1.5.2 Ma’ajiya (Banki)
A wannan lokaci da ake ciki, bankuna gaba daya sun dogara ne ga kwamfuta.
Bankuna suna amfani da kwamfuta ta waɗannan hanyoyi :-
· Buɗe asusun ajiya ta hanyar yanar gizo, wanɗada suka haɗa bincikar ragowar kuɗin asusu.Sanya kuɗi.Turawa wani kuɗi.Saka hannun jari, da kuma halastaccen ɗaukar faifai ko bayanai.
· Na’urar ATM takawo sauƙi ga abokan hulɗar kasuwanci da ke hulɗa da bankuna.
Hoto 4: Ana amfani da Na’urar ATM domin fitar da kuɗi a asusun ajiya na banki
1.5.3 Ilimi
A ɓangaren ilimi kuma, Kwamfuta ta taka muhimmiyar rawa kamar yadda zamu karanta abin zai biyo a ƙasa kamar haka:-
· Amfani da kwamfuta yana cikin abubuwa muhimmai wajen tsarin ilimi wanda muka sani da suna CBE wato (Computer Based Education)
· CBE ta ƙunshi kula, ceto da kuma kimanta harkar koyarwa.
· Akwai hanyoyi dayawa na koyarwa da kwamfuta, kuma manyan makarantu suna amfani da kwamfuta don su koyar da ɗalibansu.
· Ana shirya bayanai game da sakamakon jarabawar ɗalibai da sauransu.
Hoto 5: Malami na bada darasi ga ɗalibai
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment