HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI…1 BY SARATU M. SANI SERIES 9
*** *** ***
Usman Umar, mahaifin shi Alh
Umar shahararren dan kasuwa wanda ya yi fice, a harkar kasuwancin sa kasashe da
dama. Dan asalin katsina ne, matar shi Haj. Saudatu ce, mace mai kirki da kuma
sanin yakamata, ya’yan su uku Nafisa, Mariya sai kuma Usman da ya kasan ce, auta.
Alh Umar mutum ne mai
tausayi, sanin ya kamata da kuma hangen nesa. Mutum ne da bai dauki duniya
bakin komai ba, yana da tarin dukiya amma dukiyar dai- dai gwargwado amma
dukiyar bai dauke ta komai ba. Shi dai komai yake yi yana sa tsoron Allah a
cikin lamarin sa. Ya yi sa’a da kuma Allah ya hada shi da mace ta gari, da har
suka hadu suka yima ya’yan su tubalin tarbiyya ta gari, wanda har suka girma.
zuwa yanzu. Hakan ya sa jama’a ke yaba masa, suna yaba halayyar sa.
*** *** ***
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment