HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 12
Bai boye ma ta ba ya gaya ma ta yadda suka yi da mahaifin shi, tsorace ta kalleshi, jin cewa idan ma ta aure shi ba ita kadai ceba, hawaye suka shiga zubo mata Usman din da ta kallafa rayuwar ta, kenan, wani kishin kuma ya tattaro yake kokarin dunkule zuciyar ta.
A hankali ta shiga yi masa Magana cikin tattausar muryar, wanda tun zuwanta wurin sai yanzu ta iya furta wani abu, “Usman ka daina wannan zance tunda Allah ya riga ya hukun ta niba matar ka bace” Sai da gaban shi ya fadi jin maganar da ta furta, zazzare ido ya yi kamar wani sabon kamun hauka, nan danan kuma wasu sirarrun hawaye suka zubo mishi bai yi zaton zai samu matsala a wurin ta ba, shi dai son na ta na neman azabtar da shi. “Farida ya zaki ce haka? Don Allah farida kada ki ki ni lokaci daya, ki tallafi rayuwa ta ban....” Dakatar da shi ta yi lokaci daya zuciyar ta wani zafi take mata, saboda raradin kaunar shi dake neman dada karuwa gareta. Ta dan share hawayen da suka zubo ma ta.
Ya rasa dalilin da yasa take kokarin kawo musu hukunci daban a tsakanin su, sai ganin ta yi gwiwa bibiyu ya gurfana yana rokon ta duk kada ita ma tace ta fasa auren shi. “usman ka dai na gurfana min bana son irin haka kai ne babba a gareni bai dace kayi hakan ba, ta dan yi shiru sai kuma a hankali ta ci gaba, “shin da gaske ne kana kauna ta? Tambayar ta dirar mishi a bazata ya ji ta wani banbarakwai. “ Farida ba sai na gaya miki ba ni kaina ban san tsananin kaunar da na ke miki ba ni ka dai nasan yadda na ke ji” ta ci gaba, “tunda haka ne ka nuna min kaunar da ka ke yimin, ta hanyar yimin alfarma daya, amma sai ka yi alkawarin zaka yimin wannan alfarma.” Ba musu yake cewa, “ki fada farida na yi mikin alkawarin insha’Allahu ko raina ki ke bukata zan sallama miki in dai hakan zai faranta miki rai,” na gode”, tace mishi sannan ta ci gaba da cewa “Usman ba wani abu bane face ka faranta ran iyayen ka hadi da biyayya ga zabin da suka yi maka, ka karba, ka rika amana hannu bibiyu, hakan ba karamin farin ciki zai sanya musu ba.
Usman nasan har yanzu Baba ba zai so auren nan nawa ba, tsananin tausayayin ka ne yasa ya amince maka har da ka hada auren mu mu biyu. Ka yi hakuri idan Magana ta tayi maka zafi, ka gafartamin, ba abinda zan so kayi bayan wannan. Usman don Allah kayi wannan biyayyar ka gani, nasan zata zamo maka alheri, a rayuwa. Kasan ita biyayya lokacin da da ya yi ma iyayen sa, kai ko ba iyayen sa bane biyayyar bata faduwa banza. Kasa ce ma ta ko mai ya yi gaskiya ta kara sanya shi cikin wani tashin hankali, jin maganganun ta baya da niyar can za ra’ayi alhali yana matukar son ta. A hankali har yanzu magar tata ke fitowa cikin muryar ta mai dadin sauraro, “Usman” ta kira sunan shi ya dago kai yana kallon ta suka hada ido, bata son suna saurin hada idanu ita kadai tasan yadda hahan ke haifar mata, ta tausaya mishi amma a ganinta gara a ce sun bi umurnin iyayen su mhm. Ta dan saukar da ajiyar zuciya hadi da dan sunkuyadda kai sannan ta ci gaba da cewa,”nasan duk wannan zaka yi tunanin na daina son ka,” lokacin kuma hawaye suka dan tararo mata bata kula da ta share ba, ta ci gaba da maganar ta “Usman inaa son ka hadi da kaunar ka bazan boye maka ba, usman son ka ya riga yamaye duk wani gurbi da kake zato a zuciya ta, ina tausayin kaina, Usman ina son ka in kara jaddada maka son da banyi zaton zan sake yima wani da namiji irin sa ba.
Tsananin son da nake maka ne har ya haifarmini da kaunar ka, har nake jin zuciya ta ta yi sallama da duk wata soyayya idan ba taka ba. Ina son duk wani abin da kake so, sai dai kuma bazan taba son abin da zaisa ka bijirewa iyayen ka ba. Hmm saboda haka a ganina ya kama ta mu hadu mu hakura da juna, insha, Allahu wannan zai zamo alheri a garemu da fatar zumuncin mu bazai yanke ba.”? Ita ma kanta tasan karfin hali tayi da ta furta wannan magana don sai da zuciyar ta ta girgiza, tasan abu ne mai wuya ta iya cire Usman a zuciyar ta, wani dan siririn kuka ta fara yi, ita ma kan ta bata san lokacin da kukan ya zo mata ba, ta riga ta gama Magana ta san kuma shima yanzu yana da maganar yi, amma gudun kada ya lallabe ta da kalaman shi masu ratsa mata zuciyar ta yasa tayi, saurin mikewa tsaye, da sauri ta kama hanyar shiga gida, kiranta yake, amma taki tsayawa bata son biye mishi ta riga ta yanke ma kansu hukun ci a ganin ta hakan zai fi musu.
Ya jima wurin tsaye, ya kasa dagawa da wurin duhu- duhu ya rika gani sai kuma tsananin ciwon kai da ya karu ga reshi, ya rasa inda zai saka kan shi. To wai me yasa zata yanke wannan hukunci alhali yana da tabbacin tana son shi 100%, ya kudiri niyyar shifa ba zai fasa auren ta ba, bai hana idan baya numfashi ba. Haka ya fito dakyar, cikin tsarin Ubangiji ya isa gida lafiya.
Tana shiga gida sashenta ta nufa, kwanci tayi kan gado tana darzar kuka, nan kuma ta daina kukan ta shiga neman taimakon Ubangiji da ya sa hakan ya zamo mata alheri. Sai dai kam sai wani ikon Allah zai sa ta daina son Usman. Mom din ta ce ta shigo dakin, ta shiga yi mata nasiha saboda ta samu ta kwantar mata hankali, farida ta dan yi murmushin karfin hali ganin hankalin Mom din ta a tashe, “ba komai mom, wannan duk cikin hukunci ne na Ubangiji.” Mom din ta ji dadi ganin ‘yar ta bata dauki al’amarin da zafi ba, koda yake ta riga ta san ‘yar ta Allah ya riga ya hore mata hakuri, ta shiga sa mata albarka.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment