BABI NA SHIDA
6.0
WANENE BABAN KWAMFUTA
Muna
da ɗaruruwan
mutane waɗanda
suka bayarda kaso mai yawa na gudummawarsu don a cimma nasara ga kimiyyar
kwamfuta. Amma duk da wannan bayanin nawa baza a rasa wanda shi ne tushe da ga
cikin waɗan nan mutane ba, haka kuma a kwai wanda shi ne uba ga ita kanta
kwamfutar tafi-da-gidanka wadda dukkaninmu ita muka fi sani a yau.
Kamar
yadda aka sani cewa Carles Babbage shi ne wanda aka yi yakini da cewa
shi neuban kwamfuta, bayan ƙirƙiro (analytical engine) da ya yi a
shekarar 1837. Shi (analytical engine) ya ƙunshi wani abu da ake
cema (arithmetic logic unit) ALU, da sauƙaƙaƙƙen (flow
control) da kuma (integrated memory). Daga nan wannan
kwamfuta ba a sake ƙerata
ba lokacin da Charles Babbage yake a raye. Haka kuma a shekarar
1910. Henry Babbage, ƙaramin ɗan Charles Babbage ya cigaba don ya
kammala aikin wannan inji wanda ke aiki don sauƙaƙa lissafi.
Shi ma Babbage
bai kammala wannan aikin ba a cikin rayuwarshi, hikimominshi da gudummuwar shi
da ya bayar su ne sukasa shima ya zama baban kwamfuta
Kamar
yadda na faɗa
a baya, akwai mutane da yawa da za a iya dubawa kuma su cancanci zama ubannan
kwamfuta, waɗanda
suka haɗa
da Alan Turing, John Atanasoff da kuma John
von Neumann. Haka kuma a sanadiyar wannan kundi za muje mu binciko Konrad
Zuse a matsayin baban kwamfuta da kuma ire-iren cigaban da ya kawo na
Z1, Z2, Z3 da kuma Z4.
A
shekarar 1936 zuwa 1938 Konrad Zuse ya ƙirƙiro Z1 a cikin ɗakin da mahaifansa ke
zama. Shi Z1 ya ƙunshi
sassan karafa sama da 30,000 kuma wannan shi ne abu na farko da aka fara na (electro-mechanical
binary programmable computer) a shekarar 1939, (German Military
Commissioned) suka nemi Zuse da ya fito da Z2, wanda yake
shine yafi girma akan Z1. Bayan wannan, ya kuma kammala Z3 a watan Mayu a
shekarar 1941, shi dai Z3 an (revolutionary computer) a lokacin
shi, sannan kuma an dubeshi a matsayin (electromechanical) da (program–controlled
computer). A ƙarshe,
cikin watan Juli, sha biyu a shekarar 1950 (12/07/1950), Zuse ya kammala kuma ya cigaba da
aikin san a kwamfutar Z4, wanda wannan aikin na Z4 ne aka fara duba a matsayin
kwamfutar kasuwanci (commercial computer).
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment