AMFANIN KWAMFUTA: KIMIYYAR NAURA MAI KWAKWALWA 7



1.3 AMFANIN KWAMFUTA
Abin da zai biyo baya shine, kaɗan daga cikin amfanin kwamfuta a wannan rayuwa tamu ta yau da kullum:-
1.3.0 Sauri Mai Yawa
·       Kwamfuta ita ce mafi saurin na’ura
·       Kwamfuta na dauƙar bayanai masu girma/yawa
·       Kwamfuta na raba saurinta cikin  abinda bai cimma daƙiƙa ɗaya ba. Tana gudanar da miliyoyin lissafi cikin abin da ya ƙasa ga daƙiƙa, wanda yake idan aka misalta shi da mutum da zai ɓata watanni yana gudanar da aiki ɗaya. 
1.3.1 Dai-daito            
Bugu da ƙari kuma bayan sauri da himma da kwamfuta take dashi haka kuma tana da cikakkiyar daidaito ko ace daidaituwa kwarai da gaske.

·       Kuma kwamfuta na iya gudanar da lissafi 100% batare da samun kuskure ba.
·       Kwamfuta na iya gudanar da kowane irin aiki 100% tare da cikakkiyar daidaito.

1.3.2 Damar Ajiya
Ƙwaƙwalwa na da muhimmanci ƙwarai da gaske ga kwamfuta, ƙwaƙwalwa wata dabi’a ce mai taka rawar gani sosai ga kwamfuta.
·       Kwamfuta nada isasshiyar ma’adana fiye da ɗan adam.
·       Tana iya adana bayanai masu ɗinbin yawa.
·       Tana adana abubuwa iri daban-daban misali; hotuna, bidiyo, rubutu, sauti, da sauransu.
1.3.3 Himma ko Ƙwazo
Saɓanin mutane, ita kwamfuta bata gajiya, ba ta kuma buƙatar mataimaka wajen gudanar da aikinta.
·       Kwamfuta na aikin ta batare da tsayawaba, kuma ba tare da kawo kowane irin matsala ko rashin jin shauƙi ga aikin da take gudanarwa ba.
·       Ta na kuma iya maimata aiki ɗaya batare da naƙasa ko gajiyawa ba.
1.3.4 Rashin Ƙasawa
Kwamfuta na’urace wacce bata ƙasawa
·       Kwamfuta na’urace wacce bata ƙasawa a wurin gudanar da ayyuka ko kuma wajen tafiya daidai.
·       Na’urar tana iya wanye ko daidaita matsalolin da suka shafi fannoni iri daban-daban.
·       A lokaci guda, zata iya kuranye  ko kawar da matsala maigirma da ta shafi harkar kimiyya, kuma a wannan halin kana iya yin wasa (game) da ita.


1.3.5 Aminci
Kwamfuta na’ura ce amintacciya ko abin amincewa.
·       Kwamfutocin zamani yardaddune wajen rashin yawan kawo matsala, suna ɗaukar lokaci mai tsawo ba tare da sun kawo wata matsala ba.
·       Na’urar kwamfuta anyitane don abubuwasu sauƙaƙa.
1.3.6 Aiki da kai
Kwamfuta na’ura ce dake iya gudanar da aiki ita kaɗai ko kuma ince aiki da kanta.
·       Aiki da kai yana nufin tana da damar gudanar da aiki ita kaɗai ba tare da mataimaka ba idan har an shiryamata aikin kuma an bata umurnin yin haka, ma’ana idan ta adana bayanin da aka bata a cikin ƙwaƙwalwarta shi zai bata damar aiwatar da aikin ba tare da mutum ya taimaka mata ba.
1.3.7 Raguwar aiki da takarda
Aiki da kwamfuta don adana muhimman abubuwa a ma’aikatu na zama sanadiyyar rage wanzuwar aiki da takardu da kuma saurin gudanar da aiki a cikin ƙanƙanin lokaci.
·       Idan an adana bayanai a cikin na’ura mai aiki da wutar lantarki zasu zauna ne har sai lokacin da aka nemesu don ayi amfani da su. Kunga kenan kamata ya yi makarantu su nemawa kansu da kansu sauƙi ta wajen aiki da kwamfuta idan zasu ɗauki sabbin ɗalibai. Don haka matsalar tara tari-tarin fiyil zai ragu.

1.3.8 Sauƙi Wajen Kashe Kuɗi
·       Koda yake a farkon jari a harkar kasuwanci, sanya kwamfuta abu ne mai wahala amma yana kuma kawo sauƙi wajen zirga-zirga da kuma kawo cigaba wajen harkar tattalin arziki.

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment