyarta cike da damuwa; Yaya Mukhtar ya fahirnci damuwar da ta samu lokaci daya, yasan bazata yi saurin gayama mutum damuwar ta ba saboda tsananin zurfin ciki.
Bayan sun kamala Yaya Mukhtar ya ce, “jeki dauko mayafinki  mu je gaida Inna” kakar su Haj balki kenan ta ce, “to” ba musu sai dai ita sam bata cika son shiga gidan Inna din ba, koma ta shiga ba wani kallon arziki innar zata yi ma ta ba balle ta kula ta, sam jininsu bai hadu ba ita ta rasa dalilin wannan tsanar da inna ke ma ta.
          Ta dora mayafinta ga kai suka fito gida su ka shiga gidan Inna, sunyi sallama tun kamin su shiga falon yaya mukhtar ya fara tsokanar ta wasan jika da kaka, cikin fara’a ta amsa sallamar ganin farida yasa tadan sauya fuska sama-sama ta karba gaisauwar da farida ke ma ta, ganin haka yasa ta mike tsaye hadi da Cewa “Inna sai anjima” ta fito zuciyarta zafi take mata, ba tada halin ta shiga gaida ta ita kadai tatas  inna zatayi ma ta. Za kaga ta fara maganganu daban daban, ita dai farida ta rasa me ta yi ma innar har ta tsane ta. Shima Mukhtar ganin farida ta fita bai tsaya yima innar sai anjima ba, balle yar hira ya fito abin sa tana kiran sa yaki tsayawa sauri yake ya cimma kanwar tashi, nan ya barta ta shiga fada. Gida ya same ta wurin mom din su hira take yi da ita cikin nutsuwa, ya sami wuri ya zauna ya katse hirar da Cewa, “don Allah mom me yasa inna koda yaushe take kokarin cusa ma mutum damuwa a zuciya?” Mom din tasan inda maganar ta shi ta nufa, ta tabbata farida inna ta taba shi yasa yake wannan tambayar, ta dubi farida “hala kin je gaida ita ne? “eh tare da yaya mukaje” farida ta ce  da ita, mom din ta yi murmushi “kiyi hakuri farida Sai dai ki rage yawan shiga wurin ta kin ji ko?” ta dan yi murmushi ba komai mom nasan haduwarjine ne da kuma tsufa.”
*** *** ***

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment