HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 5



HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 5




*** *** ***
Lokacin auren na kara gaba towa, dayan bangaren kuma sai kara samun texts ga wayar ta, al’amarin sai dada karuwa yake. Hakan yasa ta yanke hukuncin canza layi, ta sanya sabon layin ga wayar ta ba wanda yasan ta canza layin.
Cikin falo take zaune ta na kallon wani comedy daya da rabi na rana text ya shigo wayar ta, layin da ko sau daya bata kira kowa ba saboda haka bata yi far gaba ba, sai lokacin da ta fara karanta text din kamar haka:
Farida me yasa kike kokarin guje mini alhali ni da ke mutu ka raba?.
Ta kara dubawa ba number sam yanzu bata yadda da wannan text din ba. Ya za’ayi daga canja layi har a samu lambar ta wannan lamari da sa ke. A hankali ta rufe idanun ta, ta kwanta ko zuciyar ta zata dan fahimtar da ita wani abu, amma sam ta kasa fahimtar da ita komai saboda ta na tattare da RASHIN SANI!... wanda hausawa ke cewa yafi dare duhu. Fitowa ta yi ko zuciyar ta zata samu sauki, ta nufi lambun gidan zaune ta ke daya daga cikin kujerun biyu da suka zagaye table din, ta na tattare da damuwa, sai dai kuma tana jin dadin kamshin fulawowin.
Ba zato taji muryar Yayan na ta wurin, ta daga kai ta dube shi hadi da dan gajeren murmushi. Tsaye ya ke ya dan harde hannayen sa a kirjinsa ya na kallon ta, ya dan saukar da ajiyar zuciya sannan ya ja kujera ya zauna, suna fuskantar juna. “lafiya na ganki  haka”? ta danyi jim sannan ta kalli Yayan ta ce, “Yaya al’amarin na neman yima zuciya ta yawa,  ta dan yi shiru ba tare da ta ce   komai ba ta mika masa wayar ta ta. Ya karbi wayar hadi da cewa, “matsala wayar ta samu?” girgiza kai ta yi alamar a’a ta dan numfasa duba text message din da ke ciki, har yanzu da sauran murmushi tattare a fuskar sa ya karanta text din, ya dan dubeta to menene? Tasan Yayan na ta bai fahimci inda ta dosa ba, hakan ya sa ta yi masa bayani bata boye masaba. Ya danyi shiru kamar me tunani can kuma ya ce, “to Farida ina laifin wanda ya kamu da son ki”? Ta dan dube shi “to Yaya ni ba wannan ba ko ya yi shekarun maiki ya na turo message din shi ba wani tasiri kalaman shi za su yi ba. Ni yanzu abin da ya shige min duhu yau na canza layi, layin da ba wanda ya sani, na yi hakan domin guje ma text din amma hakan bai yi tasiri ba. Na damu matuka ina son sanin ainihin mutumin.
Saukar da ajiyar zuciya yayan ya yi, “gaskiya farida ba bin da za ki yi face du’a’i wannan ita ce, mafita. Ya ciro wayar shi nidai ga waya ta ki samin lambar, tun da rowar lamba ki ka so yi. Ta karbi wayar dubawan farko hoton ta ne ta na dan murmushi a matsayin screen saver din wayar, hoton ya yi kyau, ta ci gaba da sa lambar ta gama ta mika mishi wayar, ya karba hadi da Cewa,”na gode koda yake sai da na roka. To amma yanzu ai sai ki daina boye lambar ki sanar da mutane tunda canjin layin baiyi amfani ba, ko ki koma ga tsohon layin.” Ya karasa maganar cikin dariya, ita ma sai yanzu lamarin ya bata dariya ta riga ta saba da dabi’un sa.
Da hakan kuma suka koma cikin gida. Da shigar su gidan Dad ya kira su, tare su ka nufi kiran Dad din na su, sun sami Mom din su a ciki. A kasan carpet din wurin su ka zube hadi da bada gaisuwa, sannan su ka gyara zaman su, shi dai mukhtar ba zai raba dayan biyu ba,ya san magar auren shi za’a yi, kamar kuwa ya sani Dad din ya yi gyaran murya, “dama ba komai ya sa na kira ku ba sai don batun auren ku. Mukhtar gaban shi ya shiga faduwa sam ya tsani a tada mishi zancen aure ya san yanzu ba maganar da za’a yi bayan ta shi. Dad din ya ci gaba “mukhtar saboda kai muka hadu a nan, yanzu don Allah kafi son kayi ta zama haka ba auren? Shifa aure wani kariyar mutun ci ne na daban, wanda komai dukiyar ka, girman ka, da kuma mukamin minka idan ba aure tare da kai mutuncin ka ragagge ne.ka na zaton haka yafi maka?. Mukhtar na sanya maka ido domin inga iya gudun ruwan ka, to amma sai naga abin naka sai gaba- gaba yake yi ka na neman wuce gona da iri. Kaga tun yanzu idan kasan da wacce ka ke so ka fito fili ka gaya mana, idan ba haka ba zan hada ka da sadiya kanwar ka kodan mukara dankon zumunci”. Dad din ya yi shiru ko akwai abin da Mukhtar zai ce.
Mukhtar ya kara takushewa wuri daya, cikin nuna alamar girmamawa yake Magana, hadi da tausasa murya ya ke cewa, “Dad don Allah ku gafarceni, kada ku rike ni da wannan a zuciya har ya sanya ku yi fushi da ni”. Ya dan kara kaskantar da murya “Dad shi aure nufi ne na Ubangiji, kuma ya na da loka ci gaskiya a yanzu zuciya ta tattara zancen aure ta aje, Dad bazan boye muku ba.
Sai dai na san idan lokaci na ya yi ko ina so ko ba na so zan yi, wannan hukunci ne na Allah.”
Ya na ida maganar hawaye suka tararo mishi, al’amarin da ya basu mamaki kenan.farida tadan gyara zama cikin nuna alamar biyyayya ta ce,, “Dad don Allah ku yi hakuri kada ku dauki wannan doguwar  matsala, idan aka yawaita du’a’I  za’a shawo kan lamarin da sannu lokaci ke zuwa ya yi aure.” Mom din tace,, “tun yau she ake bin sa da lalama? Amma ya rika yawo da hankalin mutane, yanzu kam ba zai bata mana tsari ba. Rana daya mu ke son hada bikin auren ku.
Bai iya cewa komai ba, shi kadai yasan yadda yake jin zuciyar sa, ya kasa Magana, kirjin sa ke neman yi mishi ciwo, kan shi wani tsananin ciwo yake mishi. Farida kam tausayin shi ya kamata, ta tsani takurawa da ake son yima yayan ta, ganin laifi ta ke wai meyasa ba za’a kyale shi ba har ranar da ya yi niyya don kan shi? Sai dai tasan duk wannan yawan fada da ake masa laifin Inna ne, ita ke yawan yima Dad Magana. zuciyar ta na da tabbaci ko wannan hadin auren da ake son yi mishi da Sadiya hadin inna ne. kai gaskiya inna nason takura rayuwar dan adam, ta rasa dalilin da yasa take ire-ire wannan lamarin. Hakuri ta shiga ba dad din ita dai bata son a tilasta masa wannan auren.
Cikin tausasa harshe ya shiga ba iyayen hakuri, da kyar su ka hakura da hadin auren da za su yi mishi, sai dai da sharadin ya tabbatar da nan da wata daya ya fitar mu su da yarinyar da zai aura.
Bayan sun fito da sashen Dad din, zaune su ke cikin falo Farida ke yi mishi nasiha da ya yi kokari ya faranta ma iyayen su rai, kada ya yi abin da yasan zai taba zuciyar su. Allah sarki yana jin dadin yadda kanwar ta shi take godiya yake ga Allah. Bai ki maganar ta ba zaiyi iya kokari don ganin ya fitar da yayinyar da yake son ya aura kamin cikar wa’adin da aka diba mishi. A hankabi ya shiga tunani, amma sam kwakwalwar sa ta ki aminCewa ta nuna ma zuciyar shi yarinya daya da zai aura, shima da kanshi ya san zuciyar shi ba zata aminceba. Ya shiga damuwa baya son ana tada mishi magar auren nan, yakan shiga wani yanayi na daban ba a bin da zai yi yanzu face neman zabi a wurin Ubangiji. To ko meye dalili?.
Da wannan tunanin abokin shi Bashir ya same shi bashir din ya yi sallama amma sam hankalin shi bai kawo ba balle ya ji sallamar. Ya isa kusa da shi ya dafa kafadar shi, Mukhtar ya yi firgigi sai dai ya dan yi murmushi ganin abokin na shi. Farida ce ta kawo mishi lemu da ruwa masu dan sanyi ta fita.
Bashir ya kurba lemun ya aje cup, sannan ya dubi abokin shi hadi da cewa, “wai kai me ke damun ka ne? kai kenan koda yaushe cikin tunani”. Mukhtar ya saukar da ajiyar zuciya hadi da cewa, “Bashir ka bar ni kawai al’amarin ya yi min  yawa, ka riga ka yi auren ka ka huta, ni gani koda yaushe cikin tunani da neman mafita. Basher ka na sane da irin yawan fadan da su Dad ke yimin ba don komaiba sai saboda aure, har takai sun bani lokaci nan da wata daya suke son in fitar da mata. Bashir na yi iya kokari ko zuciya ta zata sassauta na kasa, sai dai ina sa rai me yiyuwa haka Allah ya riga ya tsara tawa rayuwa banida rabon aure a duniya.” Nasiha Bashir ya shiga yi mishi, tare da nuna mishi idan yasan da yarinyar da yake so kada ya bar cuta a zuciyar shi, ya fito fili ya nuna ma yarinyar da kuma iyayen sa. Amma haka kawai zuciyar mutum baza ta ki amince mishi yin aure ba, sai idan zuciyar nada wacce, ta ke so ko kuma wani dalili. Idan ko ba haka ba baiga dalilin da zai hana shi yin aure ba. Murmushin karfin hali kawai mukhtar ya yi saboda ba a bin da zai cema Bashir, shidai a nasa bangare ya san zuciyar shi ta rasa mafita, sai dai neman taimakon Allah.

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment