HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 7



HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 7

 


*** *** ***
Inna ke faman yima Dad fada Cewarta “ai laifin shi ne ace,   kamar Mukhtar ya zuba mishi ido, tun da yace, baya auren shikenan ta zaunu. To yanzun kuma da ake kokarin hada zumunci ya tubure ba zai yi ba to da kai har shi ba ku isa ku bata mana zumunci ba.yanzu gashi kace, kun bashi wata daya ya fidda mata, me ya rage tunda har gashi anyi sati biyu, saura sati biyu kenan, amma hankalin shi kwance, ba inda ya sa kai. Maganar gaskiya Ibrahim da sati biyun nan sun cika bai fitar da matar da zai aura din ba, ba wani lokaci da za’a kara masa, ya zama tilas a hada wannan auren ko baya so. Koda yake goyon bayan ka yake samu shi yasa.” Haka Inna taci gaba da fadan gaskiya ranta yabaci sosai, dole Alhaji ya shiga bata hakuri. Ya rasa yadda zaiyi da kansa gaskiya baya son takurama yaron yafison a bishi a sannu, sai dai kuma ba yadda zaiyi dole ne shima ya matsa ma Mukhtar.
Ya samu ya ba innar hakuri ta sasauto da fadan da take yi “shikenan Ibrahim na hakura, amma nasan yaron nan so yake ya rika yawo da hankalin jama’a, amma Allah ya kaimu cikar sati biyun nan lafiya zaiyi mamaki.”
Alh da shigar sa gida ya yi sa’a Mukhtar yana nan ya kira shi ya kara jaddada mishi hukuncin da za su zartar idan cikar sati biyun nan ya yi bai fitar da mata ba. Abin mamaki kuma yanzu ba inda hankalinlin shi ya tashi balle ya damu kamar kwanaki, a zaton Dad din kila zai yadda da zabin su ne.mukhtar ya fito ya nufi falo, mom ta dubi Alh, “haba! Alh yanzu haka za’a kyale yaronnan?  ka dubeshi don Allah yanzu ba inda ya damu da maganar da muka yi, hankalin shi kwance,”. Alh ya yi murmushi, “to Amina so kike mu rika tada masa hankali koda yaushe, ki bari kigani  idan lokacin da muka diba masa ya cika, kuma bai bi umurnin na mu ba, sannan asan matakin dauka.
Yauma kamar kullum farida kwance, take cikin kujerar falon, ta na kallon cartoon din Tom & Jerry. Yaya Mukhtar ne ya shigo ya sami tana kallon cartoon din, ya dan yi murmushi mai kama da dariya ya zauna hadi da Cewa, “kai Farida yau kuma cartoon ake kallo?” cikin dan murmushi ta ke maganar “yaya ai ko cartoon dinnan yana da kyau” “eh to tun da kin maida kan ki karamar yarinya,” “Allah yaya ina sha’awar kallon shi”.
“Tunda kin ce haka nima bari in kalla”. Kallon yake yaga ba wani abin da ya fahimta , shi cartoon din ma dariya yake ba shi, ya san ita ma ta na kallon ne don nishadantarwa, har ya fara gajiya farida ko kallon ta take cikin nishadi. Mujallar da ke saman kujerar ya dauka ya ci gaba da karanta wa.

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment