KADDARAR RAYUWA



H
ajiya Zainab, kyakkyawar mace, zaune a katafaren falonta, shekararunta za’a iya cewa tadan kwana biyu a duniya, sia dia da yake tanada jiki mai kyau zaka iya cewa iya shekaraunta Arba’in alhali ta wuce shekarun. Ita kadaice cikin falon, shiru da alama akwai tunanin da take, shigowar yar ta kuma autar tat a katse mata tunani ta shigo da Sallama gudu-gudu ta isa wurin mahaifiyarta tana kokarin fadawa jikinta mahaifiyar tadanyi murmushi hadi da tare tad a hannu tana cewa, “a’a Mufeeda kada kijimin ciwo, wannan gudu da kikazo dashi”, dariya sukaji ashe yaya mukhtar ne, yau Ummi keda autar taki kuma? Mufeeda tadan zumbura baki ta fara. Magana kamar zatayi kuka “Ummi kinga yaya Mukhtar yanamin dariya ko?. Ummi tace, “Zo abinki auta, kyale wannan yayan naki, ta dora yima yayan gwalo. Ummi tace, kin kaima mama kande sakon? Mufeeda tace, “eh”.
Gaskiya Ummi kina sagarta Yarinyar nan, “a’a Mukhtar bari na lallashi Yata, amma baya hana idan tayi min ba dai-dai ban a saba mata.
Mukhatar yace, gashinan yarinya ta girma amma kullum kamar jinjira, ya karasa maganar lokacin da yakai zaune shima, ya gaida Ummin ta mishi sannu da zuwa ya amsa Yana fara’a sai lokacin itama Mufeeda ta sauko ta gyara zamanta hadi dayi mishi sannu da zuwa sai kuma ga sauran yayan na shigowa, Umar, Abdulmajid, Bilal suka gaida mahaifiyar sannan suka gaida yaya Mukhtar, itama Mufeeda ta gaidasu.
Nanfa suka zauna tare da mahaifiyarsu suna hira, cikin kwanciyar hankali gwanin ban sha’awa daka gansu kasan iyalan suna cikin farin ciki, cikin hirar, Mufeeda ke cea, “Ummi niko wai mama Kande, ya kuke da ita ne? naga akwai aminci da fahimtar juna tsakaninku saurian yayan sukace kai gaskiya auta kinyi tambayaar da kullum mukeso muyiwa Ummi, Yaya mukhtar yace “Mama kande ai yayar umm ice, Umar Yace, Amma Ummi bata taba fada mana ba sai dai ko yaushe nasiharta mu rike Mama Kande tamkar yada zamu riketa wani lokacin har cewa take mu rike Mama Kande tamkar Uwa fiye ma da yadda zamu riketa, Bilal yace nikuma ina mamakin yadda Ummi ta rike MamaKande, kullum ciki dawainiya da ita, bata gajiya nifa wani lokaci har haushi nakeji yanda Ummi ke bata lokacin ta wurin yi mata hidima, to bale ance Mama kande batada lafiya to shikenan Ummi ba zama Abdulmajid yace ni kuma Mama kande tausayi take bani gashi batada shi, kuma gashi Allah ya jarabeta da rashin haihuwa sannan dangi a rasa mai kula da ita, saboda batada shi, yaya Mukhtar yace ai mutane yanzu sai kanada shi ne sannan ake sonka idan bakada shi to kasha ma yafika daraja ga jama’a ka dubi boyar Allah nan wallahi rayuwarta akwai tausayi.
Ummi tadan numfasa hadi da cewa “hakane Rayuwarta akwai tausayi, shiyasa koda yaushe Abbanku dani kaina muke kara nuna muku kada ku dauki duniyar nan wani abu tsoron Allah tausayi hakuri, girmama na gaba dakai, addua duk wanda ya rike wannan zakuga al’amuran duniya nazo mushi da sauki rayuwar nan da kuke gani ba komai bace amma yanzu sai gashi munzo lkacinda sai kanada shi kake da mutunci da girma ga Jama’a idan kuma bakada shi to kai da babu duk daya ga Jama’a.
Ta dan numfasa Rayuwa indai kana raye, to babu shakka ba’a halittarka ba, sannan dole Rayuwa kowace da jarabobin da Allah ke kaddara mata a Rayuwa.
Mama kande koda yaushe na kalleta saina zubda hawaye duniyar kuma saita kara firgitani tsoron Allah Yana kara shigata musamman idan na hada rayuwarta da tamu Rayuwa idan na tuna baya mama kande, tana da matukar muhimmanci a rayuwarmu tayi mana komai, shiyasa kukaga nida Abbanku babu yanda za’ayi mu manta da ita, mama kande ta cancanci komai a wurinmu.
Shekararun baya da suka wuce....

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment