3.0.2 Na’urorin fitarwa
(Output Device): Su ne duk
wani abin da za a iya amfani da shi wanda zai bada damar fitarda bayanai a
cikin kwamfuta. Kuma akwai sanannu guda uku, gasu kamar haka:-
Jerin gwanon
na’urorin da ake iya gani masu fitar da bayanai kuma a taɓasu kai tsaye
LAMBA
|
SUNA
|
HOTO
|
1.
|
Abin Kallo ko Allon Majigi(Monitor):Wannan shine allo mai fitar da saƙo lokacin da ake gudanar da wani abu ko ake
danna wasu madannai ga Allon Rubutu (keyboard).
|
|
2.
|
Injin ɗab’i (Printer): Wannan ita ce firinta dake fitar da bayanai ta
hanyar fitarda su bisa takarda.Su kuma waɗannan takardu da ta fitar, su ake kira had kwafi (hard
copy).
|
|
3.
|
Abin Magana (Speaker):
Murya tana ɗaya daga cikin saƙo ko kuma a ce
bayanan da za a iya karɓa
daga abin magana.
|
|
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment