HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 6
*** *** ***
Text din da take samu koda
yaushe ya karu fiye da yadda ta saba samu. Shin wai shi me wannan text din bai
gadi gajiya bane? Abin da take tambayar kan
ta ken an. Bangaren Usman kuwa idan ya zo yana kara jaddada ma ta irin kaunar
da yake mata. Haka ma ta waya baya gajiya da kiran ta, tana jin dadin kalaman
sa, bata gajiya da sauraren shi mawuyacin abu ne zuciyar ta ta iya rabuwa da
shi.
Kamar kullum zaune take cikin
falo, tana sanye da riga da siket shigar kananin kaya, rigar mai dan karamin
hannu ce,, kanta ba dan kwali ta yi kyau matuka; koda yake abune mawuyaci duk
yadda ta yi shiri zakaga ta yi fes fes da ita gwanin sha’awa da shiga rai,
wannan baiwa ce,, da ga Allah.
Wani Indian film ta ke
kallo, bata san shigowar yayan na ta ba hankalin ta ya dauku ga film din da
take kallo. Ya tabbata batasan shigowar sa ba, a’a ya za’a yi kallon film ya
dauki hankalin mutum da yawa haka”? abin da yake tambayar kan shi kenan.
Ta bayan kujerar da take
zaune ya isa, a hankali ya sa hannayen shi ya rufe mata idanu. Ba zato taji an
rufe ma ta idanun, tana da tabbacin yayan ta ne, sai dai gaskiya taji tsoro har
da ‘yar kara ta saka, zuciyar ta ta shiga bugawa alamar tsoro. Dariya ta kama
shi ya yi mamakin ganin yadda ta tsorata da yawa haka, ya bude mata idanun, da
sauri ta waigo ta ganshi tsaye ya dan saki wani dan lallausan murmushi, itama kan
ta murmushin ya burgeta, tana son dabi’un yayan na ta sai dai kuma ta riga ta
san yayan na ta mutum ne na daban da Allah ya zuba mishi baiwar halitta ta
musamman, ba taga laifin ‘yan matan da ke kururuwa a kanshi ba ya na da saurin
shiga rai.
Zagayowa ya yi ya zauna ya
dan dubeta “ashe tsoro gare ki ban sani ba”? “ai kuwa ni bani da tsoro kawai
dai yanzu ka taki sa’a” ta ce, da shi.
Murmushi kawai ya yi shima ya ci gaba da kallon film din. Kamar kullum yanzu ma
text ne ya shigo wayar ta a jere har kusan biyar, ta dauki wayar dake kan
kujerar da take zaune ta shiga duba texts din. Yau kam zuciyar ta ta sha
ban-ban bisa ga kwanaki, ba inda ta damu, haka kawai yanzu take son ganin
wannan mutumin. Abin mamaki kuma kalaman da ke cikin messages din sun tsaya
mata a zuciya, jikin ta wani sanyi na musamman take ji yana ratsata, ta
lunsashe idanu yanzu ta daina kallon, zuciyarta ta shiga wani tunani na daban
wanda ita kan ta, ta rasa dalilin wannan sauyi da zuciyar ta ta samu a yau, ‘
kai wannan mutumin mayaudari ne, sai dai kuma bata san dalili ba du’a’i take
Allah ya bayya na mata wannan mutumin ko waye shi. Hmm!!! Ta yi saurin kawar da
tunanin gudun kada yayan ta da ke zaune wurin ya fahimci wani abu.
*** *** ***
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment