HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 13
Ganin tadan lallabeta mom din ke shaida ma ta Dad din ta na kira, mikewa tayi tare da Mom din suka nufi sashen dad din. Ta sami wuri ta zauna, dad din ya shiga bata Magana tare da bata hakuri da lallami, ran dad din har yanzu a bace yake ya tsani abun da zai zo ya tada ma ‘yar sa hankali, duk da haka, ya nuna mata shima ba zai taba yadda ta auri Usman ba. Ta dan cije lebe Allah sarki, bata so dad din ta ya dauki zafi da yawa ba , hawaye suka tararo mata, cikin tausasa murya take Magana Cewa tabi umurnin sa ta hakura da auren Usman, sam bata son saba ma iyayen ta, tana iya gwargwado don ganin ta faran ta rayukan su. Har yanzu tana son Usman sai dai ta riga tayi alkawali ta hakura da shi don ganin ta yi biyayya ga mahaifin ta tun da hakan shine farin cikin sa. Sai dai taci gaba da du’a’in Allah ya hada ta da miji na gari
Inna ce ta shigo ta same su “au ‘yar ce aka saka gaba ana lallashi ce kake karamar yarin ya? Koda yake ba wannan ya kawoni ba.” Ta dan gyara zama “Ibrahim dama Cewa nayi gara inzo da kai na idan ba haka ba, ko yanzu ba tada masa zancen nan na auren sa za kuyi ba, alhali yau ne cikar wa’adin da aka diba masa. Na ga alamar kunfi son ku biye wa yaron nan saboda haka ni yanzu ku kira shi gamu zaune a ji tabakin shi, idan har yanzu Allah bai hore ya hana shi ganin wadda zai aura, mu Allah yahore mana muna da wadda zamu hada.” Tun lokacin da inna ta fara magana ko tari ba wanda ya yi shi dai Dad hakuri ya shiga bata, yana fama da wannan matsalar ta farida ya ma manta ya tuntubi mukhtar ya ji tabakin sa, sai dai baisan ko mukhtar din yana gida ba hakan ya sa ya dauki waya domin ya kira shi. Mom kuwa indai maganar auren mukhtar ce, takan goyi bayan inna, ganin take yaron yana nema ya rena mutane, in dai Dad ne ba ruwan shi, ba inda zai sa kai balle ya damu har ya rika yi mishi fadan auren, saboda Cewar sa ba zaiyi ma ya’yan sa auren dole ba, kan haka baya son takura mishi. Wan da ga sa’annin sa nan sun yi uren wasu har da ya’ya daga mai biyu sai mai uku.
Bangaren mukhtar kuwa tunda safe da yaje office, kasa zama yayi, saboda rashin jin dadin jikin sa da bayayi.
Gida ya dawo idon sa rufe saboda ciwon da zuciyar shi ke yi, yana shiga dakin shi kwanci yayi saman gado bayan ya rufe dakin. A hankali ya rufe idanun shi, nan da nan ya kara shiga wani sabon tunani, ya tuna yaune cikar wa’adin da aka diba masa, ya gama yanke ma kan shi hukun ci a zuciyar sa, lokaci guda tsananin ciwon kai ya taso masa lamarin yabi ya rikece masa, nan kuma ya shiga ganin jiri Allah ya taimakeshi kwance, yake da ba a bin da zai hana shi faduwa.
Bai san irin hukuncin da za suyi ma maganar sa ba, zuciyar shi kamar zata buga yake ji, numfashi yake fitarwa a hankali, duk rigimar da ake ta farida baisan ana yi ba, saboda tsananin ciwo, ya dauko magunguna ya sha, Allah ya taimake shi ya shiga furta addu’o’i, da taimakon Allah kuma ya fara samun saukin ciwon, bacci kuma ya dauke shi.
Bai jima sosai da yin baccin ba kuma ya falka, cikin ikon Allah jikin shi yayi sauki, wanka ya shiga, ya fito, ya shirya tsaf dashi shigar kananin kaya ya yi, kwarjinin na shi ya kara fita. Yana cikin shirin ne wayar shi ta shiga nuna mishi alamar kira, ya sa hannu ya dauki wayar domin ya duba mai kiran na shi bayason a takura mishi, ganin number din Dad yasa ya yi saurin karawa ga kunne. Dad din bai tsaya wata doguwar Magana ba ya shaida masa yana neman shi duk inda yake, bai jira amsar da zai bashi ba ya tsinke layin.
Fitowa ya yi ya nufi kiran da ake masa, ya riga yasan ma’anar kiran nashi, ya same su zaune ya zube kasa hadi da bada gaisuwa , sannan ya gyara zaman shi, lokacin farida ta gaida shi ya amsa gaisuwar cikin fara’a hadi da dan murmushin da ya bayyana gareshi. Inna kam ta katse masa hanzari da cewa, “kai mukhtar ka dube mu nan, kada ka rika yawo da hankalin mu ka maida mu kamar sa’an nin ka, shin ina ka tsaida zancen ka?” Dad din ya kasa cewa koma, yana shirin jin yadda zata kaya saboda yana kyautata zaton ko yanzu mukhtar bai zo da wata kwakkwarar maganaba don ya san kwanan zancen, ya san ko yan zu cewa zai yi bai tashi ba.
Mom kuwa daka masa tsawa tayi “ya ana maka Magana zaka wani sadda kai ka kyale mutane, ka tashi kaba mutane wuri idan har baka da abin cewa, tunda dama munsan kwanan zancen naka har yanzu maganar ka day ace, baka tashi ba, amma kasan cewa daga yau ka yadda da auren Sadiyar.” Cikin razana ya dago fuskarshi wadda take sharkaf da hawaye, al’amarin nashi mamaki yake ba su.
Ya dan tausasa murya “don Allah mom ku gafarceni, ku tausaya min wallahi ina da wacce nake son aure, Dad ku tausaya kada kuyi fushi da ni, nima kaina bansan yadda a kayi hakan ya faru ba. Nayi iyakar kokari na don ganin na kawadda wannan a zuciya ta, amma al’amarin dada karuwa yake, hakan yasa na yadda da cewa yin Allah ne ba yina bane. Dad ku iyaye na ne da banda tamkar ku, a duniya, nasan zaku so farin ciki na, kamar yadda zaku ki abinda zai zamo sanadiyyar salwantar rayuta, me yiyuwa idan na rasa farin cikin.” Hawaye keci gaba da tararo mishi yaci gaba da maganar da yake hadi da kara marairai cewa.
Farida kam tausayin shi ya kamata dama ta raya a ranta cewa duk wannan abun na yayan ta akwai wacce yake hange, sai dai batasan dalilin da ya hanashi bayyana hakan ba, wata kila yana shakkar iyayen na su ko baza su amince da zabin sa bane.itakam bata taba ganin soyayya irin haka ba, kai amma ko wace ceta cira tuta, yayan yana matukar kaunar ta da yawa cikin zuciyar ta take masa fatan alheri duk da batasan ko wace ce ba amma tasan yayan ta ba zaiyi zaben tumun dare ba, tayi matukar farin ciki. Yadda yake maganar hawaye na zubo mishi ya kara bata tausayi itama bata san lokacin da hawayen suka shiga zubo mata ba, sam ta manta da duk wani bacin rai dake zuciyar ta, ganin yayan ta ya shiga wani hali, kai yaya da daukar lamari da tsawo uhm ...“ tunanin ta ya katse lokacinda Dad ke cewa, “ya isa haka mukhtar ka gaya mana wace yarinya ce zaka aura? shi kenan mun huta, idan ma duk wannan magiya da kake ka na ganin kamar ba zamu goyi bayan ka ba, ka daina tunanin haka duk wacce kake so za muyi kokari don ganin ka cimma burin ka kaji ko?” zuciyar shi na tattare da fargaba yak e cewa, “don Allah dad ku yafemin, ku barni in.. in.. auri…. sai kuma ya yi shiru, kayi Magana mana kayi shiru, muna saurarenka, ya danyi jim sannan yaci gaba da maganar tattare da fargaba, don Allah dad ku aura min FARIDA.
Dad din bai fafimci maganar tashi ba “wace farida kake nufi?” a hankali ya nuna farida dake zaune kusa dashi. Zumbur Mom din ta mike hadi da bashi wani wawan mari a kunci, Sai kuma ta shiga zubda hawaye ta na cewa, “Mukhtar yanzu abin da zaka saka min kenan? To wallahi baka isa ba bazaka tona mana asiri ba dama abin da kayi nufi kenan tun da wuri kayi saurin canza raayi.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment