2.2 BAMBANCE-BAMBANCEN
KWAMFUTA TA GIRMA DA ƘARFI KO SAURIN AIWATAR DA
UMURNI
Akasarin kwamfutoci ana bambantasu
ne ta ɓangaren girmansu ko ƙarfi ko kuma saurin aiwatar da umarni.
LAMBA
|
KWAMFUTA
|
BAMBANCI
|
1.
|
Tafi-da-gidanka (Personal Computer)
|
Akasarin
irin waɗannan kwamfutocin ƙanana ne wadda mutum zai iya mallaka kuma
yayi amfani da ita a kowane wuri. Tanada ƙarfi daidai gwargwadon yin lissafelissafe da wasu ayyukan da za a bata
umurni dasu. Tana zuwane da allon rubutu (keyboard), majigi ko a ce abin
kallo wato (Monitor) ko (Display Unit) na nuna bayanai, da kuma
ƙwaƙwalwa wato (Memory) na tara
bayanai.
|
2.
|
Kwamfutar
Babban aiki (Workstation)
|
Itace
kwamfuta mafi ƙarfi ta aiwatar da ayyuka
wacce mutum ɗaya zai iya amfani da
ita. Tana yanayi ko kama da kwamfutar tafi-da-gidanka.Amma
abubuwan data ƙunsa kamar ƙwaƙwalwa sun bambanta. Tanada ƙarfin gaske da sauri wajen aiwatar da ayyuka.Kuma majiginta yafi na
kwamfutar tafi-da-gidankafitarda hotuna.
|
3.
|
Kwamfutar
Ayyuka (Minicomputer)
|
Kwamfuta
ce da mutane aƙalla goma (10) zuwa wasu ɗaruruwa zasu iya amfani da ita a lokaci
guda.
|
4.
|
Kwamfutar
(Mainframe)
|
Itace
kwamfuta mafi ƙarfi wadda mutane fiye da
dubbai zasu iya amfani da ita a lokaci guda.
|
5.
|
Kwamfutar
(Supercomputer)
|
Ita
wanna kwamfuta bayan fin kowacce kwamfuta ƙarfi, tana kuma iya sarrafa kanta.
|
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment