BABI NA TAKWAS: SHAWARWARI MASU AMFANI - KIMIYYAR NAURA MAI KWAKWALWA 44



BABI NA TAKWAS
8.0 SHAWARWARI MASU AMFANI
Kula da kwamfuta haka yake tamkar kula da littafi. Kuma kula da ita zai kasance tun daga cikin ta har zuwa sassan jikinta dake waje, dole ne a kula dasu sosai. Yawan binciken lafiyar kwamfuta kan taimaka sosai ga sanin halin da take ciki. Kan-kantawa da kuma sa ke tsare-tsaren kwamfuta suna daga cikin ayyukan da ke taimakawa (hard disk drive).
Haka kuma akwai takamaiman ayyuka da za a gudanar don ganin samun tabbacin kwamfuta ta zauna lafiya batare da wani fargabar samun matsalaba idan har an kiyayesu. Gasu kamar haka: -
v Sanyawa kwamfuta rikakafin kamuwa daga cututtuka: - (Antivirus) kan taimaka; maiyuwa kasan mekake sauke mata (download) duk da haka yana iya zo wa da cuta a cikinsa wadda za ta iya janyo kuskurewar (circuit) ko janyo matsala a softuwaya a cikin (system hardware ko software). Yana kuma iya sanya jinkirin aikin da operating system (OS) ke yi.
v Kawar da Kura:Dole ne ga mai amfani da kwamfuta yazama mai tsaftace kwamfutarshi daga ƙura da dauɗa.
v Ba’acin abinci kusa da ita: - ka da a ci ko a sha duk lokacin da ake amfani da kwamfuta, saboda abincin zai iya shiga a cikin madannin Allon Rubutu (Keyboard) ruwa kuma zai iya zubewa kanta kuma hakan na iya zama sanadiyar lalacewarta.
v Yi amfani da hannu mai tsafta: -A tabbatar an tsaftace hannaye kamin a fara aiki da kwamfuta gudun samun cikas ga allun rubutu (keyboard) ko linzamin kwamfuta watau (mouse ko kusu).
v Ayi amfani da kwamfuta cikin girmamawa: -a duk lokacin da za ayi amfani da kwamfuta, to, a kyautata mata wajen yin amfani da ita cikin karamci da girmamawa. Duk lokacin da ake da wata matsala ka da a fada mata har sai an nemi taimako, kuma ka da a bugeta lokacin da ake cikin fushi.
v Adana kwamfuta idan ankammala aiki da ita: ganin yadda kwamfuta ke mu’amalantar wutar lantarki walƙiya na iya zama mahaɗar wutar lantarkisaboda haka abin da yafi ka da ayi amfani da kwamfuta lokacin hadari.
v A riƙa Fai-fain CD da Muhimmanci: - Duk yaddaaka rika CD shi zai nuna irin tsawon lokacin da zai yi ana amfani da shi. A ko da yaushe ariƙa faifan CD da kyau (daidai).
v Aguji ajiye ruwa a kusa ga Kwamfuta: - idan har za a sha ruwa ko shayi lokacin da a ke amfani da kwamfuta, to, a tabbatar kofin yana da murfi mai kyau wanda ke kamewa a bakin kofin, kaga ko da ƙaddarar faɗuwa ta zo ruwan bazai zube ba. A sani cewa ruwa zai iya lalata ƙananan kayan wuta dake cikinta ko matsalar bugawar kwamfuta, kokasawar (circuits) kuma rowan zasu iya zama sanadiyar lalacewar bayanan da ke cikinta ko wani sashe daga cikinta. Don haka mafita ga shiga irin waɗannan matsalolin mai sai ce. Kawai a nisantar da duk wani abu mai kamada ruwa a kusa ga kwamfuta, ko da kuwa ana kula, wani zai iya faɗawa mazauninka. Ko kuma kai da kanka a halin mantuwa.
v Kada acibisa ga kwamfuta: - Shawarata a nan ita ce ayi nesa ga kwamfuta lokacin cin abinci, kada aci akanta, burbushin abin da ake ci zai iya faɗawa tsakanin maballin allon rubutu (keyboard). Burbushin abinci zai iya lalata (cuircutry) mafi munishi ne kwamfutar zata lalace da dauɗa idan har zata iya ƙasancewa da burbushin ragowar abincin da ake ci kanta, sannan kuma zata ƙeƙe. Bugu da ƙarikuma a nema mata wata ƙaramar jakar ratayawa.
v Ka zama mai tsaftace hannayenka: - Aduk lokacin da zaka yi amfani da kwamfuta, to, a tabbatar hannaye  nada kyau ta hanyar gogesu da wani kyalle tsaftatacce ko wankesu, amma idan wankewa akayi agoge da kyau gudun ka da ruwa su shiga. Bugu da ƙari, idan an tsaftace hannayen kamin ayi amfani da kwamfuta, yin haka zai taimaka mata wajen saurin kekewar ta, wanda ke faruwa sanadiyyar dauɗar zufa da hannaye keyi wanda zufar ke dauƙar matakin kai tsaye ga kwamfutaidan aka duba inda yatsa ke yawan taɓawa.
v Kare (LCD Display Monitor): - A duk lokacin da a ka kashe kwamfuta, to, a tabbatar babu wasu ƙananan abubuwa a samanta. Misali;alkalami ko abinsakawa ga kunne (ear-phone) ko kuma ƙutsar danne littafi da makamantansu, saboda sukan janyo lalacewar madannin kwamfuta ko a ce allun rubutu (keyboard) kuma zasu iya fasa abin nuna hoto/majigi (display monitor) ko su karjaye shi ma’ana abin nuna hoton ya goge.
A rufe ta (kwamfutar tafi-da-gidanka) tana kan cinyoyi tare da rike ta cikin kwanciyar hankali da lumana. Idan za a rufe sai a rika murfin ta gefe ɗaya saboda ba a son a tsananta ko a matsa mata da ƙarfi don kada maratayar (Display Monitor) ya goce a mazauninsa ko ya naɗe ko kuma ayi marus faduwar guzuma ƴa kwance, uwa kwance ma’ana ya karye.
v A tabbatar da ita abisa mazauninta: -Idan an ajiye kwamfuta ajirkice ko gilme ko kuma a wani sashe da bai dace ba ko wani mazaunin da baida dai-daito, zaa iya lalata majigi ko abin nuna hoto, wata ƙila wani zai iya faɗa mata ko ta faɗi idan tana kan teburi kuma bata zaunu a mazaunin ba. Kai tsaye maratayin da ke rike abin kallo ko kuma ita kanta zata iya goggogewa ko ta lalace kai tsaye don hawarshi da akayi ko tausarshi da karfi.
v Ka da a ja igiyar wuta: - Tuge igiyar wuta ko caja lokacin da take maƙale ga tushen wuta na soket maimakon a sanya hannu a cire kai tsaye ga inda tushen wutar yake, yin haka yakansa cajar ta lalace ko kuma shi suket din wutar ya lalalce, zata iya ƙunewa. Abu mafi sauki a nan shi ne idan akwai maɓallin kashewa a gefe sai a kashe gudun yi karo da ƙaddarar da zai sa ayi hasarar caja ko ita kwamfutar kai tsaye.
v Kada a saka Kujerar zama a cikin wayoyi:- a ɗauke wayar caja0 ta yi nesa da abin zama, wanda ya ke za a iya kuskurewa hawan wayar cajar, kuma yin hakan zai iya zama sanadiyar ƙasawarta ma’ana lalacewar ta. Ko da yaushe ayi ƙoƙarin fitar da wayoyin a kusa da abin zama don wata rana a na iya mantawa a je wucewa a jefa kafafuwa cikin wayoyin wuta ko a ɓarar da kwamfutar kaga ko an yi ba ayi ba kenan.
v A sanya komai a inda ya dace: - A koda yaushe a lura da alama a jikin kwamfuta da kyau kamun a sanya duk wani abu a jikinta. Yana da muhimmanci a kula da wannan batu.
v A kula da duk wani abu da ake iya adana bayanai a cikinsa abashi kulawa mai kyau: Misalin (Floppy Drives) ko (CDs) waɗan da aka riga a ka cire bayan anyi amfani da su ko kamin ayi amfani da su ga kwamfuta. Kai tsaye zasu iya lalacewa idan aka jefar da su a ƙasa ko aka taɓasu cikin sakaci ma’ana aka taɓa inda bai dace a taɓa ba. A sanya su a cikin mazaunin su misali jaka ko akwatin adanawa don sama masu nagartattun mazauni da kuma kulawa idan ba bu buƙatar amfani da su a kwamfuta a wannan lokacin.
v A sanya komai inda ake sashi: - sanya wani abu a inda bai dace ba  yin haka zai iya sanya wannan abin ya lalace.
v A bincika idan komai ya samu daidaituwa kamin a sanya ma’adanin tattara bayanai a cikin kwamfuta: - Ma’adanin tattara bayanaikamar (CDs, DVD) ko (Floppy disks) za su iya samun matsala ko su saka wata matsala a cikin mashigar fai-fain kwamfuta. Ka da a taɓa saka (CDs), ba tare da an tabbatar da daidaituwarsa ba, yin haka zai lalata mashigar faifan ya lalace har abada.
v Kada a bar kwamfutarka a cikin mota:- Bawai kawai saboda canjin yanayi na tsananin zafi da za a iya samu a cikin mota da shima zai iya lalata kwamfutar ba, sai dai kuma ajiye jakar kwamfuta zai iya gayyatoɓarayi.
v Nemi abubuwan da ake iyahure/gusar da ƙurar da ke cikinta: - A bawa waɗanda suka ƙware a fannin gyaran kwamfuta su gudanar da wannan aikin na gusar da ƙurar da ke cikin kwamfuta. Ko kuma ayi da kai idan za a iya. Idan ƙurar ta yi yawa a cikinta, to, lallai kwamfutar ba zata iya sanyaya kantaba. Tsananin zafi kuma zai iya tarwatsa shimfidadden allon kwamfuta.
v Guji ɗora kayan nauyi, kamar littafai a kanta ko a allon rubutunta: - Wannan zai sanya (LCD screen)har zuwa ga(keyboard) su iya lalacewa sannan kuma idan ba a dai na ba sannu sannu nauyin zai lalata kwamfuta.
v A nemi jakar da za a saka kwamfuta a ciki: - Sau da yawa kwamfuta ke fashewa a sanadiyar faɗuwa. Sanya kwamfuta a cikin jaka kan rage irin wannan matsala.
ABIN KI YAYEWA
ü A danna maɓallan allun rubutu sannu-sannu me yuwa bazasu ɓalle ba.
ü A ɗauki bayanan kwamfuta kamar (serial number) da (model) mai yuwa za a iya bada rahoto idan ta ɓata ko ɓarayi sun ɗauke ta.
ü A ɗauke kwamfutakusa ga ƙaƙanan yara.
ü A kebance wasu lokuta da ake duba matsalolinta a gyarasu kamin su yi girma ya fi bayan sun auko a ce za a yi gyara.
ü Idan har ba amfani za a yi da kwamfuta ba nan da awanni biyu, to, a kashe ta, idan ba haka ba, za ta kasance tana jan wuta sosai idan zata tashi fiye da wutar da zata ja idan tana aiki.
ü Barin na’ura mai amfani da wutar taltarki (kwamfuta) mai makon kashe ta daga wuta zai iya zama sanadiyar yawaitar zafi ko karfin shi ya ragu ya zama rauni ga wannan kwamfuta.
ü A guji sanya kwamfuta a ƙarƙashin shimfiɗa, wannan zai iya zama danadiyyar a takata kai tsaye ba tare da masaniya ba, kuma yin haka zai iya jawo lalacewarta kai tsaye.

0 comments:

Post a Comment

Thank You for Your Comment