5.2 AMFANIN YANAR GIZO/KAFAFEN SADARWA (INTERNET)
Bazan iya lissafo amfanin ta ba gaba ɗaya, saboda amfaninta
yana da matuƙar yawan da ba
za a iya lissafashi ba, amma ga kaɗan daga ciki:-
ü Fasahar Intanet wata duniya ce mai cin
gashin kanta, fasahar a yau ta zama gagarau, domin bayan hanyoyin sadarwa, duk
abin da kake da bukata a internet zaka samu ta hanyoyi daban-daban; ko dai ta
hanyar Injimin nema misalin manema ta google, ko Yahoo ko kuma AltaVista, zaka
iya samun bayanai ta tsararrun hanyoyin neman bayanai misali; (Directories).
Baya haka kuma, akwai wasu nau’ukan bayanai da suka shafi sauti ko na hoto mai
motsi (video) duk zaa iya samu a wannan hanyar ta yanar gizo.
ü
A ɓangaren ilimi kuwa; a yanar gizo za a iya karatu har a kai
ga matsayin digiri ko digirgir har a digirgire ma’anar wannan shi neza a iya
samun shedar takardar yin (degree), (Masters) da kuma (PhD). Zaka iya shiga
makaranta ka ɗauki darasi, ka nemi bayanai wurin
malaminka, kayi jarabawa har ka samu sakamakon jarabawar babbar jami’ar da ke
cin karenta babu babbaka a duniyar yanar gizo. Misalin waɗannanjami’o’in sun haɗa
da National Open University of Nigeria (NOUN), World Education University (WEU,
da kuma Online Islamic University (OIU) da sauransu.
ü
Idan kuma
muradinka haduwa da mutane, shima wannan abu ne mai sauƙin
gaske, tun daga wadanda ka sani da kuma wadanda baka sansu ba. Akwai hanyoyi da
yawa da zasu baka samu wannan damar, misali; Facebook, Twitter, MSN Messenger,
Yahoo Messenger, ICQ Chat Messenger, Sharhamak Forum da sauransu. Babu shakka
idan har wanda kake son hira dashi yana da irin waɗannan
hanyoyi kuma ya bude su, yanzu zaku yi rubutacciyar hira da nau’ukan hirarrakin
da zasu iya samuwa ta waɗannan
kafafe. Idan kuma hirar video kake so, ma’ana; kana ganin wanda kake hirar da
shi, shima yana ganin ka kai tsaye; wannan ma abu ne mai sauƙi domin akwai kafafen da wannan ne kawai amfaninsu a kafafen
yanar gizo. Misali; ooVoo da skype da sauransu.
ü Shafukan sada zumunta na yanar
gizo ba karamin taimakawa mutane ya yi ba, musamman idan kana neman wani
abokinka na shekara da shekaru ka ƙasa samun sa, to
idan ka laluba za ka same shi a daya daga cikin waɗannan shafuka wato facebook ko twitter ko instagram ko
WeChat, da sauransu. Haka kuma idan ma labari kake nema da dumi-duminsa to ka
leka daya daga cikin waɗannan
shafuka to tabbas zaka samu labarin da kake nema. Kai a takaice dai duk abinda
kake nema kama daga mutane, kayan sayarwa,
labarai da dumi-duminsa labarai na nishaɗantarwa dana ban al’ajabi da sauransu idan ka tambaya
to tabbas za ka sami mai baka ansa.
ü Intanet har wa yau wata duniya ce
ta ma’adanar bayanai. Mutum ya zauna da jahilcin wani abu, bayan ya iya
rubutu da karatu alhali ga (Intanet) – ina tunanin wannan shi ya
so ta ƙasance masa. Duk bayanin da kake bukata, zaka
sameshi (muddin wani yayi rubutu a kansa). Idan takamarka karatun jarida ne, an
gama! Dukkan wata jarida da ka san ta shahara a duniya zaka samesu a yanar
gizo (Intanet). Sai ka karanta su ma kafin a fara
sayar da su a biranen da ake bugawa ko yada su. Idan kana son karanta irin
binciken da wasu masana suka yikan wasu al’amura, duk zaka iya samu a
yanar gizo (Intanet). Dukkan wata ƙasa da ka sani zaka iya samun bayaninta a kafafen ko shafukan (Intanet),
ka karanta ko ka ma yi dukkan abinda ka ga damar yi dashi, ya rage naka.
ü
Dandalin sada zumunta a shafukan yanar gizo sun
taimakawa mata sosai, musamman matan da suke gida basa aiki ko zuwa makaranta,
sai dai zaman gida. Irin waɗannan matan da suke zaune a gida yawanci
idan sun gama aikace-aikacen gida su kan leka irin waɗannan zauren sada zumunta su zama membobi
na guruf-guruf din da ke ciki domin samun karuwa. Wasu daga cikin guruf din
facebook sun haɗa dana girke-girke, saye da sayarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa da dai
sauransu. Sau da dama za ka ga wasu matan auren sun shiga irin waɗannan guruf din
ne da zuciya daya, domin su samu su karu akan wani abu da ba su sani ba ko kuma
su yi tambaya idan wani abu ya shige musu duhu.
ü A ɓangaren
siyaya kuma, munga irin rawar da amfani da internet ya yi mana a wannan karon,
wajen yada manufufin mu na siyasa da tallata yan takararmu tundaga shugaban ƙasa, yan majalisa, sanatoci, gwamnoni
da sauransu. Don haka; internet abune mai matukar muhimmanci a wannan rayuwar
tamu ta yau da kullum, akan haka ne yasa idan za ace da mutum ya fadi amfanin
internet babu shakka sai dai kayi iya ƙoƙarinka
don kowa da irin amfanin da sai iya morema a yanar gizo.
Duk da hka kayi kokari matuka
ReplyDelete