Jerin gwanon
na’urorin da ake iya gani masu shigar da bayanai, kuma a tabasu kai tsaye
LAMBA:
|
SUNA
|
HOTO
|
|
1.
|
Allon Rubutu
(Keyboard):Ana amfani da madannin allon rubutu (keyboard) domin
rubuta wasiƙa, lambobi da kuma yin wata alama (symbols) a
cikin kwamfuta.
|
|
|
2.
|
Linzamin Kwamfuta
(Mouse): Linzamin kwamfuta wani
abu ne da ake yawo da shi, kuma yana da maɓallai waɗanda za a iya canjawa a
kowace irin siffa,akan lallatsasu lokacin da ake aiki da kwamfuta.
A na danna linzamin ta
hanyar dannawa da sake madannin. Wannan tsarin na bada damar shigar da
bayanai lokacin da ake aiki da linzamin.
|
|
|
3.
|
Abin Kwaikwayon Siffa (Scanner):Tana ɗaya daga cikin abubuwan shigarwa wacce take
kwaikwayon siffa (kwafi) daga takarda zuwa cikin kwamfuta
|
|
|
4.
|
Makirufo (Macrophone):Makirufon ana amfani da shi wajen
shigarda murya cikin kwamfuta.
|
|
|
5.
|
Kamarar ɗaukan Hoto (Digital Camera):Kamarar ɗaukar
hoto na bada damar ɗaukar hotuna waɗanda za a
iya sanyasu a cikin kwamfuta.
|
|
|
6.
|
Kamarar Bidiyo (Video Camera): Kamarar hotonbidiyo ta kwamfuta na
bada damar ɗaukar hoton bidiyo, kai harma da hotunan da bana
bidiyo ba, kuma a sanya su a cikin kwamfuta.
|
|
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment