BABI NA
BAKWAI
7.0 MA’ANAR KWAYAR CUTAR
KWAMFUTA

Kwayar cutar kwamfuta wani
shiri ne wanda aka kirkira don ya yi shirya kanshi kuma ya kutsa kanshi zuwa ga
wani shiri ya kuma hayayyafa ya yada kanshi ba tare da masaniyar mai amfani da
kwamfuta ba.
Wasu shirye shirye zasu
dinga aiki batare da sanin mai amfani da kwamfutar ba kuma su tilasta wasu
shirye shirye daga cikin kwamfutar yin abin da ba donshi aka yisu ba. Wannan kalar kwayar cutar ana kiranta Warms,
Trojan horses, da Droppers. Dukkan wadannan shirye shiryen wadanda suka kunshi
kwayar cututtuka suna daga cikin shirye shirye da muka sansu da sunan (malware
ko malicious-logic software). Idan ka sayi sabuwar kwamfuta, a wannan ranar
yana da kyau ta fito da kunshin maganin kwayar cuta da za a saka a cikinta. Wannan
bangaren yafi komai mahimmanci ga kwamfuta. Kada a dauki matsalar kwayar cutar
kwamfuta da sauki, kwayar cutar tana lalata rayuwar kwamfuta gaba daya.
Kwayar cutar
Kwamfuta wasu kwayoyin cuta ne da ake iya samunsu wajen sanyawa ko kwafi wanda
idan ya samu wata kafa kai tsaye sai ya shiga a cikin wasu shiryeshiryen
kwamfuta ko fayil ɗin da ke ƙunshe da bayanai ko ta kasance mai nauyi wajen
yin (boot)ko (booting) a (hard drive)
ɗin ta idan
har wannan ƙwayar cutar ta yi nasarar shiga ko kama kwamfutar wannan shi ne za a iya
cema (infected).
Ƙwayar cutar
ya kunshi wasu kashekashen (harmful activity) na (infected
hosts) kamar tauye filin (hard disk) ko lokaci a CPU, ko
ya rusa wasu boyayyayun bayanai, ya kan lalata bayanai. Haka kuma ba duk kanin ƙwayar cuta ke
ƙoƙarin ɓoye kansu ba.
Akwai wasu daga cikin kwayar cututtukan da ke ninninka kansu ga shirye-shiryen
kwamfuta kuma su sa ka kansu ba tare da sanin mai amfani da kwamfuta ba.
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment