BABI NA TARA
9.0 HANYOYIN TARTSE NA MAƁALLAN ALLON
RUBUTU (KEYBOARD SHORTCUT)
Gajerun hanyoyin Allon Rubutu (keyboard shortcut)
shi ne hade maballai biyu ko fiye don ayi amfani da su wajen gudanar da wani
abu wanda linzanmin Kwamfuta ke gudanarwa ko wani abu da ake iya amfani da shi
don a bawa Kwamfuta wani umurni wanda ba linzamin kwamfutaba. Gajerun hanyoyin
maballan Allon Rubutu za su iya zama sune mafi saukin hanyar da za a yi amfani
dasu ga Kwamfuta don rage bata lokaci a lokacin da a ke gudanar da aiki da
Kwamfuta ko wani kunshi.
Da yawan kumussa suna da nasu (shortcut)
gasherun hanyoyi da a ke amfani da maballai don samun sauki wajen amfani da su
ta wajen zabi ko kuma umurni da za a iya basu.
Wata kila baka taba sanin wasu maballai da ake amfani
da su a lokaci daya ba a Kwamfuta.
Babu shakka a Kwamfuta maballain da ake amfani da su a
lokaci guda suna taimakawa wajen saukaka
aiki tun daga wajen rubutu ko kuma inda ba nan ba, ba tare da daukar lokaci ba
wajen gudanar da aikin.
Don haka na yi sha’awar cewa mai karatu ya san
wadannan gajerun hanyoyin don shima ya amfana, a kan haka naso inga kwamfutar
mai karatu lokacin da yake amfani da wadannan gajerun hanyoyin na maballan Allon
Rubutu (keyboard shortcut) don inga irin nashi gwanin ta.
ABIN KIYAYEWA: Wasu daga cikin gajerun hanyoyin da aka bayar ba zasu iya amfani ba ga (versions) da ke kasa ga Windows 8 ba.
Jerin Gwanon Gajerun
Hanyoyin Amfani Da Maɓallan Allon
Rubutu (Keyboard Shortcut)
L/B
|
MADANNI
|
AMFANI
|
1.
|
Print
Screen:
|
Yana bada dammar daukar duk wani abu da ke kan
majigin a ce abin kallon Kwamfuta kai tsaye.
|
2.
|
Alt + Print Screen:
|
Amfanin shi wajen daukar hoto (photographing
capture) na mutsin kwamfuta na karshe a abin kallo da kuma adana shi ga
(Clipboard).
|
3.
|
Ctrl + C:
|
Amfani sa domin kwaikwayon sifar da dama akwaita da
ke cikin wani fayil ko a kunshin (Microsoft word)
|
4.
|
Ctrl +X
|
Yana bada dammar dauke abu
|
5.
|
Ctrl + V
|
Amfanin sa shi ne idan ka dauko wani abu da ka
kwaikwayi siffarsa ko ka dauke shi sai ka ajiye shi da (ctrl + V)
|
6.
|
Ctrl + Z
|
Yana bada dama wajen cirewa ko maidawa zuwa ga na asali
|
7.
|
Delete:
|
Ya na bada dama wajen goge abu ko daukeshi zuwa ga
kwamdun shara (Recycle Bin) sai dai akwai banbanci idan anyi amfani da shi a
(Folder flash)
|
8.
|
Shift + Delete:
|
Zai bada damar goge abin da aka zaba kuma gogewa da har abada ba tare
da kai abin a cikin kwandun shara ba (recycle Bin)
|
9.
|
Ctrl tare da zabin wani
abu a danne a ja:
|
Wannan zai bada damar kwaikwayon siffar abin da aka zaba
|
10.
|
Maballin F2:
|
Na bada damar canja sunan abin da aka zaba
|
11.
|
Ctrl + Shift tare da duk
wani (direction na arrow):
|
Zai bada damar rufe rubutu da wani bular launi
|
12.
|
Shift tare da wani daya
daga cikin (direction arrow):
|
Zai bada damar zabin abu ga window ko desktop ko wani rubutu a
daftarin aiki (documents)
|
13.
|
Ctrl + A:
|
Zai bada damar zabi duka
|
14.
|
F3:
|
Amfanin sa shi ne nemo fayil ko folder
|
15.
|
Alt + Enter:
|
Na
bada damar duban (properties) na abin da aka zaba
|
16.
|
Alt + F4:
|
Na
bada damar rufe aikin da ake yi, ko aikin da aka riga aka shirya
|
17.
|
Alt + Space bar:
|
Zai
bada damar a bude gajerun hanyoyin zabi na (active window)
|
18.
|
Alt + Tab:
|
Amfanin
sa wani sirri ne da yafi kowane sauri idan a na bukatar kashe kwamfuta
|
19.
|
Tambarin Windows :
|
Amfaninsa
don ya bude abubuwan da suka boye a (Start menu)
|
20.
|
Tambarin Windows + Break:
|
Na
bada damar nuna (system properties)
|
21.
|
Tambarin Windows + D:
|
Amfanin
sa don a dawo ga (desktop)
|
22.
|
Tambarin Windows + M:
|
Amfanin
sa don ayi (minimized windows)
|
23.
|
Tambarin Windows + Shift + M:
|
Na
bada damar mayarda abinda akayi (minimized) (restore minimized windows)
|
24.
|
Tambarin Windows + E:
|
Wannan
yana bada damar bude (My computer)
|
25.
|
Tambarin Windows + L:
|
Amfanin
sa don a rufe maballan Allon Rubutu (keyboard)
|
26.
|
Tambarin Windows + R:
|
Na
bada damar bude (run)
|
27.
|
Tambarin Windows + U:
|
Na
bada damar bude (Utility Manager)
|
28.
|
Ctrl
+ F:
|
Yana bada damar nemo rubutu ko fayil da ke
cikin kwamfuta
|
29.
|
Ctrl
+ S:
|
yana bada damar adana daftarin aiki, safin
yanar gizo da sauransu
|
30.
|
Ctrl
+ D:
|
ya na bada damar kowane irin fayil ko
daftarin aiki ko rubutu
|
31.
|
Ctrl
+ P:
|
Amfanin sa shi ne don gurza takardun da ke
cikin kwamfuta
|
32.
|
Ctrl
+ A:
|
ana amfani da wannan don a rufe dukan rubutu
ko fayil wani bula a launi
|
33.
|
Ctrl
+ N:
|
amfanin sa don a bude wani sabon window ko
fayil ko kuma daftarin aiki
|
34.
|
Alt
+ F4 ko Ctrl + W ko kuma Ctrl + Q:
|
amfanin su don a rufe aikace aikacen windows
kuma ana iya amfani da su wajen rufe kwanfuta
|
35.
|
Alt
+ tab:
|
amfanin sa don ayi (switch windows)
|
36.
|
Alt
+ tab + tab + … + tab:
|
don a cigaba da canja windows
|
37.
|
F1:
|
ana amfani da shi don neman taimako
|
38.
|
F2:
|
amfanin sa don canja sunan abinda aka riga
aka zaba
|
39.
|
F3:
|
ana amfani das hi wajen nemo fayil ko folder
|
40.
|
F4:
|
ana amfani da shi wajen nuna (address
bar list) a (file explorer)
|
41.
|
F5:
|
amfaninsa don (refreshing active window)
|
42.
|
F6:
|
amfanin sa don yawatawa a cikin abubuwan da
ke kan majigin kwamfuta a (windows) ko (desktop)
|
43.
|
F10
|
amfanin sa (activate the menu bar) a cikin
komfin da ake amfani da su
|
44.
|
Alt +
F4:
|
amfanin sa don rufe aiki da ake kanshi ko
rufe kunshin da ke bude
|
45.
|
Alt +
Esc:
|
yana amfani wajen yawo cikin abubuwa a
lokacin da suke bude
|
46.
|
Alt +
underline letter a cikin akwatin zabi:
|
na amfani wajen bada umurni ga wannan
(letter)
|
47.
|
Alt +
Entre:
|
na amfani wajen nuna cikakkun bayanai abun da
aka zaba
|
48.
|
Alt +
Space bar:
|
na bude gajerun hanyoyin da za a iya zaba ga
aikin da ake kanshi
|
49.
|
Alt +
Left arrow:
|
ana amfani da shi don a dawo baya
|
50.
|
Alt +
Right arrow
|
Ana amfani da shi don a je gaba
|
51.
|
Alt +
Page Up:
|
Amfanin sa zuwa sama idan kuma a cikin
ms-word ne zai meda kai a shafi farko
|
52.
|
Alt +
Page down
|
Ana amfani da shi don a je kasa
|
53.
|
Ctrl +
F4:
|
Ana amfani da shi domin a rufe daftarin aikin
da ake amfani da shi kai tsaye
|
54.
|
Ctrl +
C ko Ctrl + Insert:
|
Amfanin sa kwaikwayon sifar abin da aka zaba
|
55.
|
Ctrl +
D ko Delete
|
Ana amfani da shi don a goge wani abu da aka
zaba a dauke shi zuwa ga kwandon shara
|
56.
|
Ctrl +
R ko F5:
|
Ana amfani da su ne don daidaita window
|
57.
|
Ctrl +
V ko Shift + Insert:
|
Amfanin su a ajiye abun da aka kwaikwaiyi
siffarsa (copy)
|
58.
|
Ctrl +
X
|
ana amfani dashi don a yanke wani abu da ake
bukata
|
59.
|
Ctrl +
Y:
|
Ana amfani dashi wajen maida abin da aka goge
|
60.
|
CTRL + + or CTRL + –
|
Ana amfani da su wajen kara girman wani abu,
kamar misalin kumussan da muke da su a allon farawa (start screen)
|
61.
|
Ctrl +
Mouse Scroll wheel:
|
Yana canja girman icons da ke kan destop ko
ya kara girmansu, misalin (apps pinned) na allon farawa(start screen)
|
62.
|
Ctrl + A
|
Lullube rubutu (Lighitling)
|
63.
|
Ctrl + B
|
Sanya Rubutu ya zama baki sosai
|
64.
|
Ctrl + C
|
Kwafi
|
65.
|
Ctrl + D
|
Sarrafa rubutu
|
66.
|
Ctrl + E
|
Mayar da rubutu tsakiya
|
67.
|
Ctrl + F
|
Nemowa
|
68.
|
Ctrl + G
|
Jeki zuwa ga Shafi
|
69.
|
Ctrl + H
|
Maye gurbi
|
70.
|
Ctrl + I
|
Mayar da rubutu (Itali)
|
71.
|
Ctrl + J
|
Dai – dai ta rubutu
|
72.
|
Ctrl + K
|
Nemo a cikin
|
73.
|
Ctrl + L
|
Mayar da rubutu a gefen hagu
|
74.
|
Ctrl + M
|
Matsa rubutu zuwa wani bagire
|
75.
|
Ctrl + N
|
Bude wani
sabon daftarin aiki
|
76.
|
Ctrl + O
|
Bude dakin
daftarin aiki
|
77.
|
Ctrl + P
|
Gurzawa (Print)
|
78.
|
Ctrl + Q
|
Mayar da rubutu hagu
|
79.
|
Ctrl + R
|
Mayar da rubutu a ɓangaren
dama
|
80.
|
Ctrl + S
|
Ajiyewa
|
81.
|
Ctrl + T
|
Shirya rubutun refires
|
82.
|
Ctrl + U
|
Yiwa
rubutu layi
|
83.
|
Ctrl + V
|
Ajiyewa
|
84.
|
Ctrl + W
|
Rufewa
|
85.
|
Ctrl + X
|
Daukewa ko yankewa
|
86.
|
Ctrl + Y
|
Mayar da gyara
|
87.
|
Ctrl + Z
|
Gyara
|
88.
|
Crtl + Maballi mai Kibi na hagu
|
Yana mayarda linzamin kwamfuta daga farko
ruwa Kalmar gaba
|
89.
|
Ctrl + Maballi mai Kibi na dama
|
Na
mayarda linzamin kwamfuta zuwa ga Kalmar da ake kai
|
90.
|
Ctrl + Maballi mai Kibi na kasa
|
na
mayar da linzamin kwamfuta zuwa ga wani sakin layi
|
91.
|
Ctrl + Maballi mai Kibi na Sama
|
Yana
mayar da linzamin kwamfuta farkon sakin layi
|
92.
|
Ctrl + Alt + TAB
|
suna
amfani tare da maballin mai kibiya don yawata daga cikin kowane kunshi
|
93.
|
Ctrl + Kibiya + mashayar matsawa (Spacebar)
|
amfanin
hakan don a zabi abubuwa mabambanta a kan window ko a kan desktop
|
94.
|
CTRL + SHIFT + ARROW
|
Rufe
rubutu da bular launi
|
95.
|
CTRL + ESC
|
Bude
majigi/abin kallo (monitor) (Start
screen]
|
96.
|
CTRL + SHIFT + ESC
|
Bude (Task Manager)
|
97.
|
SHIFT + F10
|
Nuna
hanyar zabin gajeruwar hanya
|
98.
|
SHIFT + DELETE
|
Gogewa
ta din-din-din ba tare da abinda aka goge ya shiga a kwandon sharaba
|
99.
|
ESC
|
Tsayarda ko dakatarda aikin da ake kai
|
100.
|
Tambarin Window + F1
|
Neman Taimako
|
101.
|
Tambarin Window
|
Nunawa ko rufe (start screen)
|
102.
|
Tambarin Window + B
|
(notification area)
|
103.
|
Tambarin Window + C
|
Amfaninsa don bude (charms)
|
104.
|
Tambarin Window + D
|
Amfaninsa don nuna ko rufe (desktop)
|
105.
|
Tambarin Window + E
|
Amfaninsa don bude (file explorer)
|
106.
|
Tambarin Window + F
|
Ana amfani dashi don bude (search charm da search for files)
|
107.
|
Tambarin window + H
|
Bude (share charm)
|
108.
|
Tambarin Window + I
|
Ana amfani da shi don bude (setting charm)
|
109.
|
Tambarin Window + K
|
Ana amfani dashi don bude (device charm)
|
110.
|
Tambarin Window + L
|
Amfaninsa don kulle/Rufe PC ko makunnin jama’a
|
111.
|
Tambarin Window + O
|
Kulle/rufe na’u’rori (device orientation)
|
112.
|
Tambarin Window + P
|
Zaben (presentation display mode)
|
113.
|
Tambarin Window + Q
|
Bude (search charm) don binciken ta ko ina ko dai-dai da kumussa (Applications)
|
114.
|
Tambarin Window + R
|
Bude akwatin (run)
|
115.
|
Tambarin Window + S
|
Bude (search charm) zuwa (search windows)
da kuma yanar gizo
|
116.
|
Tambarin Window + T
|
Yawo tsakanin kumussan mashayar task (taskbar)
|
117.
|
Tambarin Window + U
|
Bude (Ease of Access Center)
|
118.
|
Tambarin Window + V
|
Zagayawa tsakanin (notifications)
|
119.
|
Tambarin Window + Shift + V
|
Yawatawa tsakanin (notifications) ta hanyar (reverse order)
|
120.
|
Tambarin Window + W
|
Bude (search charm) da mena don gyara
|
121.
|
Tambarin window + X
|
Bude (Quick Link menu)
|
122.
|
Tambarin Window +Z
|
Ana amfani da shi don nuna umurni da ake da su ga kumussa
|
ABIN KIYAYEWA:Idan aka ce “Ctrl” ana nufin (Control),
“Alt” kuma ana nufin (Alternate) shi kuma tambarin windows (windows
logo) shi ne tambarin nan da ke kan maballan Allon Rubutun kwamfuta.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment