Welcome to Ramadan 2018



AZUMI DA FALALA

https://i.ytimg.com/vi/PpxNRTdN3u0/maxresdefault.jpg


Ramadan 2018 will begin in the evening of
Tuesday
,
15 May
and ends in the evening of
Thursday
,
14 June
  Insha Allah






SHARAHBIL MUHAMMAD SANI


Copyright © Sharhamak, 2015
Hakkin Mallaka © Sharhamak, 2015

27th Sha’aban 1436AH
15th June, 2015CE
 

GODIYA
Auzu Billahis-Sami’ul Alim, Minash-Shaidanir Rajim. Bismillahir Rahmanir Rahim.
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki kuma aminci ya tabbata a bisa zababben jakada Shugaban Annabawa Muhamamd Dan Abdullahi wanda aka saukarma fiyayyen littafi (al-kur’ani) domin ya zama shiriya da kuma waraka ga muminai.
Yarda da aminci su kara tabbata a bisa iyalan gidansa da sahabbansa da kuma muminai har ya zuwa ranar karshe.
Bayan haka: Lalle Allah madaukaki Ya kimtsa mini kuma Ya taimakeni akan na tarawa kaina day an uwana wani abu na daga fadakarwa kan babban bakon da zai ziyarcemu a cikin yan kwanakin nan da basu wuce biyu ko uku ba.
Hakika na cirato wasu bayanai daga maganganun wadansu malamai tare da ayoyi da hadisai don ganin na cinasarar tsara wannan littafi. Ina yiwa dukkan wadanda nayi amfani da wani abu nasu ta hanyar kafa hujja godiya da kuma fatar Allah Ya biyasu Ya amfanar da su da ni da kuma Al’uma daga wannan littafi amin.
Ina mika godiya tag a iyayena wadanda sune suka bani tarbiyya har zuwa ga wannan hali da na tsinci kaina a cikinsa, ina rokon Allah Ya raya mu tare da su Ya kuma kyautata rayuwarsu da mu Ya yiwa rayuwar albarka amin.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
WASALLALLAHU ALA NABIYI AL-KARIM
WATAN RAMADAN
Allah madaukaki Yana cewa a cikin al-kur’ani: “Shi ne wanda Ya sanya muku rana babban haske da wata mai haske, kuma Ya kaddara shi ga Manziloli domin ku san kidayar shekaru da lissafi. Allah bai halitta wannan ba face da gaskiya, Ya bayyana ayoyi daki-daki domin mutane wadanda suke sani”. (Suratul Yunus).
Allah Ya halicci wata ne don mu san farko da karshen watanni ta hanyar ganin shi. Wata yana kwana talatin ne (30) ba ya karawa akan hakan, kamar yanda yake iya yin kwana ishirin da tara (29) baya kasawa ga hakan don haka yana da muhimmancin gaske ga kowane musulmi yasan wadannan watannin musulunci kamar yanda zan zano manasu. Wadannan sune ake cewa watannin hijiriyya ko hilaliya ko kuma kamariya, kuma wadannan watannin su goma sha biyu ne.
1.   Al-Muharram
2.   Safar
3.   Rabi’ul Auwal
4.   Rabi’ul Sani
5.   Jimadal Ula
6.   Jimadas Saniya
7.   Rajab
8.   Sha’aban
9.   RAMADAN
10.                        Shawwal
11.                        Zul-Ka’ada
12.                        Zul-Hijja
Zamu ga cewa daga cikin wadannan jerin gwanon watannin akwai wani wata mai suna RAMADAN wanda ya ke shine wata na tara kuma a cikinsa ne aka wajabta yin azumi ma’ana a azumci watan gaba dayansa.
MENE NE AZUMI?
A yaren Larabci, shi ne kamewa daga barin ko mene ne, kuma akan yi amfani da kalmar akan ko wane irin kamewa kamar yadda Allah (S.W.T) ke bada labari akan Maryam (A.S) inda ta ke cewa “Lallai ni na yi alwashi ga Allah mai rahama zan yi azumi”. (Suratul Maryam aya ta 26).
AZUMI A SHARI’ANCE
Shi ne kamewa daga abubuwa kamar Ci da Sha da kuma Saduwa da iyali tun daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana tare da niyyar bautawa Allah Maigirma da daukaka.
Za a iya bashi wannan Ma’anar: Azumi shi ne niyar azumtar dukkan kwanakin watan RAMADANA ta fuskar nisantar ababen da ke bata azumin wadanda dukkansu suna komawa ne ga ababe uku ne kamar haka:
·       Barin cin duk wani nau’in abinci ko abin da ke cikin hukuncin shi, amma ababen da basu da hukuncin abinci kamar aswaki ko kwalli ko saka turare ba su bata shi.
·       Barin nau’ukan abin sha ko abin da ke da hukuncin abin sha kamar taba amma abin da ba shi da hukuncin abin sha kamar wanka ko yawu ba ya cutar da azumi
·       Nisantar tarawa da iyali ko duk wani abu wanda ke motsar da sha’awa, amma sumbantar iyali ko rungumarsu ba ya bata azumi, duk da ya ke abin da ya fi shi ne nisantar hakan.
Azumi yana daga cikin mafi girman da’a kuma Allah Yana bada lada mara iyaka ga mai yin azumi, da azumi ake yin gafarar zunuban da suka gabata kuma Allah Yana nisantar da fuskar mai yin azumi daga barin wuta, kuma Yana cancantar da shigarshi aljanna. Muna rokon Allah Ya sanyamu daga cikin wadanda zai yanta a cikin wannan wata na ramadana amin.
KASHE KASHEN AZUMI
Azumi Ya kasu kashi biyu kamar yadda zan zayyana mana su kamar haka:
·       Akwai azumi na wajibi (Dole ke nan)
·       Akwai azumi na nafila (Wanda ba dole ba ko kuma a ce na neman lada yanda wadansu ke cewa)
Azumin wajibi ma’ana wanda yake dole kenan shi ma ya kasu kashi uku.
·       Akwai wanda yin shi dole ne a wani lokaci ayyananne shi ne watan Ramadana
·       Akwai wanda yake dole ne saboda wani (illa) wato dalili wanda yake wajabta kamar kaffarar zihari ko na kisan kai akan kuskure ko na rantsuwa da sauransu.
·       Akwai wanda yake wajibi ne ta hanyar mutum ya lizimtawa kansa yin azumi (kamar alwashi).
HUKUNCIN AZUMIN WATAN RAMADANA
Hukuncin yin azumin watan Ramadana wajibine ga kowane Musulmi baligi mai hankali lafiyayye mazaunin gida kuma rukuni ne daga rukunnan musulunci. Littafin Allah (Al-kur’ani) da sunna sun tabbatar da haka tare da ijima’in malamai.
Allah maigirma da daukaka ya ce “Ya ku wadanda su kayi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabaceku ko kwaji tsoron Allah”. (Suratul Bakara aya ta 183).
Manzon Allah (S.A.W) ya ce “An gina Musulunci akan abubuwa guda biyar.
1.   Shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammadu (S.A.W) Manzon Allah ne
2.   Da tsayar da Sallah
3.   Da bayar da Zakka
4.   Da kuma aikin Hajji
5.   Da Azumtar watan Ramadana (Bukhari ya ruwaito shi Hadisi na 8 da Muslim Hadisi na 16 daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda dashi)
Wani Balaraben kauye yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) kanshi a cukurkude ya ce “Ya Manzon Allah (S.A.W) bani labarin abin da Allah Ya farlanta a kaina na azumi?” sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Azumin watan Ramadan sai dai kuma in ka so ka yi azumin nafila”. (Buhari Ya ruwaito shi Hadisi na 50 da Muslim Hadisi na 9 daga Dalhatu dan Abdullahi (Allah Ya yarda dashi).
Malaman Musulunci sun yi ijima’i akan cewa, azumi rukuni ne daga cikin rukunnan Musulunci sanannu a cikin addini. Kuma Malamai sun tabbatar da cewa ana iya kafirta wanda duk ya yi musun azumtar watan Ramadan kuma azumin baya faduwa akan kowane balagagge mai hankali sai dai da wani uzuri daga uzurorin shari’a wadda ta ke abin lura. (Al-Ifsah na Ibnu Hubaira) Mujalladi na 1 shafi na 232 da (A-Mugny na Ibnu Kuddama) Mujalladi na 3 shafi na 285 da (Al-Majmu’u na Imamun Nawawi) Mujalladi na 6 shafi na 252.      
SAHUR
Abincin da mai azumi yake ci kafin bullowar Al-Fijir shi ake cewa (Sahur) kuma yana da kyau a jinkirta shi har kusan bullowar Al-Fijir. Wannan kuwa abinci ne mai muhimmanci ga mai azumi don zai ba mai azumi karfi.
Haka kuma yana kamata ga mai azumi a nan ma a lazimci ladubban musulunci lokacin yin Sahur kamar haka: Ya ce “Bismillahi” Ya ci da hannun dama kuma Ya ci gabanshi.
BUDA BAKI
Abin da mai azumi yake ci bayan faduwar rana shi ake cewa (Buda Baki). Yana da kyau mai azumi ya gaggauta buda baki bayan faduwar rana kada ya jinkirtar da yin buda baki har zuwa Sallar Isha’i kamar yanda masu akidar Shi’a su ke yi.
ABUBUWAN DA AKA FI SO A BUDA BAKI DA SU
Misalin abubuwan da aka fi so a yi buda baki da su: Ya halatta a bude baki da dukkan abincin da ya ke halal, duk da yake ana son a bude baki da (DANYEN DABINO) idan bai samu ba sai a yi da (BUSASSHEN DABINO) idan shima bai samu ba sai a bude baki da (RUWA KO WASU YAYAN ITATUWA). Kuma ana son a lazimci ladubban cin abinci wadanda musulunci ya tanada kamar yadda na fada a inda ya gabata wurin yin SAHUR.
FALALAR AZUMI DA FA’IDOJINSA
An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Duk wanda ya azumci watan Ramadana yana mai imani, yana mai neman lada. To, an gafarta masa zunubansa wanda ya gabata. (Bukhari ya ruwaito shi hadisi na 1900 da Muslim Hadisi na 760).
An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Idan watan Ramadana ya shigo ana bude kofofin sammai kuma ana rufe kofofin wuta, ana kuma daure Shaidanu. (Bukhari ya ruwaito shi Hadisi na 1899 da Muslim Hadisi na 1079)
An karbo daga Sa’ad dan Sa’ad (R.A) ya ce “Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Lallai a cikin aljanna akwai kofofi guda biyu ana kiransu da suna ARRAYYAN babu wanda zai shige su sai su (wato masu azumi). Za a ce ina masu azumi? sai su mike sai a ce babu wanda zai shige ta wanda basu ba, idan suka shiga sai a rufe kofar aljannar. Ba mai shiga wannan kofa ta ARRAYYAN sai masu azumi”. (Bukhari ya ruwaito hadisin 1896 da Muslim Hadisi na 1152).
Daga Abu Huraira (R.A) ya ce Manzon Allah (S.A.W) “Salloli biyar daga Juma’a zuwa Juma’a da kuma Ramadana zuwa Ramadana suna kankare abin da ke tsakaninsu idan sun nisanci manyan zunubai. (Muslim ya ruwaito shi Hadisi na 233).
An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce “Lallai Manzon Allah (S.A.W) ya ce”. “Allah Maigirma da daukaka ya ce”. “Dukkan ayyukan Dan Adam nasa ne (ma’ana na mai aikin ne) amma banda azumi. Domin azumi nawa (ma’ana azumi na Allah ne) kuma Ni ne zan yi sakayya ga mai yin azumi, domin azumi garkuwa ne. duk ranar da mutum ke yin azumi baya zina baya daga murya kuma baya yin wauta don idan wani ya zage shi ko ya neme shi da fada lallai ya ce ni ina yin azumi (sau biyu) Manzon Allah (S.A.W) ya ce na rantse da wanda raina yake a hannunsa warin bakin mai azumi yafi kamshi a wajen Allah ranar kiyama daga kamshin turaren almiski, kuma mai azumi yana da farin ciki guda biyu da zai yi farin ciki dasu lokacin da yake buda baki zai yi farin ciki da lokacin da zai hadu da ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa”. (Bukhari ya ruwaito shi Hadisi na 1904 da Muslim Hadisi na 1151).
Babban Malami Abu Amr Ibnu Abdul-Barri Al-Maliyy (Allah Ya yi masa Rahama) ya ce “Fadin Manzon Allah (S.A.W) azumi nawa ne ni zan yi sakayya da shi”. Ya ce “Wannan ya isa falala ga azumi akan sauran ibadoji sai dai ya ce Malamai sun yi sabani akan abin da Allah (S.W.T) ya ke nufi da azumi nawa ne, ni zan yi sakayya dashi tare da cewa kowane aiki nashi ne (wato Allah S.W.T) kuma shi ne yake yin sakayya da shi, sun yi sabani mai yawa (wato manyan malamai) na farko sun ce domin azumi riya ba ta shiga cikinsa kamar yadda yake a cikin ayyuka. Imamul Kurdubi (Allah Ya yi masa Rahama) ya ce “da yake ayyukan riya tana shiga cikinsu. To, amma azumi babu riya a cikinsu. Domin shi aikin ana yin shi ne tsantsar shi ga Allah (S.W.T) shi ya sa Allah Ya jinginashi zuwa gareShi (wato Shi ne ya ce azumi nawa ne, Ni ne zan yi sakayya da shi). (Daga Asarabul Muhibbina Fi Ramadan Na Muhamamd Hussaini Yakub Shafi na 18).
 Al-Hafiz Ibnu Rajab Al-Hambali (Allah Ya yi masa rahama) ya ce “Malamai sun yawaita maganganu akan ma’anar fadin Manzon Allah (S.A.W) idan ya ce Allah (S.W.T) ya ce azumi nawa ne zan yi sakayya da shi. Ya ce Malamai sun ce, lallai azumi shine raba zuciya da sha’awoyinta na asali wanda Allah Ya dabi’anceta akan su  karkata zuwa ga Allah (S.W.T) ya ce ba a samun wannan a sauran ibadoji sai dai azumi kawai.
Na biyu suka ce “Lallai azumi sirri ne tsakanin bawa da Allah (S.W.T) babu wata ibada da ked a wannan kuma niyya ce ta boye kuma ba mai iya tsinkayar wannan sai Allah, kuma ya bar sha’awarsa wadda adabi’ance da al’ada shi yasa babu riya a cikinsa ta inda mutum yana barin abin da zuciyarsa ta ke kiransa zuwa gareshi na son sha’wa babu wanda ke iya tsinkayar wannan sai Allah (Lada’iful Ma’arif Na Ibnu Rajab Al-Hambali Shafi na 209 – 212).
Idan mai azumi zai iya tafiyar da dukkan lokacin shi a cikin ambaton Allah, abu ne mai kyau. Kamar karatun Al-kur’ani, sadaka, magana mai kyau, kyawawan halaye da kuma rokon Allah har zuwa lokacin buda baki.
Ibn Abbas (R.A) yana cewa: “Manzon Allah (S.A.W) yafi kowa kyauta kuma kyautar shi ta fi yawa a cikin watan Ramadan lokacin da Mala’ika Jibril yake haduwa das hi kuma Jibril ya kasance yana haduwa da shi cikin kowace rana ta Ramadan domin ya yi bitar Alkur’ani da Manzon Allah (S.A.W) kuma Wallahi Manzon Allah (S.A.W) ya fi iska mai gudu kyauta.
Kuma bayan shan ruwa da sallar Isha’i yana da kyau a yi sallar Asham tare da musulmi; domin a kasance daga cikin masu samu ladan rana da daren watan Ramadan.
MUHIMMANCI DA WAJABCIN AZUMI
A watan Ramadana ne ayoyin Al-kur’ani na farko suka sauka: Allah Ya na cewa “Watan Ramadana ne wanda aka saukar da Al-kur’ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To, wanda ya halarta daga gareku a watan sai ya azumce shi”. (Suratul Al-Bakrah).
Kamar yadda yake a bayyane Allah Ya umurci muminai da su azumci wannan watan gaba dayan shi domin su godewa Allah game da ni’imar wannan al’kur’anin da ke kunshe da shiriya da dadin kai ga talikai.
Idan namiji ya balaga ma’ana idan ya kai shekaru 15 ko gashi ya fara tsirowa a gabansa ko ya ga maniyi a jikinsa to wajibi ne ya azumci wannan wata.
Haka ne itama mace idan ta kai shekarun balaga ko ta ga jinin al’ada ya zama wajibi akan tat a azumci wannan wata.
Kuma Manzon Allah (R.A) Ya kara mana bayani game da shi wannan azumin inda ma har ya sanya shi daya daga cikin rukunnan musulunci biyar. Don haka wajibi ne a kan baligi ya azumce shi gaba daya domin ya samu falalar azumtar shi kuma ya kubuta daga ukubar Allah akan wanda ya sha azumin wannan watan ba tare da uzuri ba.
Amma game da yaro wanda bai balaga ba, ba dole ba ne ya yi azumi ba. Duk da yake ya kamata musulmi su horar da yayansu game da yin azumi don su saba, don kada ya basu wahala idan sun girma.
Hakika duk lokacin da musulmi suka iske kansu a cikin watan Ramadan, rayuwa takan sauya sukan koma ga Allah ta wajen gudanar da ayyukan da’a. wadanda suke jin nauyin yin Sallah sukan motsa su rika yin ta a kan lokaci cikin jama’a, masu sharholiya sukan rage ko su bari baga daya. Saboda an daure shaidanu masu ingiza mutane ga sabon Allah.
Wannan duk albakarcin saukar da Al-kur’ani ne a cikin watan Ramadana domin da azumin watan Ramadan din da sauran ayyukan da’a duk sun biyo bayan saukar Al-kur’ani ne. saukarsa ce ta kawo duk wasu ayyukan alkhairi da da’a dad an adam ke gudanarwa har zuwa yau ya alla a cikin watan Ramadana ne ko a wanin watan ne na daban.
Kuma Al-kur’ani Maigirma ya bamu labarin dalilin wajabta yin azumin a cikin fadar Allah madaukaki “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi akanku kamar yadda aka wajabta shi akan wadanda suke a gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa. Kwanuka ne kidayayyu. To, wanda ya kasance daga gareku majinyaci ko kuwa yana a halin tafiya sai ya biya adadi daga kwanuka na daban. Kuma akan wadanda suke yinsa da wahala akwia fansa; ciyar da matalauci sai dai wanda ya kara alkhairi, to, shi ne mafi alkhairi a gareshi. Kuma ku yi azumin da wahalar ne mafi alkhairi a gareku idan kun kasance kuna sani”. (Bakara 83 – 84)
Fa’idojin da zamu samu daga wadannan ayoyi biyu suna da yawa, daga ciki akwai:
1.   Wanda ya samu kansa a cikin watan Ramadana yana cikin hankalinsa kuma baligi. To, azumtarsa wajibi ne a kansa (Jami’ul Bayan Mujalladi na 3 Shafi na 454).
2.   Azumi yana daga cikin sabubban samu da ginuwar takawa a zukatan mutane
3.   Mai azumi yana tarbiyyantar da kansa ne kan tsoron Allah da kiyaye dokokinSa (Allah). Ta barin abin da zuciyarsa ke so ko sha’wa alhali zai iya boyewa ya aikata, amma sai ya ki saboda ya san Allah Yana ganinsa.
4.   Azumi yana takaitawa ko toshe magudanar shaidan. Domin Shaidan yana gudana ne a jikin dan adam kamar yadda jini ke gudana. To, ta hanyar azumi sai a raunana ikon gudanarsa sabo ya ragu.
5.   A galibi mai azumi ayyukansa na da’a na karuwa ayyukan da’a kuwa suna daga cikin siffar takawa.
6.   Idan mawadaci ya dandani wahalar yunwa, hakan zai karfafa masa gwiwar ya taimakawa talakawan da basu da, wannan ma siffa ce ta takawa.
7.   Allah Ya yi wa marasa lafiya da matafiya rangwame su ci abinci. To, amma saboda irin maslahar da ke cikin azumi ga kowane musulmi, sai ya zamo Ya umurce su da su rama abin da suka bari a wasu kwanuka na daban, lokacin da ciwon ya warke ko aka dawo daga tafiya aka samu hutu. (Alfawa’id Mujalladi na 2 Shafi na 272).
8.   Azumi yana hana jindadi da sha’awoyin da zuciya ke ji, fiye da yadda sauran ibadoji suke iya hanawa.
9.   Azumi sirri ne tsakanin bawa da ubangijinsa, babu mai riskar hakikaninsa sai Shi (Allah), don haka ne Allah Ya ce naSa ne Shi zai saka a kansa, sabanin sauran ibadoji na zahiri.
Sai aya ta gaba inda Allah Ya fayyace a wane wata za a yi azumin cikin fadin Allah madaukaki “Watan Ramadana ne wanda aka saukar da Al-kur’ani a cikinsa, yana shiryarwa ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To, wanda ya halarta daga gareku a watan sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban, Allah Yana nufin sauki a gareku kuma ba Yana nufin tsanani gareku ba kuma domin ku cika adadin kuma ku girmama Allah akan Ya shiryar da ku, kuma tsammaninku zaku gode”. (Bakara aya ta 185)
Haka kuma akwai Hadisai da suke da nasaba da wannan aya kamar:
Daga Abu Huraira (R.A) ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa (Bukhari da Muslim)
Daga Abu Huraira (R.A) cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Wanda ya yi tsayuwar Ramadan yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa”. (Bukhari da Muslim)
Daga Jabir bin Abdullahi (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Ku rika cin gajiyar saukin da Allah Ya yi muku (ma’ana matafiyi ya sha azumi ya rama)” (Muslim)
Daga Muhajjinul Aslamiyyu ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Lallai mafi alkhairin addininku shi ne mafi saukinsa”. (Bukhairi)
Daga Anas bin Malik (R.A) ya ce “Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Ku saukaka, kada ku tsananta, ku zaunar kada ku kora”. (Bukhari)
A wannan aya fa’idojin da zamu samu sun hada da:
1.   Falalar watan Ramadan saboda saukar Al-kur’ani a cikinsa da kuma kebe shi da daren lailatul kadr. (Jami’ul Bayan Mujalladi na 3 Shafi na 448)
2.   Wajabcin azumtar Ramadan akan daukacin mukallafai (Tafsirul Kur’anin Azim Mujalladi na 1 shafi na 206)
3.   Sauki ga marasa lafiya da matafiya kan su ci su sha a watan Ramadana da wajabcin rama abin da suka sha (Fathul Kadir Mujalladi na 1 shafi na 281 – 282)
4.   Saukin shari’ar Musulunci da rashin tsananinta (Tafsirul Kur’anil Azim Mujalladi na 1 shafi na 206)
5.   Shar’anta yin kabbarori a daren Idi da Ranarsa domin godiya ga ni’imar Allah ta samun shiriya da Musulunci.
Shi kuma aya ta gaba na cewa: “Kuma idan bayiNa suka tambaye ka daga gareNi, to lallai Ni makusanci ne. Ina karba kiran mai kira idan ya kiraNi, saboda haka su nemi karbawaTa, kuma su yi imani daNi tsammaninsu, su shiryu”. (Bakara aya ta 186)
Kasancewar mai azumi yana neman kusanci ga Allah ne da rokonSa shiriya da sauran alkhairai sai Allah Ya nuna cewa Shi makusanci ne ga masu kiranSa, amma da sharadin su nemi karbawarSa bayan sun yi imani da Shi. Akwai Hadisai da dama da suke da alaka da abin da ayar take magana, daya daga ciki shi ne Hadisin Abu Haraira (R.A) da ya ce “Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Lallai Allah Yana cewa: “Ina inda bawaNa yake zatoNa, kuma ina tare da shi idan ya kiraNi.” (Muslim ya ruwaito shi) Fa’idojin wannan aya sun hada da:
1.   Shar’antawa da mustahabbacin yin addu’a. (Taisirul Karimur Rahman Shafi na 69)
2.   Kusancin ubangiji ba ya lizimtar cudanya, a’a Allah makusanci ne a cikin daukaka.
3.   Makaruhancin daga sauti a lokacin ibada, face wadannan ibadu kamar haka:
i.                   Talbiyya
ii.                Kiran Sallah
iii.              Da ikama (Aisarut Tafsir Mujalladi na 1 shafi na 165)
4.   Wajabcin amsawa da mika wuya ga umurnin Allah. (Jami’u Ahkamil Kur’an Mujalladi na 2 shafi na 313)
5.   Amsa kira da bin umurnin Allah yana gadar da shiriya da dacewa. (Taisirul Karimir Rahman shafi na 69).
Aya ta gaba kuma sai ta ce “An halatta a gareku a daren azumi yin tarayya zuwa ga matanku, su tufa ne a gareku, kuma tufa ne a garesu, Allah Ya sani lallai ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karbi tubarku kuma Ya yafe muku. To, yanzu ku rungume su, kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku. Kuma ku ci ku sha har silili far ya bayyana a gareku daga silili baki daga alfijir, sannan ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu I’itikafi a cikin masallatai. Wadannan iyakokin Allah ne: don haka kada ku kusance su, kamar haka ne Allah Ya ke bayyana ayoyinSa ga mutane tsammaninsu za su yi takawa”. (Bakara 187)
Allah mafi girma! Dubi yadda ayar farko an rufe ta da takawa, haka kuma dubi yadda aka rufe aya ta karshe da batun takawa bayan Ya yi magana kan abubuwan da aka halatta ga mai azumi da dare. Wannan yana nuna kashin bayan yin azumi shi ne a samu takawa.
Fa’idojin da wannan aya take koyarwa sun hada da:
1.   Halaccin ci da sha da tarayya a dararen azumi bayan ya kasance haramtacce idan aka yi barci a baya. (Jami’ul Bayan Mujalladi na 3 shafi na 464).
2.   Lokacin azumi ana faraway ne daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana. (Aljami’u Li’ahkamil Kur’an Mujalladi na 2 shafi na 319).
3.   Ana son yin amfani da kinaya maimakon bayyanawa baro-baro a abin da akwai kunya a cikinsa. (Aljami’u Li’ahkamil Kur’an Mujalladi na 2 shafi na 315)
4.   Shar’anta I’itikafi a cikin watan Ramadana da yankewa daga mutane domin yin ibada. Kuma mai I’itikafi bai halatta a gareshi ya  ji dadi da matarsa har sai lokacin da I’itikafinsa ya kare. (Tafsirul Kur’anil Azim Mujalladi na 1 shafi na 213).
5.   Haramcin keta hurumin shari’a da ke tare haddodinta. (Tafsirul Kur’anil Azim Mujalladi na 1 shafi na 213)
Bayyana makasudin saukar da shari’o’I da sanya haddodi wato takawa ga Allah madaukaki. (Ruhul Ma’ani Mujalladi na 2 shafi na 69) 
ABUBUWAN KI GA MAI AZUMI
Idan musulmi yana cikin halin azumi ya kamata ya nisanci dukkan abin da ya kasance haram ko makaruhi; ya nisanci fasikanci da maganar alfasha da daga murya a cikin magana da hayaniya ko da wani ya neme shi da fada ya ce da shi “Ni mai azumi ne”.
Kamar yanda ya zo a cikin Sahih Bukhari Manzon Allah (S.A.W) yana cewa “Wnda bai bar magana zur ko aiki da shi ba, Allah ba ya bukatar wannan mutum ya bar abincinsa da abin shansa”.
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Azumi garkuwa ne don haka mai azumi ya nisanci fasikanci da jahilci, idan wani ya ya keshi ko ya zage shi ya ce da shi; “Ni mai azumi ne”. (Bukhairi ya ruwaito shi)
UZURI LOKACIN AZUMI  
Idan mai azumi ya ci abinci da mantuwa ko kuma ya sha wani abin sha, to ya cigaba da azuminsa kuma ba zai ranka ba bayan Ramadana.
Kuma haka ne ma idan mutum ya kasance bai sani ba sai ya ci ko ya sha, sai da ya kammala azuminsa idan ya samu sani; saboda shi ma jahilci uzuri ne karbabbe a cikin musulunci.
Wannan kuwa duk daya ne; da wanda bai san hukuncin ba, ko kuma ya jahilci shigar lokaci ko fitar shi kuma shi ma ba zai ranka wannan azumin ba a bayan Ramadana.
Kuma haka ne idan aka tilasta mutum ya ci ko ya sha saboda tilastawa uzuri ce karbabbe.
Haka ma mai barci idan ya yi mafarki kuma maniyi ya zubar mishi sai ya yi wanka ya cigaba da azuminsa.
Haka ne idan mutum ya kasance a cikin halin tafiya (balaguro) yana da damar ajiye azumi bayan watan ramadana sai ya ranka wannan yinin idan kuwa tafiyarshi a kwana biyu ne kuma ya ajiye azumi na tsawon kwana biyu sai ya ranka wandannan kwanaki biyu; a takaice zai ranka iya kwanakin da ya sha.
Idan kuma matafiyi ya ga yana iya yin azumi to ba dole ba ne ba, sai ya sha ruwa domin shan ruwa sauki ne da Allah Ya bashi, yana da damar yin azumi: ya dubi abin da ya fi sauki gare shi sai ya aikata.
Kuma dukkan abin da ya yi kama da rashin lafiya ana bashi hukuncin rashin lafiya misali; mutum ya yi kaho ya fitar da bataccen jini, ko kuma ya bada jini lafiyayye sai ya samu raunin jiki kamar mara lafiya.
Haka ma mace idan taga jinin al’ada wajibi ne akanta ta bar azumi sai ta ranka kwanakin da ta sha bayan watan Ramadana.
Ita ma mai biki ya haramta a kanta ta yi azumi kuma bayan watan Ramadana ita ma za ta ranka ranakun da ta sha.
Amma mace mai ciki ko mai goyo idan azumin ya kasance zai cutar da ita ko zai cutar da dan ta sai ta ajiye azumin sa’annan bayan Ramadana sai ta ranka iya kwanakin da bata azumta ba, kuma yana da kyau ta ciyar da miskini guda dukkan wuni bayan ta ranka azumin.
Mutunen da kuma ba shi da karfin yin azumi kuma likitoci suka tabbatar mishi cewa ba zai iya yin azumi ba, to wajibi ne akan shi ya yi sadaka; wannan sadakar ita ce: ciyarda miskini guda ko wace rana da bai azumta ba; kenan zai ciyar da kwatankwacin abincin da zai ishi miskini talatin ya ciyar da miskini talatin abincin da zai ishe su.
RANAR IDI
Idan musulmi suka gama azumtar watan Ramadana gaba daya, ranar farko ta watan Shauwal Idi ne na musulmi; shi ne kuma ake kira idin samun baki ko buda baki bayan watan azumi. A cikin wannan rana musulmi suna nuna farin cikinsu saboda Allah Ya basu damar cika ibadar azumtar watan Ramadana.
Kuma suna nuna farin cikinsu ne ta fuskoki masu awa daga cikinsu akwai:
·       Nuna farin ciki ta fuskar yawan godiya ga Allah madaukaki.
·       Yawaita kabarbari da girmama Allah; don haka tun daga daren Idin har zuwa safiya suna yawaita cewa (Allahu Akbar, Walillahil Hamd)
·       Suna yin sadaka ko wane magidanci zai fitar da kwatankwacin kilo uku na alkama ko shinkafa ko abincin mutanen wannan garin ga duk wanda ciyar dashi ya rataya a wuyanshi.
·       Suna nuna farin cikinsu ta hanyar halartar sallar Idi bayan bullowar rana da dan lokaci kadan; inda suke sallar raka’a biyu a cikin jama’a, suna masu sanya tufafi masu kyau mafifita. Wannan duka yana nuna mana cewa idin musulmi babu nuna jiji da kai ko shan giya ko abin da yayi kama da haka a cikin shi, sabanin yanda yake wajen wadanda ba musulmi ba. Idi ne na biyayya ga Allah da yin sadaka da sadar da zumunta da rahama da gafartawa juna tare da yin sulhu… Suna masu jiran babban Idi yayin da za su kasance a cikin al’janna suna matasa, kuma babu mutuwa ko tsufa ko ciwo ko tabewa. Wannan kuma shine babban rabo.
Wannan kuma shi yasa musulmi ya ke rayuwa a nan duniya cikin kwancin hankali da yarda da halin da yake ciki duk yanda ya kasance a cikin musiba domin ya san abin da ke wajen Allah gobe kiyama. Allah Yana cewa “Kuma abin da aka basu daga kome, to, jin dadin rayuwar duniya ne da kawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shi ne mafi alkahiri kuma mafi wanzuwa. Shin ba ku hankalta?”. (Suratul Al-Qasas).
Daga karshe ina rokon Allah daya datar damu alkhairinSa tun a nan duniya Ya kuma taimake mu Ya sanya mu a cikin RahamarSa a Lahira Ya sanya mu aljannarSa madaukakiya amin.
Daga mai kaunar Rahamar UbangijinSa mai yawan kyauta.
Sharahbil Muhammad Sani

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment