HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 3



RASHIN SANI…1 

BY SARATU M. SANI SERIES 3


*** *** ***
Soyayya mai karfi ta kara kulluwa tsakanin farida da Usman, yauma kamar kullum ya zo wurin ta hira suke cikin nishadi da natsuwa, Usman yadan tsar eta da ido ya na kallon ta, murmushi ta yi hadi da sadda kanta, ya dan yi murmushi shidai dabi’un ta na bashi sha’awa ya katse shirun da Cewa, “Farida” cikin sigar  muryar sa mai jan hankali da dadin saurare, ba ta gajiya da sauraren muryar shi, ta dan dago ta kalle shi kallon na daban ne, hakan ke sa zuciyar shi na kara kamuwa da shaukin kaunar ta. Ya ci gaba, “don Allah da gaske ki na so na?” tambayar ta ji ta ba zata, batasan amsar da za ta ba shi ba, ta na da tabbacin ya san ta na son shi kamar yadda ya ke son ta, sai dai batasan inda wannan tambayar ta dosa ba. Ta dan yi murmushi “Usman to meye kuma na wannan tambayar alhali ka na da tabbaci ina son ka?” ya dan yi sanyayyar ajiyar zuciya hadi da Cewa, “Farida ni kadai na san irin kaunar da zuciya ta ke miki, na tabbata bazan iya cigaba da rayuwa ba tare da ke ba, na kan zama kamar marayen da ya rasa Uwa idan ba ki kusa dani, farida tsananin son ki kan sa ni kuka hadi da tausaya ma kai na, gani na ke kamar wani zai  raba ni da ke. Don Allah farida kada ki guje ni alhali sonki ya yi min mummunar kamu, bansan halin da zan shiga ba idan na rasa ki.”
Maganganun sun shiga jikin ta tausayin shi ya kama ta, sai dai ita kam ta san ba wanda take so banci shi daya, to balle ya yi tunanin za su rabu, ba ta son irin maganganunnan su kan tayar mata hankali. A hankali ta ke Magana cikin natsuwa, “ka daina sanya wannan a ran ka, ka kwantar da hankalin ka insha’Allahu ba wanda zai raba mu face,  Ubangijin da ya hada mu, kawai mu ci  gaba da du’a’i.” Ta na cikin maganar text ya shigo wayar ta kamin ta duba wani text din ya sake shigowa, ba ta duba ba da yake ta riga ta san lambar nan ce,   da aka saba turo mata message, matsala daya boye lambar da ake.
Fuskar ta ta nuna alamar damuwa sai dai sam bata bari usman din ya fahimci wani abu ba, saboda bata son Ya shiga damuwa. Da hakan kuma ya yi sallama da ita ya wuce. 
Haka soyayyar ta su ta ci gaba da gudana cikin tsafta da natsuwa,
a bangare guda kuma take kara samun yawan text messages ga wayar ta,
wanda ba tada tabbacin mai text din. A dayan bangaren kuma zuciyar ta na matukar damuwa da yadda Inna ke mata, tsanar da Innar ke ma ta sai
karuwa take ta rasa dalilin tsanar.
Misalign sha biyu da rabi na rana ta shirya cikin wani dakakken lace, kwalliyar ta yi matukar karbuwar ta, sai wani kamshin turare take, mayafin ta kalar lace,  din ne, takalmin ta yan flat ba masu tsini ba sai yar hand bag din su mai kyau, ta fito fes da ita. Ta nufi sashen Mom din su ta shaida mata Cewa za su fita, dama gidan Humaira Yayan na ta zai kai ta, Mom din ta yi murmushi “ yar gidan daddy kinga yadda ki ka kara kyau kuwa?” murmushi kawai ta yi ta fito, ta nufi wurin dalleliyar Jeep din da yayan na ta ke jiran ta, ya bude mata gidan gaba ta shiga ta zauna, ya zagayo shima ya shiga ya dan kalle ta, fuskar shi dauke da murmushi, “kanwa ta kinga yadda ki ka yi kyau  kuwa ? kwalliyar ta yi kyau” ta dan yi murmushi “na gode da yabawa Yaya na”. A dai dai lokacin text ya shigo wayar ta, yau dai ta dan daure ta karan ta.
Kalaman sun tsaya mata arai, ta so tasan ainihin ko waye. Yayan na ta ya dan kalleta, hadi da tada motar ya karanci damuwa tattare da ita, Sai dai ya ci gaba da tukin da yake ya damu matuka baya son ya ga ta bata ran ta ko kadan, hakan da ta gani ya sa ta yi saurin sake ran ta, sai dai zuciyar ta na cike da tunani daban daban. Sun dan yi nisa da tafiya ya sake kallon ta, ya na yaba dabi’un ta du’a’in sa koda yau she Allah ya zaba masa mata kamar kanwar sa.
Sun isa gidan Humaira ya yi parking ta fito, dubu goma ya mika mata “karbi wannan kiba Humaira” ta nuna farin cikin ta ta Karba hadi da godiya, sai zuwa azahar zai zo daukar ta.yayan na ta yana matukar kula da ita, ya na son duk wani abun da take so, ya tsani damuwar ta, yafi son ya gan ta cikin nishadi ko wane lokaci.sai dai abu daya sam baya son kanwar tashi ta yi nisa da shi, sun shaku da juna sosai, wani lokaci har sukan ba jama’a mamaki. Azahar na yi ya zo daukar ta Humaira ta rako ta hadi da godiya, kawancen su son Allah ne aminci ne tsakanin su sun zama tamkar yan’ uwa.
*** *** ***

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment