ILLOLIN KWAMFUTA: KIMIYYAR NAURA MAI KWAKWALWA 8



1.4 ILLOLIN KWAMFUTA
Waɗannan bayanai da zan zana a ƙasa sune illoli ko rashin amfanin na’urar kwamfuta a wannan rayuwatamu ta yau:-
·       Kwamfuta na’urace wadda bata da tunani, hankali da kuma basira.Aƙashinkanta bata iya gudanar da komai.
·       Kowane irin aiki zatayi dole ne sai an sanar da ita shi kafin ta aikatashi.
·       Kwamfuta bata iya ɗaukar kowane irin mataki da kanta.
·       Duk abin da zatayi tana ƙarɓane daga mai amfani da ita, don haka ya zama wajibi duk abin da zata gudanar yafito daga mutum ne.
1.4.0 Muhalli
·       Tabbas muhallin da zaka adana kwamfuta ya zama mai tsafta kuma ya ƙasance wurine da ba ƙura.
1.4.1 Rashin Ji
·       Kwamfuta ba aba bace da ke ji ko gani ko kuma ta iya gudanar da wani tunanida kanta.
·       Bata iya yanke hukunci.
·       Bata iya ji ko ɗanɗano ko yin wani abin gwaninta ko kuma aiwatar da wani abu na ilimi saɓanin mutum.

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment