HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 8
*** *** ***
Kwanci tashi ba wuya a wurin
Ubangiji, saura wata biyu cif! Auren farida, bangaren Mukhtar kuwa saura kwana
biyu lokacin da aka diba masa ya cika. Wannan karon ya shiga damuwa matuka,
hatta Mom hankalin ta ya tashi ganin yadda Mukhtar ke neman fita hayyacin sa,
ka ganshi ya rame, ya dishe. Abin da ke daure ma iyayen kai kenan, sun rasa
dalilin wannan tashin hankalin da yak e shiga.
Farida kuwa text din da take
samu yanzu ya daina tada mata hankali, sai dai abin da ta kasa fahimta canjin
yanayin da take samu duk lokacin da wannan text ya shigo wayar ta.
Mukhtar yana cikin falo, ya
kasa fita yau ko zuwa office, kan shi ke masa tsananin ciwo, ya sha magani amma
duk a banza. Shi ma kan shi ya san tsananin damuwa ce,ta haifar mishi wannan. A
hankali ya lushe idanun shi ya shiga tunani kala- kala, sai dai kuma ciwon kan
sai karuwa yake balle zuciyar shi ta samu nutsuwar da zatayi tunani.
Farida ta shigo ta same shi
a haka, nan da nan hankalin ta ya tashi ta tsani taga yayan ta cikin damuwa
cikin kidima take tambayar shi “yaya lafiya? Don Allah Yaya ka...” bata ida
maganar ba sai kuma hawaye, ya shiga lallashin ta hadi da share mata hawayen da
suka zubo mata, ya dan kalleta hadi da saukar da ajiyar zuciya “farida ki daina
saurin hawayen nan kin ji ko? Ba na son kina zub da hawayen nan naki nakan kara
shiga wata damuwar kin ji?. Daga kai ta
yi alamar eh. Ya dan saukar da ajiyar zuciya yana kallon ta, ya kauda kallon da
ya ke mata hadi da komawa cikin kujerar, zuciyar shi na tattare da damuwa,
wanda sam baya son kanwar shi ta fahimta.
Farida ta gyara zaman ta
hadi da cewa, “wai don Allah yaya wace irin damuwa kake son sa ma zuciyar ka?”
ya dan yi gajeren murmushi duk da kan shi da ke mishi ciwo, “farida tunani da
kuma damuwa a yanzu sun zama mini dole, musamman da yake saura kwana biyu
lokacin da Dad suka diba mini ya cika, na so in yi karfin hali in sanya ma
zuciya ta hakuri na kasa hakura, gaskiya bazan iya wannan auren da za su hada
ba, nika dai nasan yadda zuciya ta ke ji. Ta danyi shiru sai dai tana zargin
yayan na ta anya kuwa ba wata wadda yake so? To kuma idan haka ne me zai hana
ya fito fili ya bayyana tunda ba hana shi auren wacce yake son za’a yi ba, yafi
wannan hadin auren da za’a yi masa alhali baya so, dan dama Sadiyar na matukar
kaunar shi.
Ta ci gaba da maganar da
take yi “yaya gaskiya alamomin ka sun nuna akwai wacce ka ke so, sai dai kuma
ka kasa furta hakan ga ko wace ce,. Gani na ke ba wata ‘ya mace, da zaka nuna
ka na so ta ki amince maka, sai dai wani ikon Allah na daban. Yaya
duk wannan tunanin da kake yawan tafka ma zuciyar ka ba abin da zai kara maka face
tsananin damuwa. Ka fito fili idan gaskiya da wacce
kake so ka fada, ba ka fada ba ya za’a
yi iyaye su sani balle ita yarinyar, idan ma da abin da kake shakka duk wannan
yanzu kauda shi zaka yi ka ceci zuciyar ka.
Duk maganganun da take ya
kasa cewa kala, sai wani kallon ta yake, sai dai kuma a zuciyar shi yana
jaddada maganganun ta, gaskiya ta fada, ya rasa yadda zaiyi da kanshi har yanzu
ba a bin da zai yi face neman zabi wurin Allah. Ya san wannan karon
idan ya saba ba karamar rigima za’a saka mishi ba, koda yake ba wata rigima
tunda har sun zarce hukun cin hada shi aure da Sadiya. A nan kuma
yadan yi gajeren murmushi wanda yake tattare da damuwa, har yanzu a zuciyar shi
yake maga shi dai da sun zaba ma yarinyar nan wani mijin tun da bashi kadai Allah
ya halitta ba, shifa bazai yadda da wannan hadin auren ba, tun da yana da wacce,
yake so, acewar shi ai yanzu an daina wannan, kuma ma tunda shi ba karamin yaro
bane ai ya kamata abarshi ya zaba ma kan shi. wata zuciyar ke ce mishi to ai ba
ana nufin tilas ta maka ba ne, zabi biyu ne wanda ya zama dole ka zabi daya,
idan baka yadda da auren sadiyar ba kayi tunanin wacce, zaka
aura” al’amarin ya masa zafi da yawa, shi dai auren nason zo mishi da matsaloli
barkatai.
Duk abinnan kanwar ta shi na
kallon shi, ita yanzu al’amarin shi mamaki yake bata, ganin take wannan lamarin
mai sauki ne, amma shi ya dauke shi wata babbar matsala, koda yake ba tada
tabbacin abin da ke damun shi, bata son yi mishi shishshigi cikin al’amurra
balle ta matsa masa da tambaya, sai dai ta yi alkawari ko menene zata taya shi
addu’a. mikewa ta yi ta nufi bangaren ta saboda ta tsani taga yayan hata cikin yana yi na damuwa, tana da zurfin ciki sai dai
aganin ta yayan ta yafi ta zurfin ciki duk yadda akayi akwai matsala tare da
wannan al’amari na shi. ta bar yaya mukhtar wurin, wanda ya bita da kallo.
Ta na isa bangaren nata gaba
daya daki ta shiga haka kawai ita ma bata jin dadin jikin ta, kwanci ta yi
saman gado hadi da dan rufe idanu kamar bacci ta ke, a hankali take jin faduwar
gaba, sai dada karuwa take Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un ta rika ambato ta dan samu sauki, ta shiga tunani dai dai
lokacin Usman ya kira ta, ta zura hannu ta dauki wayar hadi da karawa g a
kunne, hirarsu suke cikin natsuwa ta ma’abota soyayya tana jin dadin hirar ta
shi ba ta gajiya da sauraren muryar shi.
Cikin hirar Usman ke Cewa,
“Farida ki na jin yadda na ke ji kuwa?” tadan yi murmushi “kamar ya kenan” ita
ma ta tambaye shi , “Farida koda yaushe son ki dada karuwa yake a zuciya ta, ji
na ke kamar in matso lokacin auren nan na mu, ni gani na ke watan nan biyu sun
yimin nisa. Farida ina son ki bazan iya jure rashin ki ba kiyi min alkawari ki
so ni tamkar yadda nake son ki. Tadan yi murmushi, bai jira tace wani abu ba, sanyayyun kalaman shi ya rika gaya
mata, su na ratsa zuciyar ta, ta lunshe idanun ta, ita kadai ta san yadda take
jin dadin kalaman, ta yi tabbacin Usman ya riga ya zama wani gurbin zuciyar ta.
A karshe suka yi sallama, kwantawa ta sake yi ta rufe idanun ta kamar me bacci,
sai dai ta na tunano kalaman Usman, ya riga ya yi kyakkyawan zama a zuciyar ta.
*** *** ***
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment