MA’ANAR KWAMFUTA: KIMIYYAR NAURA MAI KWAKWALWA 6



1.1 MA’ANAR KWAMFUTA
Kwamfuta na’urace mai amfani da wutar lantarki da ke karɓar (ɗaukar) bayanai kuma ta sarrafa bayanan ta hanyar bada umarni. Sannan ta bayar da amsar umurnin da aka bata.
1.2 HALAYYARKWAMFUTA
Dukkanin (dijital) kwamfuta ta ƙunshi sharuɗɗa guda biyar waɗanda take amfani da su.
·       Ɗaukar bayanai domin shigarwa
·       Adana bayanai a cikin ma’adanar ƙwaƙwalwarta (memory) sannan tana iya amfani da bayanin da ta adana a lokacin da aka buƙaceshi
·       Tsara bayanai da kuma sarrafasu ko juya su zuwa ga bayani mafi kyau
·       Bayar da sakamako
·       Kula da dukkan waɗannan matakan guda huɗu
Waɗannan sune abubuwan da (dijital) kwamfuta ta ƙunsa.

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment