BABI NA
HUƊU
4.0 MA’ADANIN
TATTARA BAYANAI
Ma’adanin
tattara bayanai da umurni wato (Storage Media) don
amfani da su zuwa gaba. Dukkanin kwamfutuci suna amfani da ma’adanin tattara
bayanai domin adana (software) wanda sai da shi ne sannan (hardware) ya yi
aiki. A matsayinka na mai amfani da kwamfuta, ka na
ajiye ko adana bayanai iri daban-daban a cikin kwamutarka ko kuma
a cikin ma’danin tattara bayanai.
Ma’adanin
tattara bayanai, wani abu ne da za mu iya ganin shi a zahirance, ba ɓoyayyen abu bane
da zaa ce baa iya ganinshi ko kuma a taɓashi ba, abu ne da ake iya adana ko
ajiye bayanai da kuma umurni. A duk lokacin da mai amfani da kwamfuta ya adana
bayanai a cikin ma’adanin bayanai, a taƙaice dai ya adana fayil kuma wannan matakin ana kiransa
da suna rubutu (writing).
Idan fayil ɗin a buɗe yake wannan
matakin ana kiransa da suna karatu (reading).
Waɗan da mukafi sani su ne:
LAMBA
|
SUNA
|
HOTO
|
|
1.
|
(HardDrive):-Wannan ma’adanin
matsakaici, wanda ya yi kama da wanda ke ƙasan shi, ana ce masa (hard drive). Wannan (hard
drive)yana zuwa ne tare da kwamfuta, sannan
kuma a kodayaushe yana cikinta.
Yanaadana dukkan
shirye-shiryen da kwamfuta zata iya buƙata don ta
yi aiki. Bugu-da-ƙari, masu amfani da kwamfuta
suna adana
bayanai a cikin shi.
|
|
|
2.
|
(FloppyDisk):-Wannan
ma’adani matsakaici, zaa iya saka
shi a cikin kwamfuta sannan a adana bayanai acikinsa, sannan a fitar da shi.Zaa
kuma iya tafiya dashi duk inda ake da buƙata.
|
|
|
3.
|
CD ko
DVD:-Irin wannan ma’adanin bayanai yana karɓar bayanai
sosai fiye da (Floppy Disk). Wannan
ma’adanin bayanai ya zo da bambancin siffa
ko siga. Wannan yana nufin muna da CDs da kuma DVDs waɗanda zaa iya
adana bayanai kawai a kansu, amma baa iya
goge bayanan da aka saka a cikinsu. Bugu-da-ƙari, akwai waɗan da ake iya adanawa sannan
kuma a goge bayanan idan an buƙaci
yin hakan.
|
|
|
4.
|
(USB
Flash Drive):Wannanshima
yana ɗaya daga cikin ma’adanin bayanai da muke da su, wanda
ya ke da matuƙar sauƙi wajen ɗauka aje duk inda ake da buƙata da shi, sannan yafi sauƙin riƙewa bisa ga (floppy disk). A yaddamuke
gani a cikin hoto yana da ƙanƙanta sosai idan mun
kwatanta shi da sauran da suka gabata.
|
|
0 comments:
Post a Comment
Thank You for Your Comment